Hujjoji Yaya Jehobah Yake Ɗaukansu?
“MACEN da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci,” in ji mutumin. Matar ta ce, “macijin ya ruɗe ni, ni kuwa na ci.” Waɗannan kalaman da iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u suka furta ga Allah, su ne somawar dogon tarihin ba da hujjoji na ’yan Adam.—Far. 3:12, 13.
Hukuncin Jehobah a kan Adamu da Hauwa’u don rashin biyayya da suka yi da gangan ya nuna cewa bai yarda da hujjoji da suka ba da ba. (Far. 3:16-19) Don hakan, za mu kammala ne cewa Jehobah ba ya amince da dukan hujjoji? Ko kuwa yana amincewa da wasu hujjoji? Idan haka ne, yaya za mu san bambancinsu? Don mu samu amsar, bari mu fara yin la’akari da ma’anar hujja.
Hujja dalili ne da aka ba da don a bayyana abin da ya sa aka yi wani abu, da ya sa ba a yi wani abu ba, ko kuma dalilin da ya sa ba za a yi wani abu ba. Hujja za ta iya zama bayani da aka ba da don wata kasawa kuma za ta iya ƙunshi neman gafara na gaske da ke sa a sauƙaƙa ko kuma a yafe wa mutum laifinsa. Amma, kamar yadda yake a batun Adamu da Hauwa’u, hujja za ta iya zama dalilin ƙarya da aka ba da don a ɓoye ainihin abin da ya faru. Tun da yake sau da yawa hujjoji da ake ba da irin wannan ne, ana yawan yin shakkar su.
Sa’ad da muke ba da hujjoji, musamman idan sun shafi hidimarmu ga Allah, dole ne mu guji ‘ruɗin kanmu’ da tunanin ƙarya. (Yaƙ. 1:22) Saboda haka, bari mu yi la’akari da wasu misalan Littafi Mai Tsarki da ƙa’idodi da za su taimaka mana mu “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—Afis. 5:10.
Abin da Allah Yake Bukatan Mu Yi
A cikin Kalmar Allah muna samun takamammu umurni da mu a matsayin mutanen Jehobah muke bukatan mu yi biyayya da su. Alal misali, umurnin Kristi “ku tafi fa, ku almajirtarda dukan al’ummai” umurni ne da har ila ya shafi dukan mabiyan Kristi. (Mat. 28:19, 20) Hakika, cika wannan umurnin yana da muhimmanci sosai har manzo Bulus ya ce: “Kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba.”—1 Kor. 9:16.
Duk da haka, wasu da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su da daɗewa har ila suna jinkirin yin wa’azi na bisharar Mulkin Allah. (Mat. 24:14) Wasu da suke aikin wa’azi a dā sun daina yin hakan. Waɗanne dalilai ne waɗanda ba sa saka hannu a aikin wa’azi suke ba da wa? Mene ne Jehobah ya yi wa waɗanda suka yi jinkirin yin biyayya ga takamammu umurninsa a dā?
Hujjoji da Jehobah Ba Ya Amincewa da Su
“Yana da wuya ainun.” Zai yi kamar aikin wa’azi yana da wuya ainun, musamman ga waɗanda suke jin kunya. Amma, ka yi la’akari da abin da za a iya koya daga misalin Yunana. Ya samu aikin da ya yi masa wuya sosai, wato, Jehobah ya gaya masa ya sanar ga Nineba game da halaka da ke tafe. Ba shi da wuya a ga dalilin da ya sa ya yi wa Yunana wuya ya yi wannan aikin. Nineba babban birnin Assuriya ne, kuma an san mutanen Assuriya da yin zalunci. Wataƙila Yunana ya yi mamaki: ‘Yaya zan kasance tsakanin waɗannan mutanen?’ ‘Mene ne za su yi mini?’ Ba da daɗewa ba sai ya gudu. Duk da haka, Jehobah bai amince da hujjar Yunana ba. Maimakon haka, Jehobah ya sake gaya masa ya je ya yi wa mutanen Nineba wa’azi. A wannan lokacin, Yunana ya yi aikinsa da gaba gaɗi, kuma Jehobah ya albarkaci sakamakon.—Yun. 1:1-3; 3:3, 4, 10.
Idan kana tunani cewa aikin yin wa’azin bishara ya yi maka wuya ainun, ka tuna cewa “ga Allah abubuwa duka ya yiwu.” (Mar. 10:27) Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ƙarfafa ka sa’ad da ka ci gaba da roƙon taimakonsa kuma zai albarkace ka idan ka yi ƙoƙari ka kasance da gaba gaɗi don ka cika hidimarka.—Luk 11:9-13.
“Ba na son na yi.” Mene ne za ka yi idan ba ka sha’awar yin hidimarka na Kirista? Ka tuna cewa Jehobah zai iya aikata a gare ka kuma ya shafi sha’awoyinka. Bulus ya ce: “Allah ne yana aiki a cikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma, zuwa abin da ya gamshe shi.” (Filib. 2:13) Saboda haka, za ka iya gaya wa Jehobah ya sa ka so yin nufinsa. Sarki Dauda ya yi hakan nan. Ya roƙi Jehobah: ‘Ka sa na yi tafiya cikin gaskiyarka.’ (Zab. 25:4, 5) Za ka iya yin hakan ta wajen yin addu’a sosai cewa Jehobah ya motsa ka ka so yin abin da zai faranta masa rai.
Hakika, sa’ad da muka gaji ko kuma muka yi sanyin gwiwa, a wani lokacin muna iya tilasta wa kanmu mu halarci taro a Majami’ar Mulki ko kuma mu fita hidima. Idan haka ne, ya kamata ne mu kammala cewa ba ma ƙaunar Jehobah da gaske? A’a. Bayin Allah masu aminci a dā ma sun ƙoƙarta don su yi nufin Allah. Alal misali, Bulus ya faɗa cewa ‘yana dandaƙin jikinsa,’ a alamance, don ya yi biyayya ga umurnin Allah. (1 Kor. 9:26, 27) Saboda haka sa’ad da muka tilasta wa kanmu mu yi hidima, za mu iya samun tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu. Me ya sa? Domin mun tilasta wa kanmu mu yi nufin Allah don dalilin da ya dace, wato don muna ƙaunar Jehobah. Ta yin hakan, muna ba da amsa ga da’awar da Shaiɗan ya yi cewa bayin Allah za su ƙi Allah idan aka gwada su.—Ayu. 2:4.
“Ina da ayyuka da yawa.” Idan ba ka sa hannu a hidima domin kana ji cewa kana da ayyuka da yawa, yana da muhimmanci sosai ka sake bincika abubuwa da suka fi maka muhimmanci. “Ku fara biɗan mulkinsa,” in ji Yesu. (Mat. 6:33) Don ka bi wannan ƙa’idar ja-gorar, kana bukatan ka sauƙaƙa salon rayuwarka ko kuma ka rage lokacin yin nishaɗi don ka yi amfani da shi a hidima. Hakika, nishaɗi da biɗan namu abubuwa suna da nasu amfani, amma ba ƙwaƙƙwarar hujja ba ce na ƙyale hidimar. Bawan Allah na saka Mulkin farko a rayuwarsa.
“Ban cancanta sosai ba.” Kana iya jin cewa ba ka cancanci zama mai hidimar bishara ba. Wasu bayin Jehobah masu aminci a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki suna jin ba su cancanci yin aiki da Jehobah ya gaya musu ba. Ka yi la’akari da misalin Musa. Sa’ad da ya samu takamaiman umurni daga Jehobah, Musa ya ce: “Ya Ubangiji, ni ba mai-iya baki ba ne, ko dā, ko kuwa yanzu da ka yi magana da bawanka: gama mai-nauyin baki ne ni, harshena kuma da nawwa.” Ko da Jehobah ya tabbatar masa, Musa ya amsa: “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka aike ta hannun wanda za ka aike.” (Fit. 4:10-13) Yaya Jehobah ya aikata?
Jehobah bai gaya wa Musa kada ya yi wannan aikin ba. Amma, Jehobah ya naɗa Haruna ya taimaka wa Musa wajen yin wannan aikin. (Fit. 4:14-17) Bugu da ƙari, a shekaru na gaba, Jehobah ya taimaki Musa kuma ya yi masa tanadin duk abin da yake bukata don ya yi nasara wajen cika aikin da Allah ya ba shi. A yau, za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai sa ’yan’uwa masu bi da suka manyanta su taimaka maka ka cika hidimarka. Fiye da kome, Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa Jehobah zai sa mu cancanci yin aikin da ya umurce mu mu yi.—2 Kor. 3:5; ka duba akwatin nan “Shekaru da na Fi Farin Ciki a Rayuwa.”
“Wani ya ɓata mini rai.” Wasu sun daina fitan hidima ko kuma halartar taron ikilisiya domin an ɓata musu rai, suna tunani cewa Jehobah zai amince da wannan hujjar don daina ayyuka na ruhaniya da suka yi. Ko da yake daidai ne mu yi fushi sa’ad da wani ya ɓata mana rai, amma hakan ƙwaƙƙwarar hujja ne na daina yin ayyuka na Kirista kuwa? Wataƙila Bulus da ɗan’uwansa mai bi Barnaba sun yi fushi sosai bayan da “jayayya ta tashi.” (A. M. 15:39) Amma dukansu sun daina yin hidima domin hakan? Ko kaɗan!
Hakan nan ma, idan wani ɗan’uwa mai bi ya yi maka laifi, ka riƙa tunawa cewa magabcinka da yake son ya cinye ka shi ne Shaiɗan ba ɗan’uwanka ajizi ba. Amma, Iblis ba zai yi nasara ba idan ka ‘tsaya masa fa, kana tabbatawa cikin bangaskiyarka.’ (1 Bit. 5:8, 9; Gal. 5:15) Idan kana da irin wannan bangaskiya, ba za ka “kunyata ba.”—Rom. 9:33.
Muna da Iyaka ga Abin da Za Mu Iya Yi
Daga waɗannan ’yan misalai na ba da hujjoji, ya kasance a bayyane cewa babu ƙwaƙƙwarar dalili na Nassi na ba da hujjar rashin cika takamaimai umurni na Jehobah, har da umurnin yin wa’azin bishara. Duk da haka, muna iya samun dalilai masu kyau na rashin yin hidima sosai. Wasu hakki na Nassi suna iya rage yawan lokaci da za mu keɓe don aikin wa’azi. A wani lokaci kuma, muna iya gajiya ainun da gaske ko kuma mu yi rashin lafiya sosai da ba za mu iya yin yawan yadda za mu so mu yi a hidimar Jehobah ba. Amma, Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa Jehobah ya san sha’awarmu kuma yana yin la’akari da kasawarmu.—Zab. 103:14; 2 Kor. 8:12.
Saboda haka, muna bukatan mu mai da hankali don kada mu mugun shari’anta wa kanmu ko kuma wasu a irin waɗannan batutuwa. Manzo Bulus ya rubuta: “Wanene kai da ka ke zartar wa bawan wani? tsayawarsa ko fāɗuwarsa ga nasa ubanɗaki ne.” (Rom. 14:4) Maimakon mu riƙa gwada yanayinmu da na wasu, ya kamata mu tuna cewa “kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Rom. 14:12; Gal. 6:4, 5) Sa’ad da muka yi addu’a ga Jehobah kuma muka gabatar masa da hujjojinmu, bari mu yi hakan da “kyakkyawan lamiri.”—Ibran. 13:18.
Abin da Ya Sa Bauta wa Jehobah Yake Sa Mu Farin Ciki
Dukanmu muna iya bauta wa Jehobah da farin ciki saboda ko da mene ne yanayinmu a rayuwa, bukatunsa sun dace kuma ana iya cim ma su. Me ya sa za mu iya faɗin haka?
Kalmar Allah ta ce: “Kada ka hana alheri ga waɗanda ya wajibce su, lokacin da yana cikin ikon hannunka da za ka aika.” (Mis. 3:27) Mene ne ka lura a wannan karin magana game da bukatun Allah? Jehobah bai ba ka umurni ka yi ƙoƙari ka yi daidai da ƙarfin ɗan’uwanka ba amma yana bukata ka bauta masa da abin da ke ‘cikin ikon hannunka.’ Hakika, kowanenmu ko yaya ne rashin ƙarfinmu ko kuma yawan ƙarfinmu, muna iya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu.—Luk 10:27; Kol. 3:23.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 14]
“Shekaru da Na Fi Farin Ciki a Rayuwa”
Ko da muna da kasawa na zahiri ko na sosuwar zuciya, bai kamata mu yi saurin kammala cewa waɗannan za su hana mu sa hannu sosai a hidima. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru da Ernest, wani ɗan’uwa Kirista a ƙasar Kanada.
Ernest yana i’ina kuma yana jin kunya sosai. Bayan ya yi ciwon baya mai tsanani, ya daina aikinsa na gine-gine. Ko da yake ya naƙasa, sabon yanayinsa ya ƙyale shi ya ba da lokaci sosai a hidima. Ƙarfafawa da aka ba da a taron ikilisiya cewa a yi aikin majagaba na ɗan lokaci ya sa ya kasance da sha’awar yin hakan. Amma, bai ji cewa ya cancanta yin irin wannan hidimar ba.
Don ya tabbatar wa kansa cewa aikin majagaba na ɗan lokaci ya fi ƙarfinsa, ya cika fam na yin hidimar majagaba na ɗan lokaci na wata guda. Cim ma hidimar da ya yi ya ba shi mamaki sosai. Sai ya gaya wa kansa, ‘Na san cewa ba zan sake iya yin sa kuma ba.’ Don ya tabbatar da abin da ya faɗa, sai ya sake cika fam na yin hidima a wata na biye kuma ya sake cim ma hidimarsa.
Ernest ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci na shekara guda, kuma ya ce, “Na tabbata cewa ba zan taɓa iya yin hidimar majagaba na kullum ba.” Don ya tabbatar da abin da ya faɗa, sai ya cika fam ɗin yin hidimar majagaba na kullum. Ya yi mamaki sosai sa’ad da ya gama shekara ta farko ta hidimar majagaba na kullum. Ya tsai da shawara ya ci gaba, kuma ya samu albarkar yin hidimar majagaba na kullum har na tsawon shekara biyu da farin ciki, bayan hakan sai ya mutu, sanadiyyar ciwonsa da ya daɗa tsanani sosai. Amma kafin mutuwarsa, sau da yawa yakan gaya wa waɗanda suka ziyarce shi da hawaye a idanunsa cewa, “Waɗannan shekaru da na bauta wa Jehobah a matsayin majagaba ne na fi farin ciki a rayuwa.”
[Hoton da ke shafi na 13]
Za mu iya sha kan kowace irin matsala da za ta hana mu yin hidima
[Hoton da ke shafi na 15]
Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka bauta masa da dukan ranmu, ta wajen yin dukan abin da yanayinmu ya ƙyale mu mu yi