Wakilci Na Cika Nufin Allah
“[Allah] da ke aikata dukan abu bisa ga shawarar nufinsa.”—AFISAWA 1:11.
1. Me ya sa duka ikilisiyoyin Shaidun Jehobah za su taru a ranar 12 ga watan Afrilu 2006?
ARANAR Laraba da yamma, 12 ga watan Afrilu ta shekara ta 2006, kusan mutane miliyan 16 ne za su taru su kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji. A dukan wurin da suka taru, za a ajiye gurasa marar yisti bisa teburi, alamar jikin Kristi, da kuma ruwan inabi, mai nuna alamar jinin Kristi da aka zubar. A kusan ƙarshen jawabinsa bayan da ya bayyana muhimmancin Tuna Mutuwar Yesu, za a miƙa wa waɗanda suka halarci taron, da farko gurasa sai kuma ruwan inabi. A cikin ikilisiyar Shaidun Jehobah, mutane kaɗan ne cikin waɗanda suka halarci taron za su ci isharar. A wurare da yawa kuma, babu wanda zai ci isharar tsakanin waɗanda suka halarci taron. Me ya sa Kiristoci kaɗan ne kawai waɗanda suke da begen rayuwa a sama suke cin isharar, amma kuma mutane masu yawa da suke da begen rayuwa a duniya har abada ba sa ci?
2, 3. (a) Ta yaya Jehobah ya yi halitta bisa ga nufinsa? (b) Don menene Jehobah ya halicci duniya da mutane?
2 Jehobah Allah ne mai manufa. Ta wurin cika manufarsa, yana “aikata dukan abubuwa bisa ga shawarar nufinsa.” (Afisawa 1:11) Da farko ya halicci Ɗansa makaɗaici. (Yohanna 1:1,14; Ru’ya ta Yohanna 3:14) Ta wurin Ɗansa, Jehobah ya halicci iyali na ruhu, daga baya kuma ya halicci sararin samaniya ta zahiri da duniya da kuma mutum da ke cikinsa.—Ayuba 38:4, 7; Zabura 103:19-21; Yohanna 1:2, 3; Kolosiyawa 1:15, 16.
3 Jehobah bai halicci duniya ta zama wurin gwada mutane don ƙara girman iyalinsa na ruhu a sama ba, kamar yadda cocin Kiristendom suke koyarwa. Ya halicce ta “domin wurin zama,” nufin zuciyarsa ke nan. (Ishaya 45:18) Allah ya halicci duniya domin mutane, mutane kuma domin duniya. (Zabura 115:16) Manufarsa ita ce duniya duka ta zama aljanna, cike da mutane masu adalci, waɗanda za su ginata, su kuma kula da ita. Ba a taɓa yin wani zancen zuwa sama da ma’aurata na farko ba.—Farawa 1:26-28; 2:7, 8, 15.
An Ƙalubalanci Manufar Jehobah
4. Ta yaya aka ƙalubalanci hanyar nuna ikon mallaka ta Jehobah a farkon tarihin ’yan adam?
4 Wani ruhu ɗan Allah ya yi tawaye kuma ya tsayayyawa nufin Jehobah, ya yi ƙeta da ’yancin da Allah ya ba shi. Ya lalata salama ta dukan masu nuna biyayya ga ikon mallaka na Jehobah. Shaiɗan ne ya ruɗi ma’aurata na farko suka nemi hanyar samun ’yancin kansu daga wurin Allah. (Farawa 3:1-6) Ko da yake Shaiɗan bai musanci ikon Jehobah ba, amma ya tuhumi hanyar da Jehobah yake nuna ikon mallakarsa da kuma ’yancinsa na sarauta. Muhimmancin wannan batu na ikon mallaka na Jehobah ya fara ne a farkon tarihin ’yan adam a duniya.
5. Wane batu ne aka tayar, kuma ya shafi su waye?
5 Bayan batun ikon mallaka, Shaiɗan ya tada wani batu a zamanin Ayuba. Shaiɗan ya tuhumi dalilin da ya sa halittun Jehobah suke yi masa biyayya kuma suke bauta masa. Shaiɗan yana da’awar cewa suna bauta wa Allah ne saboda sonkai, idan har aka gwada su, za su juya wa Allah baya. (Ayuba 1:7-11; 2:4, 5) Ko da yake wannan batu saboda mutane masu bauta wa Allah ne, batun ya shafi ’ya’yan Allah na sama, har da ɗan Jehobah makaɗaici.
6. Ta yaya Jehobah ya nuna amincinsa don ya cika manufarsa da sunansa?
6 Domin ya cika manufarsa tare da ma’anar sunansa, Jehobah ya mai da kansa ya zama Annabi kuma Mai ceto.a Ya ce wa Shaiɗan: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Farawa 3:15) Ta wurin zuriyar “Macen,” ko kuma ƙungiyarsa ta samaniya Jehobah zai amsa ƙalubalancin Shaiɗan ya kuma yi wa zuriyar Adamu tanadin begen samun ceton rai.—Romawa 5:21; Galatiyawa 4:26, 31.
“Asirin Nufinsa”
7. Wane manufarsa ne Jehobah ya bayyana ta wurin manzo Bulus?
7 A cikin wasiƙarsa ga Kiristoci na Afisus, manzo Bulus ya yi bayani game da yadda Jehobah yake yin abubuwa don cika manufarsa. Bulus ya rubuta: “Ya sanashe mu asirin nufinsa. Bisa ga yardarsa da ya nufa a cikinsa zuwa wakilci na cikar wokatai, shi tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.” (Afisawa 1:9, 10) Manufar Jehobah shi ne ya kawo haɗaɗiyar sararin samaniya cike da halittu da za su yi biyayya ga ikon mallakarsa. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Za a tsarkake sunansa, Shaiɗan kuwa zai zama maƙaryaci, sa’an nan nufin Allah zai cika “a duniya kamar yadda ake yi a sama.” (Matta 6:10)
8. Menene ma’anar kalmar da aka fassara ta “wakilci”?
8 “Yardar” Jehobah, za ta cika ta wurin ‘wakilcinsa.’ A nan Bulus ya yi amfani da kalmar da ke nufin “tafiyar da iyali.” Yana nufin hanyar da Allah zai gyara abubuwa ne amma ba gwamnati kamar ta Mulkin Almasihu ba.b Hanya mafi kyau da Allah zai gyara abubuwa don kammala manufarsa “asiri” ce da za ta ɗauki ƙarnuka ana sanar da ita a hankali.—Afisawa 1:10; 3:9.
9. Ta yaya Jehobah ya bayyana asirin nufinsa?
9 Ta wurin alkawuransa, Jehobah ya bayyana yadda manufarsa game da Zuriyar da aka yi alkawarinta a Adnin za ta cika. Alkawarin da ya yi wa Ibrahim ya nuna cewa Zuriyar da aka yi alkawarinta za ta zo a iyalin Ibrahim za ta kuma zama hanyar da “dukan al’umman duniya” za su sami albarka. Wannan alkawarin ya nuna cewa wasu za su haɗa kai da ainihin zuriyar. (Farawa 22:17, 18) Doka ta alkawari da aka yi da Isra’ila ta zahiri ta bayyana cewa nufin Jehobah ne ya kafa “Mulki na firistoci.” (Fitowa 19:5, 6) Alkawarin da aka yi da Dauda ya nuna cewa Zuriyar za ta zama Shugaban Mulkin har abada. (2 Sama’ila 7:12, 13; Zabura 89:3, 4) Idan har doka ta alkawari ta kai Yahudawa ga Almasihu, Jehobah zai bayyana wata hanya ta cika manufarsa. (Galatiyawa 3:19, 24) Mutanen da za su zauna tare da ainihin zuriyar za su zama “Mulki na Firistoci” za su kuma shiga cikin “sabon alkawari” su zama sabon “Isra’ila,” ta ruhaniya.—Irmiya 31:31-34; Ibraniyawa 8:7-9.c
10, 11. (a) Ta yaya Jehobah ya bayyana zuriyar da aka annabta? (b) Me ya sa Ɗan Allah makaɗaici ya zo duniya?
10 Lokaci ya kai ga zuriyar ta fito a duniya daidai da wakilcin Allah. Jehobah ya aiko mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu cewa za ta haifi ɗa da za a kira shi Yesu. Mala’ika ya ce mata: “Shi za ya zama mai girma, za a ce da shi Ɗan Maɗaukaki: Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki kuma bisa gidan Yakubu har abada; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luka 1:32, 33) Daga baya an fahimci Zuriyar da aka yi alkawarinta.—Galatiyawa 3:16; 4:4.
11 Ɗan Jehobah makaɗaici zai zo duniya don a gwada shi har iyaka. Hanya mafi kyau ta amsa tambayar da Shaiɗan ya yi tana hannun Yesu. Zai iya kasancewa da aminci ga Ubansa kuwa? Wannan asiri ne. Daga baya manzo Bulus ya bayyana matsayin Yesu: “Asirin ibada da girma yake: Shi wanda ya bayyana cikin jiki, ya bara cikin ruhu, ya ganu ga mala’iku, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, cikin duniya aka bada gaskiya gareshi aka karɓe shi bisa cikin daraja.” (1 Timothawus 3:16) Har sa’ad da ya mutu, Yesu ya mai da martani ga ƙalubalancin Shaiɗan ta wurin amincinsa marar jijjiga. Amma da wasu asirin da suka rage da za a bayyana su dalla-dalla.
“Asiran Mulkin Allah”
12, 13. (a) Menene wani fasalin “asirin Mulkin Allah”? (b) Menene ya sa Jehobah ya zaɓi mutane kaɗan su je sama?
12 Sa’ad da yake wa’azi a Galili, Yesu ya nuna cewa Asirin yana da nasaba ta kusa da Mulkin Almasihu. Ya gaya wa almajiransa: “Ku aka ba da za ku san asiran mulkin sama [“Mulkin Allah,” Markus 4:11].” (Matta 13:11) Wani fasalin asirin ya kai ga Jehobah ya zaɓi “ƙaramin garke,” wato mutane 144,000 waɗanda za su kasance da Ɗansa su zama ɓangaren zuriyar su kuma yi mulki tare da shi a sama.—Luka 12:32; Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4.
13 Da yake an halicci mutane su zauna a duniya, ana bukatar “sabon halitta” daga Jehobah domin su tafi sama. (2 Korinthiyawa 5:17) Manzo Bitrus da ke cikin waɗanda aka zaɓa su je sama ya rubuta: “Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ya maya haihuwarmu bisa ga jinƙansa mai-girma zuwa bege mai-rai ta wurin tashin Yesu Kristi daga matattu, zuwa gādo mara-ruɓewa mara-ƙazamtuwa, wanda ba shi yanƙwanewa. Ajiyayye a sama dominku.”—1 Bitrus 1:3, 4
14. (a) Ta yaya waɗanda ba Yahudawa ba ne suka samu shiga cikin “asiran Mulkin Allah”? (b) Me ya sa muke iya fahimtar “zurfafan al’amuran Allah”?
14 Wani fasalin asiri game da Mulkin Allah na nan gaba shi ne, Allah zai haɗa da mutane waɗanda ba Yahudawa ba ne cikin mutane kaɗan da za a zaɓa su yi mulki da Kristi a sama. Bulus ya bayyana wannan “shirin,” ko kuma hanyar gyara manufar Jehobah: “Wanda ba a sanar ma ’ya’yan mutane dake cikin waɗansu tsararaki ba, kamar yadda yanzu an bayana shi ga manzanninsa masu-tsarki da, annabawa cikin ruhu, cewa, cikin Kristi Yesu al’ummai abokan tarayya ne cikin gādo, gaɓaɓuwa kuma na jikin, abokan tarayya kuma cikin alkawari ta wurin bishara.” (Afisawa 3:5, 6) An bayyana wa “tsarkankun manzani” ma’anar asirin Allah. Haka ma a yau, idan ba da taimakon ruhu mai-tsarki ba, da ba mu fahimci “zurfafa na Allah” ba.—1 Korinthiyawa 2:10; 4:1; Kolosiyawa 1:26, 27.
15, 16. Me ya sa Jehobah ya zaɓi abokan Yesu da za su yi mulki da shi daga cikin mutane?
15 “Mutum zambar ɗari da zambar arba’in da huɗu” da aka gani tsaye da “Ɗan Rago” a kan Dutsen Sihiyona an “fanso su daga duniya,” “aka fanso waɗannan daga cikin mutane su zama nunan fari ga Allah, da Ɗan Ragon,” Yesu Almasihu. (Ru’ya ta Yohanna 14:1-4) Jehobah ya zaɓi na farko cikin ’ya’yansa na samaniya ya zama ainihin zuriya na alkawarin da aka yi a Adnin, amma me ya sa ya zaɓi abokan Yesu da za su yi mulki tare da shi daga cikin mutane? Manzo Bulus ya yi bayani cewa Jehobah ya zaɓi wannan adadi kaɗan ne ‘bisa ga nufinsa,’ wato “bisa ga nufinsa na alheri.”—Romawa 8:17, 28-30; Afisawa 1:5,11; 2 Timothawus 1:9.
16 Manufar Jehobah shi ne ya tsarkake sunansa ya kuma ɗaukaka ikon mallakarsa a dukan duniya. Ta wurin wannan “wakilci” wanda ba za a iya kwatantawa ba ko kuma hanyar gyara abubuwa, Jehobah ya aiki Ɗansa na fari zuwa duniya, inda aka gwada shi har mutuwarsa. Bugu da ƙari, Jehobah ya ƙudura cewa gwamnatin Mulkin Almasihu na Ɗansa zai haɗa da mutane da suka ɗaukaka ikon mallakarsa har mutuwarsu.—Afisawa 1:8-12; Ru’ya ta Yohanna 2:10, 11.
17. Me ya sa ya kamata mu yi murna cewa Kristi da abokan sarautarsa sun taɓa rayuwa irin ta mutane?
17 Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga zuriyar Adamu sa’ad da ya sa Ɗansa ya zo duniya, kuma ya zaɓa a cikin mutane waɗanda za su zama abokan gādo a Mulkinsa. Ta yaya wannan zai shafi waɗanda suka nuna amincinsu ga Jehobah, daga Habila har zuwa yau? Da shi ke an haife su cikin zunubi da mutuwa, mutane ajizai na bukatar warkarwa ta ruhaniya da ta jiki da kuma kamiltaccen rai, wanda Allah ya nufa ga mutane da farko. (Romawa 5:12) Abin farin ciki ne ga dukan waɗanda suke jiran su sami rai na har abada a duniya su sani cewa sarkinsu zai nuna masu ƙauna, zai kuma fahimce su kamar yadda ya yi wa almajiransa a lokacin da ya yi rayuwarsa a duniya! (Matta 11:28, 29; Ibraniyawa 2:17, 18; 4:15; 7:25, 26) Abin farin ciki ne su fahimci cewa abokan Kristi da za su zama sarakuna da firistoci a sama a dā maza da mata ne masu bangaskiya waɗanda suka fuskanci ajizanci da ƙalubale na rayuwa kamar yadda muke fuskantarsu!—Romawa 7:21-25.
Jehobah Ba Ya Kasa Cika Nufinsa
18, 19. Me ya sa muka fahimci kalmar Bulus a cikin Afisawa 1:8-11, kuma me za mu tattauna a talifi na gaba?
18 Yanzu mun fahimci ma’anar kalmar Bulus da ya gaya wa Kiristoci shafaffu, kamar yadda aka nuna a Afisawa 1:8-11. Ya ce Jehobah ya nuna musu “asirin nufinsa,” cewa an “maishe [su] abin gādo” tare da Kristi, da kuma “ƙadararru bisa ga nufin wannan dake aikata dukan abu bisa ga shawarar nufinsa.” Mun lura cewa wannan ya yi daidai da kyakkyawan “wakilcin” Jehobah don cika nufinsa. Kuma wannan ya taimakemu mu fahimci abin da ya sa mutane kaɗan ne cikin waