Ka Biɗi Albarkar Jehobah Sosai
“[Allah] mai sakawa ne ga dukan waɗanda suke biɗarsa sosai.”—IBRAN. 11:6, NW.
1, 2. (a) Ta yaya mutane da yawa suke biɗar albarkar Allah? (b) Me ya sa ya kamata mu mai da hankali sosai ga samun albarkar Jehobah?
IDAN mutum zai yi tafiya daga wani wuri zuwa wani wuri, mutane za su ce masa: “Allah ya kiyaye hanya!” Limaman addinai dabam-dabam suna yi wa mutane, dabbobi, da abubuwa masu rai albarka. Mutane suna iya tafiya zuwa wasu wurare na addini domin an gaya musu cewa za su sami albarka a wurin. ’Yan siyasa suna roƙon Allah a kai a kai ya albarkaci ƙasarsu. Kana ganin ya dace a yi irin waɗannan roƙon don samun albarka? Suna da amfani kuwa? Su wanene suke samun albarkar Allah, kuma me ya sa?
2 Jehobah ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, zai samu mutane masu tsabta da salama daga dukan al’ummai, waɗanda za su yi wa’azin bishara na Mulki zuwa iyakar duniya duk da ƙiyayya da hamayya. (Isha. 2:2-4; Mat. 24:14; R. Yoh. 7:9, 14) Mu da muka amince da hakkin kasancewa cikin waɗannan mutanen da aka annabta, muna so kuma muna bukatan albarkar Allah, domin idan babu ita ba za mu yi nasara ba. (Zab. 127:1) Amma yaya za mu sami albarkar Allah?
Albarka Za Ta Tarar da Masu Yin Biyayya
3. Da a ce Isra’ilawa sun yi biyayya, menene zai zama sakamakon?
3 Karanta Misalai 10:6, 7. Kafin al’ummar Isra’ila ta shiga Ƙasar Alkawari, Jehobah ya nuna cewa za su samu ni’ima da kāriya idan suka saurari muryarsa. (K. Sha 28:1, 2) Mutanen Allah ba wai kawai za su samu albarkar Jehobah ba ne amma za ta ‘tarar da’ su. Babu shakka, waɗannan masu biyayya za su samu albarka.
4. Menene yin biyayya ta gaske ya ƙunsa?
4 Da wane irin hali ne Isra’ilawa za su yi biyayya? Dokar Allah ta ce zai yi fushi idan mutanensa ba su bauta masa “da farinciki, da daɗin zuciya” ba. (Karanta Kubawar Shari’a 28:45-47.) Jehobah ya cancanci mu bi dukan umurninsa domin muna ƙaunarsa, ba kamar yadda dabbobi ko aljanu suke yi ba don ya zama dole. (Mar. 1:27; Yaƙ. 3:3) Yin biyayya ta gaske ga Allah tana nuna ƙauna. Tana bayyana ne daga farin cikin da ke fitowa daga kasancewa da bangaskiya cewa dokokin Jehobah ba su da nauyi da kuma “shi mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.”—Ibran. 11:6; 1 Yoh. 5:3.
5. Yaya dogara ga alkawarin Jehobah zai taimaka wa mutum ya yi biyayya ga dokar da ke Kubawar Shari’a 15:7, 8?
5 Ka yi la’akari da yadda aka nuna irin wannan biyayyar ta wajen bin dokar da ke Kubawar Shari’a 15:7, 8 (Karanta.) Yin biyayya ga wannan dokar ba da son rai ba ya ɗan kawo sauƙi ga matalauta, amma hakan zai kawo dangantaka mai kyau ne tsakanin mutanen Allah? Mafi muhimmanci, hakan zai nuna bangaskiya ne ga iyawar Jehobah na yi wa bayinsa tanadin da nuna godiya ga zarafin yin koyi da karimcinsa? Da kyar! Allah yana lura da yanayin zuciyar mutum mai karimci da gaske kuma ya yi alkawarin yi masa albarka a dukan aikinsa da dukan abin da yake da niyyar yi. (K. Sha 15:10) Ba da gaskiya ga wannan alkawarin zai iya motsa mutum ya aikata kuma zai kawo albarka masu yawa.—Mis. 28:20.
6. Menene Ibraniyawa 11:6 ta tabbatar mana?
6 Ƙari ga kasancewa da bangaskiya ga Jehobah a matsayin Mai sakawa, Ibraniyawa 11:6 ta nanata wani hali da ake bukata domin a sami albarkar Allah. Ka lura cewa Jehobah yana saka wa waɗanda suke ‘biɗarsa sosai.’ Kalmar yare na ainihi da aka yi amfani da ita a nan tana nufin ƙoƙartawa sosai. Ya kamata hakan ya tabbatar mana da sakamakon albarkar! Allah na gaskiya wanda, “ba ya iya yin ƙarya” ne tushenta. (Tit. 1:2) Ya nuna cikin shekaru da yawa cewa alkawuransa tabbatattu ne sarai. Kalamansa ba sa zama banza; amma suna cikawa a koyaushe. (Isha. 55:11) Saboda haka, muna da tabbaci cewa idan muka nuna bangaskiya ta gaske, zai zama Mai Sakawa a gare mu.
7. Ta yaya za mu iya samun albarka ta hanyar “zuriyar” Ibrahim?
7 Yesu Kristi ya zama sashe na farko na “zuriyar” Ibrahim. Shafaffu Kiristoci ne suka zama sashe na biyu na “zuriya” da aka annabta. An umurce su su “sanar da mafifitan al’amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.” (Gal. 3:7-9, 14, 16, 26-29; 1 Bit. 2:9, Littafi Mai Tsarki) Ba za mu kafa dangantaka mai kyau da Jehobah ba idan muka yi banza da waɗanda Yesu ya naɗa su kula da mallakarsa ba. Idan ba tare da taimakon “bawan nan mai-aminci, mai hikima” ba, ba za mu fahimci cikakkiyar ma’anar abin da muka karanta a cikin Kalmar Allah ba balle mu san yadda za mu yi amfani da ita. (Mat. 24:45-47) Ta wajen yin abubuwan da muke koya daga cikin Nassosi, za mu iya samun albarkar Allah.
Saka Nufin Allah Farko
8, 9. Ta yaya uban iyali Yakubu ya ƙoƙarta don ya aikata daidai da roƙonsa?
8 Batun ƙoƙartawa sosai don samun albarkar Allah zai tuna mana uban iyali Yakubu. Bai san yadda Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim ba, amma ya gaskata cewa Jehobah zai ninka zuriyar kakansa, wanda ’ya’yansa za su zama al’umma mai girma. Saboda haka, a shekara ta 1781 K.Z., Yakubu ya yi tafiya zuwa Haran don ya nemi mata. Ba abokiyar zama mai kyau kawai ya je nema ba; maimakon haka, ya nemi mace mai ruhaniya da take bauta wa Jehobah da kuma wadda za ta zama uwar kirki ga yaransa.
9 Mun san cewa Yakubu ya haɗu da ’yar’uwarsa Rahila. Yana ƙaunar Rahila kuma ya yarda ya yi wa babanta, Laban, aiki na shekaru bakwai domin ya aure ta. Wannan ba labarin soyayya kawai ba ne. Yakubu ya san alkawarin da Allah Maɗaukaki ya yi wa kakansa Ibrahim kuma ya sake ambata shi ga babansa, Ishaku. (Far. 18:18; 22:17, 18; 26:3-5, 24, 25) Shi kuma Ishaku ya gaya wa ɗansa Yakubu: “Allah Mai-iko duka ya albarkace ka, ya yalwata ’ya’ya gare ka, ya riɓanɓanya ka, domin ka zama taron al’ummai; ya ba ka albarkar Ibrahim kuma, a gare ka, da zuriyanka tare da kai; domin ka gāji ƙasar baƙuncinka, wadda Allah ya bayar ga Ibrahim.” (Far. 28:3, 4) Saboda haka, ƙoƙarin da Yakubu ya yi don ya samu matar da ta dace kuma ya samu iyali ya nuna tabbacinsa ga abin da Jehobah ya faɗa.
10. Me ya sa Jehobah ya yi farin cikin yi wa Yakubu albarka?
10 Yakubu ba ya neman arziki don ya kula da iyalinsa. Ya mai da hankalinsa ne a kan alkawarin da Jehobah ya yi game da zuriyarsa. Ya mai da hankali ga cika nufin Jehobah. Yakubu ya ƙudurta yin iya ƙoƙarinsa don ya samu albarkar Allah duk da tangarɗa. Ya ci gaba da nuna wannan halin har ya tsufa, kuma Jehobah ya albarkace shi don hakan.—Karanta Farawa 32:24-29.
11. Wane ƙoƙari ne ya kamata mu yi daidai da nufin Allah da aka bayyana?
11 Kamar Yakubu, ba mu da cikakken bayani game da cika nufin Jehobah ba. Duk da haka, ta wajen yin nazarin Kalmar Allah, mun ɗan fahimci abubuwan da za su faru a “ranar Ubangiji.” (2 Bit. 3:10, 17) Alal misali, ba mu san ainihin lokacin da ranar za ta zo ba, amma mun san cewa ta kusa. Mun yarda da Kalmar Allah sa’ad da ta ce idan muka ba da shaida sosai a ɗan lokacin da ya rage, za mu ceci kanmu da waɗanda suka saurare mu.—1 Tim. 4:16.
12. Wane tabbaci muke da shi?
12 Mun fahimci cewa ƙarshen zai iya zuwa a kowane lokaci; Jehobah ba zai jira har sai an yi wa kowane mutum a duniya wa’azi ba. (Mat. 10:23) Amma, mun sami ja-gora mai kyau a yadda za mu yi aikinmu na wa’azi da kyau. Cikin bangaskiya, muna yin wannan aikin iyakar yadda za mu iya, ta wajen yin amfani da kowace dukiya da muke da ita. Za mu yi wa’azi ne koyaushe a yankin da zai fi ba da amfani? Yaya za mu sani tun da wuri? (Karanta Mai-Wa’azi 11:5, 6.) Aikinmu shi ne yin wa’azi, muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu. (1 Kor. 3:6, 7) Muna da tabbaci cewa yana ganin ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu, kuma ta wurin ruhunsa mai tsarki, zai yi tanadin kowane ja-gora da muke bukata.—Zab. 32:8.
Biɗar Ruhu Mai Tsarki
13, 14. Yaya aka nuna cewa ruhu mai tsarki na Allah yana iya sa bayinsa su cim ma wani abu?
13 Idan muna jin cewa ba mu cancanci yin wani aiki ko kuma yin wa’azi ba fa? Ya kamata mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki don ya kyautata duk wata iyawar da muke da ita a hidimarsa. (Karanta Luka 11:13.) Ruhun Allah zai iya sa mutane su cancanci yin aiki ko hidima duk da yanayinsu na dā ko kuma abin da suke fuskanta. Alal misali, nan da nan bayan Fitowarsu daga ƙasar Masar, ruhun Allah ya taimaki makiyaya da bayi su ci magabtansu a yaƙi ko da yake ba su da ilimin yaƙi. (Fit. 17:8-13) Ba da daɗewa ba bayan hakan, wannan ruhun ya mai da Bezalel da Oholiab su zama gwanaye don su shirya hurarren zanen gini mai kyau na mazauni.—Ex. 31:2-6; 35:30-35.
14 Wannan ruhu mai iko ya taimaki bayin Allah na zamani su kula da bukatun ƙungiyar sa’ad da bukata ta taso na soma buga littattafai. A cikin wasiƙa, Ɗan’uwa R. J. Martin, mai kula da wajen buga littattafai a lokacin, ya bayyana abin da aka cim ma a shekara ta 1927. “A lokacin da ya dace, Ubangiji ya buɗe hanyar, kuma muka sayi babban na’urar buga littattafai duk da cewa ba mu san kome ba game da yadda aka ƙera ta da kuma yadda ake amfani da ita. Amma Ubangiji ya san yadda yake taimakon waɗanda suka miƙa masa kansu. . . . A cikin ’yan makonni, mun sa wannan na’aurar buga littattafai ta yi aiki yadda ya kamata, kuma har yanzu tana yin aikin da waɗanda suka ƙera ta ba su san za ta iya yi ba.” Jehobah yana ci gaba da yi wa irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce albarka har zuwa yau.
15. Ta yaya Romawa 8:11 za ta iya ƙarfafa waɗanda suke fuskantar gwaji?
15 Ruhun Jehobah yana aiki a hanyoyi dabam-dabam. Dukan bayin Allah suna iya samun wannan ruhun, kuma yana taimaka musu su sha kan tangarɗa masu wuya. Idan muka ji cewa jarraba ta sha kanmu fa? Muna iya samun ƙarfafa daga kalaman Bulus da ke Romawa 7:21, 25 da 8:11. Hakika, “ruhun wannan da ya tada Yesu daga matattu” zai iya aikatawa a madadinmu, ya ba mu ƙarfin yaƙar sha’awoyi na jiki. An rubuta wannan ayar ga shafaffu Kiristoci, duk da haka, mizanin ya shafi dukan bayin Allah. Dukanmu za mu samu rai ta wajen ba da gaskiya ga Kristi, ta wajen ƙoƙartawa sosai don mu kawar da sha’awoyi da ba su dace ba, da kuma yin rayuwar da ta jitu da ja-gorar ruhu.
16. Dole ne mu yi menene don mu samu ruhu mai tsarki na Allah?
16 Allah zai ba mu ruhunsa mai tsarki ne idan ba mu ƙoƙarta ba? A’a. Bayan mun yi addu’ar samun sa, dole ne mu riƙa karanta hurarriyar Kalmar Allah sosai. (Mis. 2:1-6) Ƙari ga haka, ruhun Allah yana bisa ikilisiyar Kirista. Halartan taro a kai a kai yana nuna cewa muna son mu “ji abin da ruhu ke faɗa wa ikilisiyai.” (R. Yoh. 3:6) Bugu da ƙari, dole ne mu yi abin da muka koya cikin tawali’u. Misalai 1:23 ta shawarce mu: “Ku juyo bisa ga tsautawata: ga shi, zan zuba maku ruhuna.” Hakika, Allah yana ba da ruhunsa mai tsarki “ga waɗanda su ke biyayya gare shi.”—A. M. 5:32.
17. Da menene za mu iya kwatanta albarkar Allah a kan ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu?
17 Ko da yake ana bukatan a ƙoƙarta sosai don a samu albarkar Allah, ka tuna cewa aiki tuƙuru kaɗai ba zai iya kawo abubuwa masu kyau da Jehobah ya ba mutanensa a yalwace ba. Ana iya kwatanta albarkarsa a kan ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu da yadda jikinmu yake amfana daga abinci mai kyau. Allah ya yi jikinmu yadda za mu ji daɗin abinci kuma mu samu abubuwa masu muhimmanci na gina jiki daga abincin. Shi ne kuma yake tanadin abincin. Ba mu da cikakken sani na yadda abincinmu yake samu abubuwa na gina jiki, kuma yawancinmu ba za mu iya bayyana yadda jikinmu yake samun kuzari daga abincin da muke ci ba. Mun san cewa tsarin yana aiki kuma muna ba da haɗin kai ta wajen cin abinci. Idan muka zaɓi mu ci abinci mai gina jiki, sakamakon zai fi kyau. Hakazalika, Jehobah ya kafa bukatun samun rai madawwami, kuma yana ba mu taimakon da muke bukata don mu cika waɗannan bukatun. A bayane yake cewa yana taimaka mana sosai kuma ya cancanci mu yaba masa. Duk da haka, dole ne mu ba shi haɗin kai, mu aikata daidai da nufin Allah, don mu sami albarkar.—Hag. 2:18, 19.
18. Menene ƙudurinka, kuma me ya sa?
18 Saboda haka, ka yi kowane aiki da aka ba ka da zuciya ɗaya. A koyaushe ka nemi taimakon Jehobah don ka yi nasara. (Mar. 11:23, 24) Yayin da kake yin hakan, ka kasance da tabbaci cewa “wanda ya ke nema kuma yana samu.” (Mat. 7:8) Za a albarkaci waɗanda aka shafa da ruhu da “rawanin rai” a samaniya. (Yaƙ. 1:12) “Waɗansu tumaki” na Kristi, waɗanda suke ƙoƙarin samun albarka ta hanyar zuriyar Ibrahim, za su yi farin cikin jin Ya ce: “Ku zo, ku masu-albarka na Ubana, ku gaji mulkin da aka shirya dominku tun kafawar duniya.” (Yoh. 10:16; Mat. 25:34) Hakika, “waɗanda sun sami albarka gareshi [Allah] za su gāji ƙasan, . . . su zauna a cikinta har abada.”—Zab. 37:22, 29.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene yin biyayya ta gaske ya ƙunsa?
• Menene ake bukata don a samu albarkar Allah?
• Ta yaya za mu samu ruhu mai tsarki na Allah, kuma ta yaya zai aikata a madadinmu?
[Hotuna da ke shafi na 9]
Yakubu ya yi kokawa da mala’ika don ya samu albarkar Jehobah.
Kana ƙoƙarta kamar hakan kuwa?
[Hoton da ke shafi na 10]
Ruhu mai tsarki na Allah ya taimaki Bezalel da Oholiab su ƙware sosai