Ku Koyar Da Yaranku
Sirrin da Za Ka Iya Gaya wa Wasu
AN TAƁA gaya maka wani sirri kuwa—a Akwai guda da zan so in gaya maka. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “[“asiri mai tsarki” NW] tun daga zamanu marasa-matuƙa.” (Romawa 16:25) Da farko Allah kaɗai ne ya san wannan “asirin mai tsarki.” Bari mu ga yadda Allah ya tabbatar da cewa wannan sirrin ya bayyanu ga mutane masu yawa.
Da farko, ka san abin da tsarki ke nufi?— Kalmar nan tsarki tana nufin abin da ke da tsabta, ko na musamman. Saboda haka, ana kiran sirrin nan sirri mai tsarki ne domin ya fito ne daga Allah, wanda mai tsarki ne. Su wane ne kake tunanin cewa suna son su san wannan sirri na musamman?— Mala’iku sun yi hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Su ne kuwa abubuwan da mala’iku ke ɗokin gani.” Hakika, suna son su fahimci wannan sirrin mai tsarki.—1 Bitrus 1:12, Littafi Mai Tsarki.
Sa’ad da Yesu ya zo duniya, ya yi magana game da sirri mai tsarki kuma ya soma bayyana shi. Ya gaya wa almajiransa: ‘A gareku am bada asirin mulkin Allah.’ (Markus 4:11) Sirrin mai tsarki game da mene ne?— Game da Mulkin Allah ne, wanda Yesu ya koya mana mu roƙa a cikin addu’a!—Matta 6:9, 10.
Yanzu bari mu ga yadda Mulkin Allah ya zama sirri “tun daga zamanu marasa-matuƙa” har sa’ad da Yesu ya zo duniya kuma ya soma bayyana shi. Bayan Adamu da Hauwa’u sun karya dokar Allah kuma aka fid da su daga cikin lambun Adnin, bayin Allah sun fahimci cewa har ila Allah zai mai da dukan duniya ta zama aljanna. (Farawa 1:26-28; 2:8, 9; Ishaya 45:18) Sun rubuta irin farin cikin da mutane za su more a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah.—Zabura 37:11, 29; Ishaya 11:6-9; 25:8; 33:24; 65:21-24.
Yanzu, ka yi tunani game da Sarkin Mulkin Allah. Ka san ko wane ne Allah ya zaɓa ya zama Sarki?— Ɗansa ne, “Sarkin Salama,” Yesu Kristi. ‘Mulkin za ya kasance a kafaɗarsa,’ in ji Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 9:6, 7) Dole ne ni da kai mu sami ‘sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu.’ (Kolosiyawa 2:2) Muna bukatar mu san cewa Allah ya ɗauki ran mala’ika na farko (Ɗa na ruhu) wanda ya halitta kuma ya saka ransa a cikin Maryamu. Wannan Ɗan, wanda mala’ika ne mai iko, shi ne wanda Allah ya aiko duniya a matsayin hadaya domin mu samu rai madawwami.—Matta 20:28; Yohanna 3:16; 17:3.
Ƙari ga hakan, muna bukatar mu san wasu ƙarin abubuwa game da wannan sirrin bayan cewa Allah ya zaɓi Yesu ya zama Sarkin Mulkinsa. Sashen wannan sirri mai tsarki shi ne cewa wasu mata da maza za su kasance a sama tare da Yesu da aka ta da daga matattu. Za su yi sarauta ne tare da Yesu a sama!—Afisawa 1:8-12.
Bari mu koyi sunayen wasu da za su yi sarauta tare da Yesu a sama. Yesu ya gaya wa manzanninsa masu aminci cewa zai je sama ya shirya musu wuri. (Yohanna 14:2, 3) Idan ka duba nassosin da ke gaba, za ka ga sunayen kaɗan daga cikin maza da mata da za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin Babansa.—Matta 10:2-4; Markus 15:39-41; Yohanna 19:25.
An daɗe ba a san adadin mutanen da za su yi sarauta a sama tare da Yesu a matsayin sashen Mulkinsa ba. Amma a yanzu mun san adadin. Ka san adadin?— Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mutane 144,000 ne. Wannan ma sashen sirri mai tsarki ne.—Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4.
Ka yarda cewa wannan “asirin mulkin Allah” sirri ne mai ban al’ajabi da ya kamata mutum ya sani?— Idan haka ne, bari mu ƙoƙarta mu koyi dukan abubuwan da ya kamata mu sani game da shi don mu bayyana shi ga mutane masu yawa.
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yara, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata kuma ka ƙarfafa yaron ya faɗi abin da ke zuciyarsa.
TAMBAYOYI:
▪ Mene ne ake kiran sirrin da muka tattauna, kuma me ya sa ake kiransa haka?
▪ Mene ne wannan sirrin, kuma wane ne ya soma koyar da shi?
▪ Mene ne wasu daga cikin sirrin nan da ka koya?
▪ Ta yaya za ka iya bayyana wannan sirrin mai tsarki ga aboki?
[Hoton da ke shafi na 23]
Mene ne kake tunanin cewa mala’ikun suke son su gano?