Wanene Zai Ceci Waɗanda Suke Neman Taimako?
“Ya Allah, ka ba sarki hukuntanka, . . . gama za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka.”—ZAB. 72:1, 12.
1. A batun Dauda, menene muka koya game da jin kan Allah?
WAƊANNAN kalaman suna da ban ƙarfafa, wataƙila Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ne ya rubuta su! Shekaru da yawa kafin ya rubuta su, ya yi nadama bayan ya yi zina da Beth-sheba. A wannan lokacin, Dauda ya roƙi Allah: “Bisa ga yawan jiyejiyenƙanka ka shafe laifofina. . . . Zunubina yana gabana kullum. . . . Ga shi, cikin mugunta aka sifanta ni; cikin zunubi kuma uwata ta ɗauki cikina.” (Zab. 51:1-5) Jehobah cikin jin kai yana yin la’akari da yanayinmu na zunubi da muka gada.
2. Ta yaya Zabura ta 72 za ta taimaka mana?
2 Jehobah ya fahimci yanayinmu na baƙin ciki. Amma, yadda aka annabta, Sarkin da Allah ya naɗa “za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: Matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-rashi, za ya kuwa ceci rayukan matalauta.” (Zab. 72:12, 13) Yaya za a yi tanadin taimakon? Zabura ta 72 ta gaya mana. Da yake an rera ta ne game da sarautar ɗan Dauda Sulemanu, wannan waƙar ta nuna yadda sarautar Ɗan Allah, Yesu Kristi, za ta kawar da wahalolin ’yan Adam.
Abin da Sarautar Kristi Za Ta Yi
3. Menene Sulemanu ya roƙa, kuma menene Allah ya ba shi?
3 Bayan ya ce a naɗa Sulemanu sarki, Dauda tsoho ya ba da takamammun umurni da Sulemanu ya cika da aminci. (1 Sar. 1:32-35; 2:1-3) Daga baya Jehobah ya bayyana ga Sulemanu a cikin mafarki kuma ya ce: “Ka roƙi abin da zan ba ka.” Sulemanu ya roƙi abu guda kaɗai: “Ka ba bawanka zuciya mai-hikima da za ya shar’anta jama’arka, domin in raba tsakanin nagarta da mugunta.” Domin Sulemanu ya yi roƙo cikin tawali’u, Allah ya ba shi abin da ya roƙa da kuma ƙari.—1 Sar. 3:5, 9-13.
4. Yaya wata sarauniya na zamaninsa ta kwatanta sarautar Sulemanu?
4 Da albarkar Jehobah, sarautar Sulemanu ta kasance lokacin da aka fi samun salama da wadata a ƙarƙashin kowace gwamnati a duniya. (1 Sar. 4:25) Sarauniyar Sheba tare da rundunarta mai girma suna cikin waɗanda suka zo ganin yadda sarautar Sulemanu take. Ta gaya wa Sulemanu: “Tarihi mai-gaskiya ne na ji cikin ƙasata . . . ko rabi ba a faɗa mani ba: da hikimarka, da ni’imarka sun wuce gaban mashahurin sunan da na ji.” (1 Sar. 10:1, 6, 7) Duk da haka, Yesu ya nuna hikima mafi girma, kuma ya ce game da kansa: “Ga kuwa wanda ya fi Solomon girma a nan.”—Mat. 12:42.
Samun Taimako a Ƙarƙashin Sulemanu Mai Girma
5. Menene Zabura ta 72 ta bayyana, kuma ta nuna za a yi menene?
5 Bari yanzu mu bincika fannonin Zabura ta 72 don mu koya game da albarkar da za a samu a ƙarƙashin sarautar Yesu Kristi, Sulemanu Mai Girma. (Karanta Zabura 72:1-4.) Wannan zaburar ta bayyana yadda Jehobah yake ji game da “mulkin” Ɗansa, “Sarkin Salama,” Yesu Kristi. (Isha. 9:6, 7) Ta wurin ja-gorar Allah, Sulemanu Mai Girma zai ‘yi wa matalauta shari’a da gaskiya kuma ya ceci ’ya’yan masu-talauci.’ Sarautarsa za ta zama ta salama da adalci. Sa’ad da yake duniya, Yesu ya nuna abin da zai yi a lokacin Sarautarsa na Shekara Dubu da ke zuwa.—R. Yoh. 20:4.
6. Wace albarka da za mu samu a ƙarƙashin sarautar Mulkin Yesu ne ya ɗan nuna mana?
6 Ka yi la’akari da wasu ayyukan Yesu Kristi da suka ɗan nuna mana abin da zai yi don ’yan Adam wajen cika Zabura ta 72. Muna da dalilai na yin sha’awar juyayinsa mai girma don waɗanda suke shan wahala. (Mat. 9:35, 36; 15:29-31) Alal misali, wani kuturu ya je wajen Yesu kuma ya yi roƙo: “Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Yesu ya amsa: “Na yarda; ka tsarkaka.” Kuma mutumin ya warke! (Mar. 1:40-42) Daga baya, Yesu ya haɗu da wata gwauruwa wadda ɗanta tilo ya mutu. Da “ya yi juyayi,” Yesu ya ce, “Ka tashi,” kuma ɗanta ya yi hakan. Ya rayu!—Luk 7:11-15.
7, 8. A waɗanne misalai ne Yesu ya nuna ikonsa na warkarwa?
7 Jehobah ya ba Yesu ikon yin mu’ujizai. An kwatanta hakan a batun “mace kuma, wadda ta shekara goma sha biyu tana zubar jini.” Ko da “ta sha wahala dayawa kuwa ga hannuwan masu-magani dayawa, ta ɓatasda dukan abin da ke wurinta,” sai gaba-gaba cutar take yi. Matar ta shiga cikin jama’a kuma ta taɓa Yesu, hakan karya Doka ce ga wadda take ‘zubar jini.’ (Lev. 15:19, 25) Yesu ya ji cewa iko ya fita daga jikinsa kuma saboda haka ya nemi sanin wanda ya taɓa shi. Da yake “tana jin tsoro, tana rawan jiki,” matar “ta fāɗi a gabansa, ta faɗa masa gaskiya duka.” Da ya fahimci cewa Jehobah ne ya warkar da matar, Yesu ya bi da ita yadda ya kamata kuma ya ce: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkarda ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.”—Mar. 5:25-27, 30, 33, 34.
8 Ikon warkarwa da Allah ya ba Yesu ya warkar da masu ciwo kuma ya shafi masu kallo sosai. Alal misali, babu shakka Yesu ya ƙayatar da mutane da yawa sa’ad da suka ga cewa ya warkar da mutane kafin sanannen Huɗubarsa a kan Dutse. (Luk 6:17-19) Sa’ad da Yohanna mai Baftisma ya aika manzanni biyu su je su bincika ko Yesu ne Almasihu, sun same shi yana ‘warkarda mutane dayawa daga cututtuka iri iri alobai da miyagun ruhohi; waɗansu dayawa kuwa da su ke da makamta yana ba su ganin gari.’ Sai Yesu ya gaya wa mutanen biyu: “Ku faɗa wa Yohanna abin da kuka gani kuka ji kuma; makafi suna karɓan ganin gari, guragu suna tafiya, kutare suna tsarkaka, kurame suna ji, ana tada matattu, ana yi wa talakawa wa’azin bishara.” (Luk 7:19-22) Babu shakka, wannan saƙon ya ƙarfafa Yohanna!
9. Mu’ujizan Yesu sun nuna menene?
9 Hakika, sauƙi daga wahala da Yesu ya yi tanadinsa a lokacin da yake hidima a duniya na ɗan lokaci ne kaɗai. Waɗanda ya warkar da su ko kuma ya ta da daga matattu sun mutu daga baya. Duk da haka, mu’ujizai da Yesu ya yi sa’ad da yake duniya sun nuna sauƙi na dindindin da ’yan Adam za su more a ƙarƙashin sarautarsa na Almasihu.
Aljanna a Dukan Duniya a Nan Gaba
10, 11. (a) Har tsawon wane lokaci ne albarkar Mulki za ta kasance, kuma yaya sarautar Yesu za ta kasance? (b) Waye ne zai kasance tare da Kristi cikin Aljanna, yaya zai iya yin rayuwa har abada?
10 Ka yi ƙoƙari ka ƙaga yadda rayuwa za ta kasance a cikin Aljanna a duniya. (Karanta Zabura 72:5-9.) Masu bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya za su iya more rayuwa a cikin Aljanna muddin akwai rana da wata, hakika, har abada! Sarki Yesu Kristi zai kasance da wartsakarwa, ‘kamar ruwan sama bisa sosayayyar ciyawa da zirnaniyu masu-damsasa ƙasa.’
11 Yayin da kake hangar cikar wannan zabura, ba ka farin ciki ne da begen zama har abada cikin aljanna a duniya? Hakika mai laifi da aka tsire ya yi farin ciki sa’ad da Yesu ya gaya masa: “Kana tare da ni cikin Al’janna.” (Luk 23:43) A lokacin Sarautar Shekara Dubu na Yesu, za a ta da wannan mutumin zuwa rai. Idan ya miƙa kai ga sarautar Kristi, zai yi rayuwa a duniya har abada cikin koshin lafiya da farin ciki.
