Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 12/15 p. 6
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Matasa, Ku Yi Tsayayya Da Matsi Na Tsara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 12/15 p. 6

Ka Tuna?

Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

• Wane mala’ika ne Allah ya aika ya kasance a gaba sa’ad da ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar? (Fit. 23:20, 21)

Daidai ne mu gaskata cewa Ɗan fari na Allah, wanda daga baya ya zama Yesu ne wannan mala’ika, wanda ‘sunan Jehobah yake cikinsa.’—9/15, shafi na 21.

• Game da bauta ta gaskiya, waɗanne hujjoji ne Allah ba ya amincewa da su?

‘Yana da wuya ainun. Ba na son na yi. Ina da ayyuka da yawa. Ban cancanta sosai ba. Wani ya ɓata mini rai. Waɗannan ba ƙwaƙƙwarar dalilai ba ne na rashin cika umurnan Allah.—10/15, shafuffuka na 12-15.

• A waɗanne hanyoyi ne za ka sa taron Kirista ya kasance da ban ƙarfafa a gare ka da kuma wasu?

Ka shirya tun da wuri. Ka riƙa halarta a kai a kai. Ka isa a kan lokaci. Ka zo a shirye. Ka guji abubuwa da suke raba hankali. Ka yi kalami. Ka yi furci a taƙaice. Ka yi aikin makaranta. Ka yaba wa ’yan’uwa. Ka yi tarayya kafin taron da kuma bayan haka.—10/15, shafi na 22.

• Mene ne za mu iya koya daga yadda Haruna ya faɗa wa matsi na tsara?

Sa’ad da Musa ba ya nan, Isra’ilawa sun matsa wa Haruna ya ƙera musu allah. Ya faɗa wa matsin kuma ya yi hakan. Wannan ya nuna cewa matsi na tsara ba ya shafan matasa kawai. Zai iya shafan manya ma, waɗanda suke so su yi abin da yake da kyau. Muna bukatan mu yi tsayayya da mugun matsi na tsara.—11/15, shafi na 8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba