Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 pp. 7-11
  • Matasa, Ku Yi Tsayayya Da Matsi Na Tsara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Ku Yi Tsayayya Da Matsi Na Tsara
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Matsin Bin Tsaranku Yake da Iko?
  • “Ku Yi wa Kanku Ƙwanƙwanto”
  • ‘Ku Yi Tunanin Abin da Za Ku Amsa’
  • Ku Yi ‘Shirin da Zai Kai ga Biyan Bukata’
  • ‘Ku Yi Murna a Cikin Ƙuruciyarku’
  • Ta Yaya Zan Ƙi Matsi Daga Tsarana?
    Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi
  • Ka Tuna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 pp. 7-11

Matasa, Ku Yi Tsayayya Da Matsi Na Tsara

“Bari zancenku kullum ya kasance . . . gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.”—KOL. 4:6.

1, 2. Ta yaya matasa da yawa suke ji game da kasancewa dabam da wasu, kuma me ya sa?

BABU shakka, kun taɓa jin wannan furci “matsi na tsara” kuma kun fuskance shi. A wani lokaci, wataƙila wani ya aririce ku ku yi wani abin da kuka san cewa ba shi da kyau. Yaya kuke ji sa’ad da hakan ya faru? “A wani lokaci nakan ji kamar na ɓace, ko kuma na zama kamar sauran abokan makaranta na don kada na fita dabam” in ji Christopher ɗan shekara 14.

2 Tsaranku suna matsa muku sosai ne? Idan haka ne, me ya sa? Zai iya zama cewa kuna son su amince da ku ne? Jin hakan ba laifi ba ne. Hakika, har manya ma suna son tsaransu su amince da su. Babu wanda da yake son a ƙi shi. Wasu mutane za su ƙi ka idan kana son ka yi abin da yake da kyau. Har Yesu ma ya fuskanci hakan. Duk da haka, Yesu a koyaushe ya yi abin da yake da kyau. Yayin da wasu suka bi shi kuma suka zama almajiransa, wasu sun rena Ɗan Allah kuma ba su “maishe shi wani abu ba.”—Isha. 53:3.

Yaya Matsin Bin Tsaranku Yake da Iko?

3. Me ya sa abin kuskure ne ku bi mizanan tsaranku?

3 A wani lokaci, za ku so ku bi mizanan tsaranku don kada su ƙi ku. Hakan zai zama kuskure. Bai kamata Kiristoci su “zama yara, waɗanda ana wofar da su” ba. (Afis. 4:14) Mutane suna rinjayar yara da sauƙi. Amma, a matsayin matasa, wata rana za ku zama manya. Saboda haka, idan kun gaskata cewa mizanan Jehobah don amfaninku ne, kun cancanci ku yi rayuwa bisa abin da kuka gaskata. (K. Sha 10:12, 13) Idan ba ku yi hakan ba kuna barin wasu su yi muku ja-gora a rayuwarku. Hakika, idan kun faɗa wa matsi daga mutane, za ku zama kamar ’yar tsana da ake wa ja-gora.—Karanta 2 Bitrus 2:19.

4, 5. (a) Yaya Haruna ya faɗa wa matsi na tsara, kuma waɗanne darussa kuka koya daga wannan? (b) Waɗanne hanyoyi ne tsaranku za su iya yin amfani da su don su matsa muku?

4 Akwai lokacin da ɗan’uwan Musa Haruna, ya faɗa wa matsi na tsara. Sa’ad da Isra’ilawa suka matsa masa ya ƙera musu allah, ya yi hakan. Haruna ba raunanne ba ne. Kafin wannan lokacin, ya goyi bayan Musa sa’ad da suka fuskanci Fir’auna, mutum mafi iko a ƙasar Masar. Haruna ya yi magana da gaba gaɗi, ya sanar masa da saƙon Allah. Amma yayin da ’yan’uwansa Isra’ilawa suka matsa masa, Haruna ya yi hakan. Matsi na tsara yana da tasiri sosai! Ya yi wa Haruna sauƙi ya tsayayya wa sarkin ƙasar Masar maimakon ya tsayayya wa tsaransa.—Fit. 7:1, 2; 32:1-4.

5 Kamar yadda misalin Haruna ya nuna, matsi na tsara ba ya shafan matasa kawai kuma ba matsalar waɗanda suke da niyyar yin mugunta ba ne kawai. Matsi na tsara zai iya shafan waɗanda suke so su yi abin da yake da kyau, har da kai. Tsaranku suna iya tilasta muku ku yi abin da ba shi da kyau ta wajen tsoratar da ku, zaginku, ko kuma yi muku ba’a. Babu kowanne irin matsi na tsara da yake da sauƙi a fuskance shi. Yin nasara wajen tsayayya wa matsi yana somawa ta wurin kasancewa da tabbaci ga abin da kuka gaskata.

“Ku Yi wa Kanku Ƙwanƙwanto”

6, 7. (a) Me ya sa kasancewa da tabbaci ga imaninku yake da muhimmanci, kuma yaya za ku koya kasancewa da wannan tabbaci? (b) Waɗanne tambayoyi ne za ku iya yi wa kanku don ku ƙarfafa tabbacinku?

6 Don ku iya yin tsayayya da matsi na tsara, da farko kuna bukatar ku kasance da tabbaci cewa imaninku da mizananku sun dace. (Karanta 2 Korintiyawa 13:5.) Ko da ku masu jin kunya ne, kasancewa da tabbaci zai taimake ku ku kasance da gaba gaɗi. (2 Tim. 1:7, 8) Amma, ko da mutum yana da gaba gaɗi, zai iya kasance masa da wuya ya yi tsayayya da abin da bai gaskata sosai ba. Ya kamata ku tabbatar wa kanku cewa abin da aka koya muku daga cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. Ku soma da bincika muhimman abubuwa. Alal misali, kun gaskata da Allah kuma kun ji yadda wasu suka furta dalilin da ya sa suka gaskata da wanzuwarsa. Saboda haka, ku tambayi kanku, ‘Mene ne ya tabbatar mini cewa Allah yana wanzuwa?’ Dalilin wannan tambayar ba domin ya sa ku shakka ba amma don ya ƙarfafa bangaskiyarku ne. Hakazalika, ku tambayi kanku, ‘Yaya na san cewa Nassosi hurarru ne daga Allah?’ (2 Tim. 3:16) ‘Me ya sa na gaskata cewa waɗannan “kwanaki na ƙarshe” ne?’ (2 Tim. 3:1-5) Me ya sa na gaskata cewa mizanan Jehobah don amfani na ne?—Isha. 48:17, 18.

7 Kuna iya yin jinkirin yi wa kanku irin waɗannan tambayoyi, kuna jin tsoron cewa ba za ku samu amsoshin ba. Wannan zai zama kamar ƙin kallon gejin māi da ke gaban motarku don kuna jin tsoron cewa zai nuna “Babu māi”! Idan babu māi a cikin tankin, kuna bukatar ku bincika domin ku yi wani abu game da shi. Hakazalika, ya fi kyau ku san inda kuke rashin tabbaci kuma ku yi gyara.—A. M. 17:11.

8. Ku bayyana yadda za ku ƙarfafa tabbacinku cewa umurnin Allah a guje wa fasikanci tafarki ne mai kyau da za ku bi.

8 Alal misali. Littafi Mai Tsarki ya aririce ku “ku guje wa fasikanci.” Ku tambayi kanku, ‘Me ya sa yake da kyau na bi wannan umurni mai kyau?’ Ku yi tunanin dukan dalilai da suka sa tsaranku suke yin irin wannan hali. Ku yi tunani a kan dalilai dabam dabam da suka sa mutumin da yake yin fasikanci yake “yi wa jiki nasa zunubi.” (1 Kor. 6:18) Yanzu ku gwada dalilin, kuma ku tambayi kanku: ‘Wane tafarki mafi kyau ne zan bi? Shin yin lalata kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu?’ Ku daɗa yin tunani a kan wannan batun, ku tambayi kanku, ‘Yaya zan ji idan na yi lalata?’ Da farko za ku iya samun amincewar wasu cikin tsaranku, amma yaya za ku ji daga baya idan kuna tare da iyayenku ko kuma ’yan’uwa Kiristoci a Majami’ar Mulki? Yaya za ku ji sa’ad da kuke ƙoƙari ku yi addu’a ga Allah? Za ku so ku yasar da matsayi mai kyau da Allah don ku faranta wa abokan ajinku rai?

9, 10. Ta yaya kasancewa da tabbaci game da imaninku zai taimaka muku ku yi magana da gaba gaɗi sa’ad da kuke tare da tsaranku?

9 Idan ku matasa ne, kuna lokacin rayuwarku da ‘hankalinku’ yake wayewa sosai. (Karanta Romawa 12:1, 2.) Ku yi amfani da wannan lokacin na rayuwanku ku yi tunani sosai game da abin da ya sa zama Shaidun Jehobah yake da muhimmanci a gare ku. Irin wannan bimbinin zai taimaka maku ku ƙarfafa tabbacin imaninku. Sa’an nan, sa’ad da kuka fuskanci matsi na tsara, za ku iya mayar da amsa nan da nan da tabbaci. Za ku ji yadda wata matashiya Kirista ta ji, wadda ta ce: “Sa’ad da na ƙi matsi na tsara, ina sanar wa mutane ko wane irin mutum ne ni. Addini na yana da muhimmanci a gare ni, ba suna ba ce kawai. Tushe ne na makasudai na da ɗabi’a na da kuma dukan rayuwata.

10 Hakika, yana bukatar ƙoƙarce-ƙoƙarce don ku manne wa abin da kuka san cewa yana da kyau. (Luk 13:24) Za ku iya yin mamaki ko kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu. Amma ku tuna wannan: Idan kuka bayyana kamar kuna roƙo ko kuma kuna jin kunya don ƙudurinku na yin abin da yake daidai, mutane za su lura da hakan, kuma mai yiwuwa za su daɗa matsa muku. Amma, idan kun yi magana da gaba gaɗi, za ku yi mamaki yadda tsaranku za su yi saurin daina matsa muku.—Gwada Luka 4:12, 13.

‘Ku Yi Tunanin Abin da Za Ku Amsa’

11. Wane amfani ne ake samu ta wurin yin shiri don fuskantar matsi na tsara?

11 Wani mataki mai muhimmanci na tsayayya wa matsi shi ne yin shiri. (Karanta Misalai 15:28.) Kasancewa a shirye yana nufin yin tunani tun da wuri game da yanayi da wataƙila za su taso. Wani lokaci yin shiri tun da wuri zai taimaka muku ku guji yanayi da zai iya tasowa. Alal misali, a ce kun hangi rukunin abokan makarantarku suna shan sigari. Mai yiwuwa za su ba ku sigari. Da yake kun hangi matsalar, mene ne za ku iya yi? Misalai 22:3 ya ce: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya.” Ta wurin bin wata hanya, za ku iya guje wa saduwa da su gabaki ɗaya. Wannan ba batun jin tsoro ba ne; tafarkin hikima ne.

