Ku Taimaki Matasa Su Saba da Ƙungiyar Jehobah
YARA suna son su koya abubuwa. Ku yi tunanin irin tambayoyin da yara Isra’ilawa a ƙasar Masar suka yi da daddaren Idin Ƙetarewa na farko: ‘Me ya sa za a kashe ’yar tunkiyar?’ ‘Me ya sa Baba yake yayyafa jini a baƙin kofa?’ ‘Ina ne za mu je?’ An ga cewa Jehobah ya amince da irin waɗannan tambayoyin daga umurnin da ya ba wa ubannin Isra’ilawa. Jehobah ya gaya masu game da Idin Ƙeterewa da za a yi a gaba: “Sa’anda ’ya’yanku za su ce maku, Minene dalilinku da wannan ibada? Za ku ce, Hadaya ce ta paskar Ubangiji, da ya ƙetare gidajen ’ya’yan Isra’ila cikin Masar, sa’anda ya bugi Masarawa, ya ceci gidajenmu kuma.” (Fit. 12:24-27) Daga baya, Jehobah ya tunasar da iyayen ’yan Isra’ila game da muhimmancin ba da amsa ga tambayoyin ’ya’yansu game da “farillan nan, da shari’un nan” da Jehobah ya umurta.—K. Sha 6:20-25.
A bayane yake cewa, Jehobah yana son yara su iya samun amsoshi masu gamsarwa ga tambayoyinsu game da bauta ta gaskiya, wato, amsoshin da za su motsa su su ƙaunaci Jehobah a matsayin Allahnsu da kuma Mai Cetonsu. Jehobah yana son hakan ga matasanmu a yau. Hanya ɗaya da iyaye za su iya koya wa yaransu su yi ƙaunar Allah da kuma mutanensa da dukan zuciyarsu ita ce ta taimaka musu su saba da ƙungiyar Jehobah kuma su fahimci yadda suke amfana daga tsarinta. Yanzu bari mu yi la’akari da wasu hanyoyi da za a iya taimaka wa matasa su daɗa saninsu na ƙungiyar Allah.
Ikilisiya
Matasa suna bukatar sanin ikilisiyar da iyalinsu suke tarayya. Domin ku cim ma hakan, ku iyaye kuna bukatar ku halarci dukan tarurruka na Kirista tare da yaranku. Da hakan, za ku bi misalin da Jehobah ya kafa wa Isra’ilawa, waɗanda aka umurce su: ‘Ka tattara jama’a, maza da mata da ƙanana . . . , domin su ji, su koya, su ji tsoron Ubangiji Allahnka, su kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a domin su aikata; ’ya’yansu kuma, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koya tsoron Ubangiji Allahnku.’—K. Sha 31:12, 13.
Yara za su iya soma koyo game da Kalmar Jehobah tun suna jarirai. Manzo Bulus ya ce game da Timotawus: “Tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki.” (2 Tim. 3:15) Ƙananan yara za su iya fahimci abin da ake yi a tarurruka na Majami’ar Mulki, kuma su saba da waƙoƙin Mulki. Suna koya yadda ake daraja da kuma yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da suke bayyana shi. Bugu da ƙari, za su ga halayen da suke nuna mabiyin Kristi na gaske, wato, ƙauna ta gaske. Yesu ya ce: “Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:34, 35) Yara za su so ƙauna da kāriya ta gaske da ke wanzuwa a Majami’ar Mulki kuma za ta taimake su su ɗauki halartar tarurrukan Kirista a matsayin abu mai muhimmanci a rayuwarsu.
Idan kun sa ya zama halinku ku riƙa halartar taro a Majami’ar Mulki a kan lokaci kuma ku tsaya kaɗan bayan an kammala taron, yaranku za su samu zarafin yin abokai. Maimakon ku ƙyale su su riƙa abokantaka da tsaransu kaɗai, zai dace ku sa su riƙa gaisawa da manya ma. Idan kun sa yaranku su saba da manya ma, za su koya cewa manya suna da hikima sosai. Kamar yadda Zakariya na dā wanda ‘mai koyar da tsoron Allah’ ne ya zama misali mai kyau ga matashi Uzziah, sarkin Yahuda, haka ma waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah suke kafa wa matasa misali mai kyau. (2 Laba. 26:1, 4, 5) Sa’ad da kuke cikin Majami’ar Mulki, za ku iya bayyana wa yaranku yadda ake amfani da ma’adanar littattafai, allon sanarwa, da wasu abubuwan da ke majami’ar.
Ƙungiya ta Dukan Duniya
Yara suna bukatar su san cewa ikilisiyar da suke halarta tana ɗaya daga cikin ikilisiyoyi fiye da dubu ɗari da ke dukan duniya. Ku bayyana fannonin wannan ƙungiyar, yadda ake tafiyar da ita, da kuma hakkin da yara suke da shi na tallafa mata. Ku nuna musu dalilin da ya sa kuke ɗokin halartar tarurruka na da’ira, na gunduma, da kuma ziyarar mai kula da da’ira.—Ka duba akwatin nan “Abubuwan da Za Ku Tattauna Sa’ad da Kuke Bauta ta Iyali,” a shafi na 28.
Idan kuna da zarafi, ku gayyaci masu kula da da’ira, masu wa’azi a ƙasashen waje, masu hidima a Bethel, da wasu da suke hidima ta cikakken lokaci zuwa gidanku don su ci abinci. Kada ku yi tunanin cewa ba su da lokacin zama tare da yara. Waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci suna yin koyi da Yesu, wanda yake marabta da kuma tattauna da yara. (Mar. 10:13-16) Yaranku za su iya kafa wa kansu makasudin biɗin hidima ta cikakken lokaci don sauraron labaran waɗannan bayin Jehobah da kuma ganin farin cikin da suke samu a tsarkakkar hidima.
Wane ƙarin abu ne za ku iya yi a matsayin iyali don ku taimaki yaranku su saba da ƙungiyar Jehobah? Ga wasu shawarwari: Ku yi shirin tattauna littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom a matsayin iyali. Ku nanata ba da kai, tawali’u, da amincin da bayin Jehobah suka nuna. Ku nuna yadda Jehobah ya yi amfani da su wajen yaɗa bishara a dukan duniya. Ku yi amfani da bidiyoyin da ƙungiyar Jehobah ta buga don koyar da darussa masu muhimminci na zamanin dā da na yanzu. Idan kuna da zarafi, ku ziyarci ofishin reshe da gidan Bethel da ke ƙasarku ko kuma wata ƙasa. Irin wannan ziyarar za ta sa yaranku su ga yadda ƙungiyar Jehobah a ƙarƙashin ja-gorancin rukunin bawa mai aminci suke ba da abinci na ruhaniya kuma suke ja-goranci ’yan’uwa a dukan duniya, kamar yadda aka yi a ƙarni na farko A.Z.—Mat. 24:45-47; A. M. 15:22-31.
Daidaita Koyarwar ga Kowane Yaro
Ku yi koyi da yadda Yesu ya koyar da almajiransa, sa’ad da kuke koyar da yaranku. Ya taɓa gaya musu: “Ina da sauran abubuwan da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.” (Yoh. 16:12) Yesu bai cika almajiransa da yawan bayyanai ba. Maimakon hakan, ya koya musu muhimmiyar gaskiya da sannu sannu domin su samu fahimta sosai. Hakazalika, kada ku cika yaranku da yawan bayyanai. Ta wajen koya musu abubuwa kaɗan-kaɗan game da ƙungiyar nan amma a kai a kai, za ku ci gaba da motsa su, kuma za ku sa koyo game da ikilisiyar Kirista ta kasance abin farin ciki. Yayin da bukatun yaranku suke canjawa, za ku iya sake maimaita da kuma yin ƙari a kan abubuwan da sun riga sun koya.
Ikilisiyar Kirista tana taimaka mana sosai mu kasance da ƙarfi a ruhaniya, kuma matasa da suke sa hannu da ƙwazo a ayyukanta suna samun ƙarfin yin tsayayya da rinjayar duniyar Shaiɗan. (Rom. 12:2) Muna da gaba gaɗi cewa za ku samu farin cikin taimaka wa yaranku su saba da ƙungiyar Jehobah. Da albarkarsa, bari su kasance da aminci ga ƙungiyar da kuma Allah mai ƙauna wanda muke bauta wa.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 28]
Abubuwan da Za Ku Tattauna Sa’ad da Kuke Bauta ta Iyali
Ga wasu darussa da suka shafi al’amuran ƙungiyar da za ku yi la’akari da su a lokacin Bautarku ta Iyali da yamma.
▪ Ku yi bitar tarihin ikilisiyarku. A wane lokaci ne aka kafa ta kuma ta yaya aka yi hakan? Waɗanne Majami’un Mulki ne ikilisiyar ta yi amfani da su a dā? Don irin wannan tattaunawar, zai yi kyau ku gayyaci wanda ya daɗe a ikilisiyar zuwa gidanku don ya amsa tambayoyin yaranku.
▪ Ku bayyana manufar tarurrukan ikilisiya dabam dabam da manyan taro da kuma yadda yaran za su iya amfana da su.
▪ Ku yi la’akari da makarantu dabam dabam da ƙungiyar Jehobah ta kafa. Ku ba da labarai da suka nuna sakamako masu kyau da waɗanda suka sauƙe karatu daga waɗannan makarantu suka samu.
▪ Ku taimaka wa matasa su ga muhimmancin zaman masu yin shelar bishara na kullum. Ku nuna masu yadda za su saka hannu a rahoto na dukan duniya da ake wallafawa a cikin Yearbook of Jehovah’s Witnesses.
▪ Ku yi la’akari da hidimomi ta cikakken lokaci dabam dabam da matasa za su iya yi a ƙungiyar Jehobah. Babi na 10 na littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will tushe ne mai kyau na samun bayani.
▪ Ku taimaki matasa su fahimci dalilin da ya sa ake bin wasu ƙa’idodi a cikin ikilisiya. Ku bayyana musu dalilin da ya sa za su dogara ga ƙungiyar Jehobah, har ma a abubuwan da ake ganin cewa ba su da muhimmanci. Ku nuna musu yadda za su iya sa ikilisiyar ta kasance da tsari mai kyau ta wajen bin ja-gorancin dattawa.
[Hoton]
Yaranku za su amfana idan sun yi abuta da waɗanda suke bauta wa Jehobah da daɗewa
[Hotuna da ke shafi na 26]
Kamar yadda yake a Isra’ila ta dā, iyaye a yau suna ƙoƙari su ba da amsoshi masu gamsarwa idan aka yi musu tambayoyi game da ƙungiyar Jehobah