Kana da Dalilin Yin Farin Ciki
YADDA aka tsara mitsitsin ƙwayoyin halitta zuwa damin taurari masu girman gaske ya nuna cewa akwai tsari a cikin halittun Jehobah. Wannan ba abin mamaki ba ne, don Mahaliccin “ba Allah na yamutsai ba ne.” (1 Kor. 14:33) Tsarin Allah don bauta na burgewa. Ka yi la’akari da abin da ya yi. Ya ƙafa ƙungiya ɗaya na miliyoyin halittu masu basira, wato, mutane a duniya da kuma mala’iku, dukansu suna da ’yancin zaɓe da kuma haɗin kai a bauta ta gaskiya. Wannan yana da ban al’ajabi!
A Isra’ila ta dā, sashen ƙungiyar Allah na duniya yana Urushalima, inda haikalin Jehobah da sarkin da ya naɗa suke. Wani Ba’isra’ile da ke zaman bauta a Babila ya furta yadda yake ji game da wannan birni mai tsarki haka: “Bari harshena shi liƙe wa bakina, idan ban tuna da ke ba; idan ban fi son Urushalima gaba da mafificin abin farin zuciyata ba.”—Zab. 137:6.
Haka ne kake ji game da ƙungiyar Allah a yau? Yana sa ka farin ciki fiye da kome? Yaranka sun fahimci tarihi da ayyukan sashen ƙungiyar Allah na duniya? Suna godiya cewa suna cikin sashen ’yan’uwanci na Shaidun Jehobah a dukan duniya? (1 Bit. 2:17) Ka bi shawarwari na gaba a Bautarka ta Iyali da yamma domin ka sa iyalinka su kyautata fahimi da godiyarsu ga ƙungiyar Jehobah.
Ka Faɗi Abubuwan da Suka Faru “a Zamanin Dā”
A kowace shekara, iyalai Ba’isra’ila suna yin taro don su yi Idin Ƙetarewa. Sa’ad da aka kafa idin, Musa ya umurci mutanen: “Sa’anda ɗanka zai tambaye ka wata rana, yana cewa, Menene wannan? Za ka ce masa, da ƙarfin hannu Ubangiji ya fishe mu daga Masar, daga gidan bauta.” (Fit. 13:14) Ba za a mance da tarihin yadda Jehobah ya yi sha’ani da Isra’ilawa ba. Hakika, ubanni da yawa Ba’isra’ila sun bi umurnin Musa. Shekaru da yawa, wani Ba’isra’ila ya yi addu’a: “Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah, ubanninmu suka faɗa mana, Aikin da ka yi a zamaninsu, a zamanin dā.”—Zab. 44:1.
Ga wani matashi a yau, tarihin Shaidun Jehobah fiye da shekaru 100 ko kusan hakan da suka shige yana iya zama kamar tarihi na “zamanin dā.” Yaya za ka sa waɗannan aukuwa su kasance da gaske ga yaranka? Don su yi hakan, wasu iyaye sun yi amfani da littattafan nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom da Yearbook da kuma labaran rayuwa da aka wallafa cikin mujallunmu da wasu rahotanni na tarihin tsarin Allah, har da sabon faifan DVD game da mutanen Allah na zamani. Bidiyo game da yadda aka tsananta wa ’yan’uwanmu a ƙasar Rasha ta dā da Nazi da ke ƙasar Jamus suna koya wa iyalai su dogara ga Jehobah a lokacin gwaji. Ka haɗa irin waɗannan abubuwa a Bautarku ta Iyali da yamma. Hakan zai ƙarfafa bangaskiyar yaranka sa’ad da suke fuskantar ƙalubale ga amincinsu.
Amma, jawabi game da tarihi zai yi saurin gajiyar da yara. Ka ba yaranka daman yin magana. Alal misali, kana iya tambayar yaronka ya zaɓi ƙasar da yake so, ya yi bincike a kan tarihi na tsarin Allah na wannan ƙasar, kuma ya gabatar wa iyalin abin da ya koya. A cikin ikilisiyarku, ƙila akwai Kiristoci da suke bauta cikin aminci da daɗewa da za ka iya gayyata su yi bauta ta iyali da yamma tare da ku. Wataƙila ’yarku tana iya gana da su kuma ta yi musu tambayoyi, ta sa su faɗi labaransu. Ko kuma ka sa yaronku ya zana hotuna na aukuwa na musamman, kamar su gina ofishin reshe da taro na ƙasashe ko kuma yin amfani da garmaho a hidimar gida gida.
Ka Koya Aikin “Kowace Gaɓa”
Manzo Bulus ya gwada ikilisiyar Kirista da “dukan jiki, haɗaɗe kuwa ta wurin taimakon kowace gaɓa, bisa ga aikin kowane yanki gwargwadon ma’auni nasa, yana sa ƙaruwar jiki zuwa ginin kansa cikin ƙauna.” (Afis. 4:16) Koyon yadda jikin ’yan Adam yake aiki yana ƙara sa mu nuna godiya da kuma daraja Mahaliccinmu. Haka nan ma, sa’ad da muka bincika yadda ikilisiya a dukan duniya take aiki, muna yin mamaki game da “hikima iri iri ta Allah.”—Afis. 3:10.
Jehobah ya kwatanta yadda ƙungiyarsa, har sashenta na samaniya take aiki. Alal misali, ya gaya mana cewa ya fara nuna wa Yesu Kristi wahayi, wanda ya “aiko ya shaida ta ta bakin mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna.” (R. Yoh. 1:1, 2) Idan Allah ya bayyana yadda sashen ƙungiyarsa da ba a gani yake aiki, shin ba zai so mu fahimci yadda “kowace gaɓa” yake aiki a duniya ba?
Alal misali, ba da daɗewa ba, mai kula da da’ira zai ziyarci ikilisiyarku, ka tattauna da iyalinka ayyuka da masu kula masu ziyara suke yi da kuma albarka da suke samu a wannan aikin. Yaya suke taimakon kowannenmu? Wasu tambayoyi da za ku iya tattauna su ne: Me ya sa yake da muhimmanci a ba da rahoton hidimar fage? Yaya ake tallafa wa ƙungiyar Allah da kuɗi? Yaya aka tsara Hukumar Mulki, kuma yaya take yin tanadin abinci na ruhaniya?
Sa’ad da muka fahimci yadda aka tsara mutanen Jehobah, za mu amfana aƙalla a hanyoyi uku: Za mu ƙara nuna godiya ga waɗanda suke aiki tuƙuru a madadinmu. (1 Tas. 5:12, 13) Hakan zai motsa mu mu tallafa wa shirye-shirye na tsarin Allah. (A. M. 16:4, 5) A ƙarshe, za mu ƙara tabbata da waɗanda suke shugabanci yayin da muke gani shawarwari da ke bisa Nassi da shiri da ake yi.—Ibran. 13:7.
“Ku Lura da Fadodinta”
“Ku kewaye cikin Sihiyona, ku zaga bayanta. Ku lissafta hasumiyanta. Ku duba ganuwanta da kyau, Ku lura da fadodinta; domin ku faɗa wa tsara mai-tasowa.” (Zab. 48:12, 13) A wannan ayar, marubucin wannan zabura ya aririci Isra’ilawa su ziyarci Urushalima sosai. Ka yi tunanin yadda iyalai Isra’ilawa da suka yi tafiya zuwa birni mai tsarki don bukukuwa da ake yi kowace shekara kuma suka gani haikalinsa mai ban al’ajabi suke faɗin abubuwa masu tamani da suka gani. Babu shakka hakan ya motsa su su “faɗa wa tsara mai-tasowa.”
Ka yi tunanin sarauniyar Sheba, wadda da farko take shakkar rahoton sarauta mai ban al’ajabi na Sulemanu da hikimarsa mai girma. Mene ne suka tabbatar mata cewa abubuwan da ta ji gaskiya ne? “Ban gaskanta maganarsu ba” in ji ta, “sai lokacinda na zo, idanuna kuma sun gan shi.” (2 Laba. 9:6) Hakika, abin da muka gani da ‘idanunmu’ za su iya shafanmu sosai.
Ta yaya za ka iya taimaka wa yaranka su ga al’ajuban ƙungiyar Jehobah da ‘idanunsu’? Idan akwai ofishin reshe na Shaidun Jehobah kusa da gidanku, ku yi ƙoƙari ku ziyarce wurin. Alal misali, Mandy da Bethany sun yi girma a wurin da ke da nisan miloli 900 daga gidan Bethel da ke ƙasarsu. Duk da haka, iyayensu suna ziyarar wannan wurin don su yi zagaya a kai a kai, musamman sa’ad da yaransu mata suke girma. Sun bayyana: “Kafin mu ziyarci Bethel, muna ganin cewa tsofaffi ne kawai suke zama a wurin, kuma ba a dariya. Amma mun haɗu da matasa da suke aiki tuƙuru ga Jehobah kuma suna jin daɗin aikin! Mun fahimci cewa ba wurin da muke zama ba ne kawai ƙungiyar Jehobah take ba, kuma duk lokacin da muka ziyarci Bethel muna kusantar Jehobah kuma hakan na motsa mu mu ƙara son bauta masa.” Sanin ƙungiyar Allah sosai ya motsa Mandy da Bethany su soma hidimar majagaba, har ma aka gayyace su su yi hidima a Bethel na ɗan lokaci.
Muna da wata hanya na ‘ganin’ ƙungiyar Jehobah, hanyar da Isra’ila ta dā ba ta da shi. A shekarun baya, mutanen Allah sun samu bidiyo da faifan DVD da suka nuna fannoni dabam dabam na ƙungiyar Allah, kamar su: Jehovah’s Witnesses—Organized to Share the Good News, Our Whole Association of Brothers, To the Ends of the Earth da kuma United by Divine Teaching. Sa’ad da kai da iyalinka kuka ga yadda waɗanda suke Bethel da masu kai agaji da masu hidima a wata ƙasa da ’yan’uwa da suke shirya da kuma tsara taron gunduma suke aiki sosai, babu shakka za ku ƙara nuna godiya ga ’yan’uwanci na dukan duniya.
Kowace ikilisiya na mutanen Allah tana da hakki mai muhimmanci wajen wa’azin bishara da tallafa wa Kiristoci da ke yankinta. Amma kai da iyalinka ku keɓe lokaci don ku tuna da “’yan’uwanku da ke cikin duniya.” Wannan zai taimake ka da yaranka “kuna tabbatawa cikin bangaskiyarku,” da fahimtar cewa kuna da dalilin yin farin ciki.—1 Bit. 5:9.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 18]
Ƙungiyar Allah Jigon da Ya Dace a Nazarta
Muna da tanadodi masu yawa da za su taimaka mana mu ƙara koya game da tarihi da kuma yadda ƙungiyar Jehobah take aiki. Tambayoyi na gaba za su iya taimaka maka ka soma:
☞ Ta yaya masu kula masu ziyara suka soma aikinsu na zamani?—Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1996 shafuffuka na 9 zuwa 14.
☞ Mene ne yake da muhimmanci game da “Ranar Yara” a Taro na Tsarin Allah da aka yi a shekara ta 1941?—Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2001, shafi na 30.
☞ Ta yaya aka tsara Hukumar Mulki?—Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2008, shafi na 29.