12. Yaya za ku amsa sa’ad da kuke fuskantar matsi na tsara?

12 Idan ba za ku iya guje wa wani yanayi kamar yadda aka kwatanta a baya kuma ba fa? A ce wani daga cikin tsaranku ya yi muku tambaya da mamaki cewa, “Har yanzu ba ka da budurwa?” Abin da ya fi kyau shi ne ku bi umurnin da ke Kolosiyawa 4:6: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.” Kamar yadda wannan nassi ya nuna, yadda za ka amsa wannan tambayar zai dangana ga yanayin. Wataƙila ba ku bukatar ku ba da dogon jawabi daga Littafi Mai Tsarki. Mai yiwuwa amsa na kai tsaye zai isa. Alal misali, wajen amsa tambaya game da ko kuna da budurwa, kuna iya cewa, “Ban taɓa yin budurwa ba,” ko kuma, “Wannan batun kaina ne.”

13. Me ya sa fahimi yake da muhimmanci sa’ad da kuke amsa ba’a na tsaranku?

13 Sau da yawa Yesu yana ba da ɗan amsa sa’ad da ba za a cim ma abu mai kyau ba ta wajen faɗin abubuwa da yawa. Hakika, sa’ad da Hirudus ya yi wa Yesu tambaya, bai ce kome ba. (Luk 23:8, 9) Sau da yawa yin shiru ne hanyar da ta fi kyau na bi da tambayoyi da ba su dace ba. (Mis. 26:4; M. Wa. 3:1, 7) A wani ɓangare kuma, kuna iya fahimtar cewa wani da gaske yana son ya san imaninku game da ɗabi’ar jima’i ko idan wannan a dā yana zagin ku. (1 Bit. 4:4) A wannan yanayin, bayyana imaninku sosai da ke bisa Littafi Mai Tsarki ya dace. Idan haka ne, kada ku ƙi yin hakan don tsoro. A ko da yaushe ku kasance ‘a shirye ku ba da amsa.’—1 Bit. 3:15.

14. Ta yaya za ku mayar da matsi na tsara da basira a cikin wasu yanayi?

14 A wasu yanayi kuna iya mayar musu da matsin. Amma, dole ne ku yi ƙoƙari ku yi hakan da basira. Alal misali, idan abokin makarantarku ya matsa muku ku amshi sigari daga wajensa, kuna iya cewa, “Na gode,” sai ku daɗa, “Haba, kana shan sigari?” Ka ga yadda ka mayar masa da matsin? Maimakon ka soma bayyana dalilin da ya sa ba ka shan sigari, ka tilasta wa tsaranka ya yi tunani a kan dalilin da ya sa yake shan sigari.a

15. A wane lokaci ne ya dace ku tafi ku bar tsaranku waɗanda suke ƙoƙari su matsa muku, kuma me ya sa?

15 Idan duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcenku, tsaranku suka ci gaba da matsa muku kuma fa? A irin wannan yanayin, ya fi kyau ku bar wurin. Idan kun ci gaba da zama, za ku kasance cikin hadarin karya amincinku a wata hanya. Saboda haka, ku bar wurin. Za ku iya yin hakan ba tare da jin cewa ba ku yi nasara ba. Ballantana ma, kun sha kan yanayin. Ba ku zama ’yar tsana ba a wajen tsaranku, kuma kun faranta zuciyar Jehobah.—Mis. 27:11.

Ku Yi ‘Shirin da Zai Kai ga Biyan Bukata’

16. Ta yaya matsi zai iya fitowa daga wurin wasu da suke da’awa su Kiristoci ne?

16 A wasu lokaci, wasu matasa da suke da’awa su bayin Jehobah ne suna iya matsa muku ku sa hannu a cikin ayyuka da ba su da kyau. Alal misali, idan kun isa wurin liyafa da irin wannan matashin ya shirya kuma kun gane cewa babu manya da suke kula da liyafar kuma fa? Ko kuwa matashin da yake da’awar cewa shi Kirista ne ya kawo giya zuwa wurin liyafa, kuma kai da sauran matasan da ke wajen ba ku isa shan giya ba kuma fa? Yanayi da yawa suna iya tasowa da za ku bukaci ku bi lamirinku da Littafi Mai Tsarki ya koyar. Wata matashiya Kirista ta ce: “Ni da ƙanwata mun bar gidan silima da ake nuna batsa. Wasu cikin rukunin sun ci gaba da kallo. Iyayenmu sun yaba mana don abin da muka yi. Amma, wasu a cikin rukunin sun yi fushi domin mun sa su bayyana kamar ba su da halin kirki.”

