Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali
Ka Tattauna da Yaranka Game da Jima’i
Alicia,a wata matashiya, ta ce: “A wasu lokatai ina ɗokin sanin wani abu game da jima’i, amma ina jin cewa idan na tambayi iyaye na, suna iya soma tunanin cewa ni ’yar iska ce.”
Inez, mahaifiyar Alicia, ta ce: “Ina son in zauna kuma in tattauna da ’ya ta game da jima’i, amma ba ta da lokaci.” Da wuya ta samu lokacin tattaunawa.”
A YAU, akwai hotuna da labarai game da jima’i a ko’ina—a talabijin, a fina-finai, da kuma a allon talla. Kamar dai inda kawai ake ɗaukan tattauna wannan batun a matsayin haram shi ne a tsakanin iyaye da yara. “Na so a ce iyaye sun san irin tsoro da kuma kunyar da ake ji a tattauna batun jima’i da su,” in ji wani matashi a ƙasar Kanada mai suna Michael. “Tattauna batun da abokinmu ya fi sauƙi.”
Sau dayawa, kamar yaransu, iyaye suna jinkirin tattauna batun da ya shafi jima’i. A cikin littafin ta Beyond the Big Talk, malamar lafiyar jiki, Debra W. Haffner ta ce: “Iyaye da yawa sun gaya mini cewa sun sayo wa yaransu littafin da ya tattauna batun jima’i ko balaga, sun ajiye littafin a ɗakin yaron, kuma ba su sake tattauna batun ba.” Haffner ta ce abin da suke gaya wa yara a bayyane yake: “Muna son ku san batutuwan da suka shafi jikinku da kuma jima’i; amma ba ma son mu tattauna su da ku.”
Idan kai iyaye ne, kana bukatar ka nuna wani hali dabam. Hakika, yana da muhimmanci sosai ka tattauna da yaranka game da jima’i. Ka yi la’akari da waɗannan dalilan guda uku:
1. Ma’anar da duniya ta ba jima’i ta canja. “Mutane ba sa tunanin cewa mata da miji ne kawai ya kamata su yi jima’i,” in ji James ɗan shekara 20. “A yanzu, akwai yin jima’i ta hanyar tsotsar al’aura, luwaɗi, jima’i ta hanyar intane, har da ‘aika saƙo da hotunan lalata’ ta wayar tarho.”
2. Yaranku suna iya soma jin labaran ƙarya tun suna ƙanana. “Za su soma jin labarai game da jima’i da zarar sun soma makaranta,” in ji wata uwa mai suna Sheila, “kuma ba za su fahimci irin ra’ayin da kake son su kasance da shi ba.”
3. Yaranku suna da tambayoyi game da jima’i amma zai yi wuya su soma tattauna batun da ku. “A gaskiya, ban san yadda zan soma tattauna batun jima’i da iyaye na ba,” in ji Ana ’yar shekara 15 daga ƙasar Brazil.
Babu shakka, tattaunawa da yaranku game da jima’i sashe ne na hakkin da Allah ya ɗora wa iyaye. (Afisawa 6:4) Hakika, yin hakan zai iya kasancewa da wuya da kuma kunya ga ku da yaranku. Amma gaskiyar ita ce, matasa da yawa sun yarda da Danielle ’yar shekara 14, wadda ta ce: “Muna son mu koyi batun da ya shafi jima’i daga iyayenmu, ba daga malami ko talabijin ba.” Idan haka ne, ta yaya za ku iya tattaunawa da yaranku game da wannan batu mai muhimmanci amma mai wuya?b
Ku Yi La’akari da Shekarunsu
Sai dai in sun ware kansu daga mutane gabaki ɗaya, yara suna soma jin labarin jima’i ne tun suna ƙanana. Abin da ma ya fi ta da hankali a waɗannan “kwanaki na ƙarshe,” shi ne miyagun mutane suna daɗa “mugunta gaba gaba.” (2 Timotawus 3:1, 13) Abin baƙin ciki, manya suna yi wa yara masu yawa fyaɗe.
Saboda haka, yana da muhimmanci ku soma ilimantar da yaranku tun suna ƙanana. “Idan ka jira har sai sun kusan zama matasa,” in ji wata mahaifiya a ƙasar Jamus mai suna Renate, “suna iya ƙin tattaunawa da kai a fili saboda wani irin halin ƙin yin magana da ke tattare da balaga.” Sirrin shi ne gaya wa yara bayanan da ya dace da shekarunsu.
Don ƙananan yaran da ba su shiga makaranta ba: Ku mai da hankali ga koya musu ainihin sunaye masu kyau na al’aura, kuma ku nanata cewa kada su yarda wani ya taɓa su. “Na soma koya wa ɗana sa’ad da yake ɗan shekara uku,” in ji wata uwa a ƙasar Mexico mai suna Julia. “Sanin cewa malamai, masu reno, ko kuma yaran da suka girme shi za su iya cutar da shi ya sa na damu ƙwarai. Yana bukatar ya san yadda zai kāre kansa daga baƙi.”
GWADA WANNAN: Ku koya wa ɗanku ya mai da martani da gaba gaɗi idan wani yana ƙoƙarin yin wasa da al’aurar shi ko ita. Alal misali, kuna iya koyar da ɗanku ya ce: “Ka daina! Zan kai ƙararka!” Ka tabbatar wa ɗanka cewa kai ƙarar abin da ya faru yana da kyau, ko da mutumin ya yi alƙawarin ba shi kyauta ko ya yi masa barazana.c
Don yaran da ke makarantar firamare: Ku yi amfani da waɗannan shekarun a matsayin zarafin daɗa wa ɗanku abubuwan da ya sani da sannu-sannu. “Kafin ku soma tattaunawa da su,” in ji wani mahaifi mai suna Peter, “ku tabbata cewa kun san abin da suka sani da kuma ko suna son ƙarin bayani. Kada ku cusa musu tattaunawar. Hakan zai faru cikin sauƙi idan kuna kasancewa tare da yaranku a kai a kai.”
GWADA WANNAN: Ku riƙa ɗan tattaunawa da su a kai a kai, maimakon ku zaunar da su sau ɗaya kuna doguwar tattaunawa. (Kubawar Shari’a 6:6-9) Da haka ba za ku cika yaranku da bayanai ba. Ƙari ga haka, yayin da suke girma za su san bayanin da suke bukata daidai da shekarunsu.
Don Matasa: Wannan shi ne lokacin da ya kamata ku tabbata cewa ɗanku yana da cikakken ilimi game da fasalolin zahiri, na motsin zuciya, da kuma na ɗabi’a game da jima’i. “’Yan mata da maza a makarantarmu suna ɗaukan kwanan gida,” in ji Ana ’yar shekara 15, wadda aka yi ƙaulinta ɗazu. “Ina ganin a matsayina na Kirista, ina bukatar cikakken ilimi game da wannan batun. Duk da cewa ana jin kunyar tattauna batun jima’i, ya zama dole in san wannan batun.”d
Ku kula: Matasa suna iya ƙin yin tambayoyi domin suna tsoron cewa iyayensu suna iya soma tunanin cewa sun iskance. Abin da wani uba mai suna Steven ya gano ke nan. “Ɗanmu ba ya son ya tattauna game da jima’i,” in ji shi. “Amma daga baya mun gano cewa yana tunanin muna zargin halinsa ne. Mun bayyana masa dalla-dalla cewa ba wai muna tattauna waɗannan batutuwan ba ne domin muna zarginsa; a’a, muna son mu tabbata ne cewa yana shirye ya ƙi duk wani mugun tasirin da ke kewaye da shi.”
GWADA WANNAN: Maimakon ku yi wa ɗanku matashi tambayoyi kai tsaye game da wani batu da ya shafi jima’i, ku tambayi shi ko ita ra’ayin abokan ajinsu a kan batun. Alal misali, kuna iya cewa: “Mutane da yawa a yau suna ganin cewa tsotsar al’aurar wani ba yin jima’i ba ne ba. Ra’ayin abokan ajinka ke nan?” Irin waɗannan tambayoyi na kai tsaye suna iya sa ɗa ko ’yarku matashiya ta tattauna batun da ku kuma shi ko ita ta furta ra’ayoyinta.
Magance Jinkiri da Kunya
A gaskiya, tattaunawa da yaranku game da jima’i zai iya kasancewa ɗaya daga cikin ayyuka mafi kunya da ku iyaye za ku fuskanta. Amma kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu. “Da shigewar lokaci,” in ji wata uwa mai suna Diane, “za ka daina jin kunyar, kuma tattaunawa da ɗanka game da jima’i zai iya ƙarfafa dangantakarku.” Steven, da aka yi ƙaulinsa ɗazu, ya yarda da hakan. “Tattauna batutuwa masu kunya kamar jima’i zai kasance da sauƙi idan ka kafa salon fitowa fili sa’ad da kuke tattauna duk wasu batutuwan da suka taso a cikin iyali,” in ji shi, ya kuma daɗa: “Ba wai za a daina jin kunyar ba ne gabaki ɗaya, amma tattaunawa babu wani ɓoye-ɓoye shi ne ginshiƙin duk wata iyalin Kirista na ƙwarai.”
[Hasiya]
a An canja sunaye a wannan talifin.
b Wannan talifin zai tattauna bukatar tattaunawa da yaranku game da jima’i. Talifi na gaba zai tattauna yadda za ku tarbiyyantar da su sa’ad da kuke wannan tattaunawar.
c An ɗauko shi ne daga shafi na 171 na littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
d Ku yi amfani da shafuffuka na 1-5, 28, 29, da 33 na littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Na 2, wanda Shaidun Jehobah suka wallafa, don tattaunawa game da jima’i da ɗanku matashi.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 14]
KA TAMBAYI KANKA . . .
Ku karanta furcin da ke gaba na matasa daga kewayen duniya, sai ku tambayi kanku tambayoyin da ke biye.
• “Iyayena sun gaya mini in karanta talifofin da suke magana game da jima’i kuma in yi musu duk wasu tambayoyin da nake da ita. Amma na so a ce za su tattauna batun ne da ni.”—Ana, Brazil.
Me ya sa kuke ganin yana da muhimmanci ku yi fiye da ba ɗanku littafi ya karanta kawai?
• “Na ji abubuwa masu yawa game da yin jima’i a hanyar da ba ta dace ba, abubuwan da nake ganin babana bai sani ba. Hankalinsa zai tashi idan na yi masa tambayoyi a kansu.”—Ken, Kanada.
Waɗanne fargaba kuke ganin ɗanku ko ’yarku take da su game da tattauna damuwar shi ko ita da ku?
• “Sa’ad da na samu gaba gaɗin yi wa iyayena tambaya game da jima’i, amsar da suka ba ni ya nuna kamar suna zargi na ne, sun ce, ‘Me ya sa za ki yi irin wannan tambayar? Ko wani abu ya faru ne?’”—Masami, Japan.
Sa’ad da ɗanku ya yi muku tambaya game da jima’i, ta yaya irin halin da kuka nuna zai iya sa tattaunawa a nan gaba ya yi sauƙi ko ya yi wuya?
• “Zan ji daɗi idan iyayena suka gaya mini cewa sa’ad da suke kamar ni, su ma sun yi irin waɗannan tambayoyin kuma ba laifi ba ne in yi tambayoyi.”—Lisette, France.
Ta yaya za ku iya kwantar da hankalin ɗanku, saboda shi ko ita ta tattauna da ku game da jima’i?
• “Mahaifiyata tana yi mini tambayoyi game da jima’i, amma da murya mai daɗi. Ina ganin cewa hakan yana da muhimmanci, don kada ɗan ya ji cewa ana yi masa shari’a ne.”—Gerald, France.
Wane irin murya ne kuke amfani da shi sa’ad da kuke tattaunawa da ɗanku game da jima’i? Kuna bukatar ku yi gyara?