12. A lokacin Sarautar Shekara Dubu na Kristi, wane zarafi za a ba marasa adalci da aka ta da daga matattu?
12 A ƙarƙashin sarautar Sulemanu Mai Girma, Yesu Kristi, “mai-adalci za shi yalwata,” wato, ya samu ci gaba. (Zab. 72:7) Ƙaunar Kristi da kulawa za su kasance a yalwace, kamar yadda suke sa’ad da yake duniya. A sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta za a ba har da “marasa-adalci” da aka ta da daga matattu zarafin bin mizanan Jehobah kuma su rayu. (A. M. 24:15) Hakika, ba za a ƙyale waɗanda suka ƙi su aikata daidai da bukatu na Allah su ci gaba da rayuwa kuma su ɓata salama da kwanciyar hankali na sabuwar duniya ba.
13. Yaya yawan yadda sarautar Mulki zai kai, me ya sa ba za a taɓa hana salamarta ba?
13 An nuna yawan yadda sarautar Sulemanu Mai Girma za ta kai a dukan duniya da waɗannan kalaman: “Za ya yi mulki daga teku zuwa teku, daga Kogin [Yufiretis] har zuwa iyakan duniya. Mazaunan jeji za su durƙusa a gabansa; maƙiyansa za su lashe ƙura.” (Zab. 72:8, 9) Hakika, Yesu Kristi zai yi sarauta bisa dukan duniya. (Zech. 9:9, 10) Waɗanda suke godiya don sarautarsa da albarkarta za su “durƙusa” don biyayya na son rai. A wani ɓangare kuma, za a kawar da masu zunubi da suka ƙi tuba, a alamance, ko idan suna ’yan “shekara ɗari.” (Isha. 65:20) “Za su lashe ƙura.”
Juyayi da Ƙauna a Gare Mu
14, 15. Yaya muka sani cewa Yesu ya fahimci yadda ’yan Adam suke ji kuma “za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka”?
14 ’Yan Adam masu zunubi suna cikin yanayi mai ban tausayi kuma suna bukatan taimako sosai. Amma muna da bege. (Karanta Zabura 72:12-14.) Yesu, Sulemanu Mai Girma yana jin tausayinmu domin ya fahimci yanayinmu na ajizanci. Bugu da ƙari, Yesu ya sha wahala don adalci, kuma Allah ya ƙyale shi ya fuskanci gwaji da kansa. Hakika, Yesu ya sha wahalar baƙin ciki har da “zufarsa kuma ta zama kamar manyan ɗiɗɗigar jini, suna fāɗuwa a ƙasa.” (Luk 22:44) Daga baya a kan gungumen azaba, ya yi kuka: “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” (Mat. 27:45, 46) Duk da wahalolin da ya sha, da ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi ya juya shi daga bauta wa Jehobah, Yesu ya kasance da aminci ga Jehobah Allah.
15 Muna da tabbaci cewa Yesu yana ganin azabarmu kuma “za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: Matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako.” Da ƙauna kamar Ubansa, Yesu zai ‘ji kukar masu-wahala,’ kuma zai “warkar da masu-karyayyar zuciya, yana ɗaure raunukan su.” (Zab. 69:33; 147:3) Yesu zai yi juyayin “kumamancinmu,” domin “an jarabce shi a kowace fuska kamarmu.” (Ibran. 4:15) Yana da kyau a san cewa Sarki Yesu Kristi yana sarauta yanzu a sama kuma yana ɗokin ya kawo sauƙi ga ’yan Adam da suke wahala!
16. Me ya sa Sulemanu ya ji tausayin talakawansa?
16 Domin yana da hikima da basira, Sulemanu babu shakka “ya nuna tausayi ga matalauci.” Ban da haka ma, rayuwarsa tana cike da aukuwa na baƙin ciki da na azaba. Wansa Amnon ya yi wa ƙanwarsa Tamar fyaɗe, kuma ƙanin Sulemanu Absalom ya kashe Amnon don wannan laifin. (2 Sam. 13:1, 14, 28, 29) Absalom ya ƙwace karagar Dauda, amma bai yi nasara ba, kuma Joab ya kashe shi. (2 Sam. 15:10, 14; 18:9, 14) Daga baya, ɗan’uwan Sulemanu, Adonijah ya yi ƙoƙarin ya ƙwace mulkin. Da a ce ya yi nasara, hakan babu shakka zai kai ga mutuwar Sulemanu. (1 Sar. 1:5) Abin da Sulemanu ya faɗa a addu’arsa sa’ad da ake keɓe haikalin Jehobah ya nuna cewa ya fahimci wahalar ’yan Adam. Sarkin ya yi addu’a game da talakawansa: “Kowa yana sane da nasa aloba da nasa baƙinciki, . . . [Jehobah] ka gafarta, ka sāka wa kowane mutum bisa ga dukan aikinsa.”—2 Laba. 6:29, 30.
17, 18. Wane baƙin ciki ne wasu cikin bayin Allah suke jimrewa da shi, kuma menene ya taimaka musu su yi hakan?
17 ‘Namu baƙin ciki’ yana iya zama don sakamakon wasu abubuwan da muka fuskanta a rayuwa. Mary,a wata mata Mashaidiyar Jehobah ta rubuta: “Ina da kowane dalilin yin farin ciki, amma sau da yawa rayuwata ta dā tana sa ni kunya da ƙyama. Hakan na sa ni baƙin ciki sosai, kuma na kan yi kuka, kamar dai kome ya faru jiya. Har ila abubuwa da suka faru na sa na kasance da ra’ayin rashin cancanta da jin laifi.”
18 Bayin Allah masu yawa suna jin hakan, amma menene zai taimaka musu su samu ƙarfin da suke bukata domin su jimre? “Abokai na ƙwarai da ’yan’uwa a cikin ikilisiya yanzu suna sa ni farin ciki,” in ji Mary. “Ina kuma yin ƙoƙari na mai da hankali ga alkawarin da Jehobah ya yi don nan gaba, kuma ina da tabbaci cewa kukata don taimako zai koma kukan farin ciki.” (Zab. 126:5) Muna bukatan mu sa begenmu ga tanadin Ɗansa da Allah ya yi, wato, Sarkin da ya naɗa. An annabta game da shi: “Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-rashi, za ya kuwa ceci rayukan matalauta. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.” (Zab. 72:13, 14) Hakan na da ban ƙarfafa!
Sabuwar Duniya Cike da Abubuwa Masu Yawa Tana Jiranmu
19, 20. (a) Kamar yadda aka nuna a Zabura ta 72, wace matsala ce sarautar Mulki za ta magance? (b) Wanene ainihi ya kamata a yaba wa don sarautar Kristi, kuma yaya kake ji game da abin da za ta cim ma?
19 Ka sake ƙoƙarin zana hoton nan gaba na ’yan Adam masu adalci a sabuwar duniya ta Allah a ƙarƙashin sarautar Sulemanu Mai Girma. An yi mana alkawari: “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.” (Zab. 72:16) Tun da yake ba a shuka hatsi a kan duwatsu, waɗannan kalaman sun nanata yadda duniya za ta ba da amfanin gona. Hatsinta zai zama ‘kamar na Lebanon,’ wurin mai ni’ima ne sosai a lokacin sarautar Sulemanu. Ka yi tunani! Ba za a ƙara yin ƙarancin abinci ba, ba mai rashin abinci, ba mai jin yunwa! Kowa zai more “biki na abinci mai-mai.”—Isha. 25:6-8; 35:1, 2.
20 Wanene za a yaba wa don dukan waɗannan albarka? Sarki Madawwami ne da Masaraucin dukan Sararin Samaniya, Jehobah Allah. Watau, dukanmu da farin ciki za mu haɗa muryoyinmu ga sashen kammalawa na wannan waƙa mai daɗi mai daɗaɗa rai: “Sunansa [na Sarki Yesu Kristi] za ya tabbata har abada; Sunansa za ya yaɗu muddar akwai rana: Za a albarkaci mutane a cikinsa; dukan al’ummai za su ce da shi mai-albarka. Albarka ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda yana aika al’ajibai shi kaɗai: Kuma albarka ga sunansa mai-daraja har abada; bari dukan duniya ta cika da darajarsa. Amin, Amin kuma.”—Zab. 72:17-19.
[Hasiya]
a An canja suna.
Yaya Za Ka Amsa?
• Zabura ta 72 ta wurin annabci ta nuna menene?
• Wanene Sulemanu Mai Girma, kuma yaya yawan yadda sarautarsa za ta kasance?
• Menene ke ba ka sha’awa game da albarkar da aka annabta a Zabura ta 72?
[Hoton da ke shafi na 29]
Mecece wadatar da aka more a lokacin sarautar Sulemanu take alamta?
[Hoton da ke shafi na 32]
Kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu mu yi dukan iya ƙoƙarinmu mu samu rai a cikin Aljanna a ƙarƙashin sarautar Sulemanu Mai Girma