17. Sa’ad da kuka halarci liyafa, waɗanne matakai masu kyau ne za ku ɗauka don ku manne wa mizanan Allah?

17 Kamar yadda labarai na baya suka nuna, bin lamirinku da Littafi Mai Tsarki ya koyar yana iya sa ku cikin yanayi da zai sa ku ji kunya. Amma ku manne wa abin da kuka gaskata cewa shi ne tafarkin da ya dace. Ku yi shiri. Idan za ku tafi wurin liyafa, ku shirya hanyar da za ku fita sa’ad da wataƙila ba a tsara abubuwa yadda kuke tsammani ba. Wasu matasa sun shirya da iyayensu cewa kiransu ta waya shi ne kawai suke bukata don su dawo gida da wuri. (Zab. 26:4, 5) Irin wannan ‘shiri zai kai ga biyan bukatarku.’—Mis. 21:5, Littafi Mai Tsarki.

‘Ku Yi Murna a Cikin Ƙuruciyarku’

18, 19. (a) Me ya sa za ku kasance da tabbaci cewa Jehobah yana son ku yi farin ciki? (b) Yaya Jehobah yake ji game da waɗanda suke yin tsayayya da matsi na tsara?

18 Jehobah ya halicce ku don ku ji daɗin rayuwa, kuma yana son ku kasance da farin ciki. (Karanta Mai-Wa’azi 11:9.) Ku tuna cewa abin da tsaranku suke fuskanta ‘daɗin nishatsin zunubi na ’yan kwanaki’ ne kawai. (Ibran. 11:25) Abin da Allah na gaskiya yake so ku samu ya fi hakan. Yana son ku kasance da farin ciki har abada. Saboda haka, sa’ad da kun fuskanci gwajin yin wani abu da kuka san cewa ba shi da kyau a idanun Allah, ku tuna cewa a ƙarshe, abin da Jehobah yake bukata a gare ku a koyaushe don amfaninku ne.

19 A matsayin matasa, kuna bukatar ku fahimci cewa ko idan tsaranku za su amince da ku, shekaru da yawa nan gaba wataƙila yawancinsu ba za su ma iya tuna sunanku ba. Akasin haka, sa’ad da kuka yi tsayayya da matsi na tsara, Jehobah yana lura da hakan, kuma ba zai iya taɓa mancewa da ku ba ko kuma amincinku. Zai ‘buɗe muku sakatan sama, ya zuba muku da albarka, har da ba za a sami wurin da za a karɓa ba.’ (Mal. 3:10) Bugu da ƙari, yana ba ku ruhunsa mai tsarki a yalwace don ya sauya duk wani kasawa da kuke da shi yanzu. Hakika, Jehobah zai iya taimaka maku ku yi tsayayya da matsi daga tsaranku!

[Hasiya]

a Ka duba taswira mai jigo “Peer-Pressure Planner” (Yadda Zan Yi Shirin Fuskantar Matsi na Tsara) a cikin littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na biyu, shafuffuka na 132 da 133.

Ka Tuna?

• Wane iko ne matsi na tsara zai iya kasancewa da shi?

• Ta yaya tabbaci yake taimako wajen yin tsayayya da matsi na tsara?

• Yaya za ku yi shiri don ku yi tsayayya da matsi na tsara?

• Yaya kuka sani cewa Jehobah yana lura da amincinku?

[Hoton da ke shafi na 8]

Me ya sa Haruna ya yarda ya yi ɗan maraƙi na zinariya?

[Hoton da ke shafi na 10]

Ku yi shiri, ku shawarta abin da za ku faɗa tun da wuri

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba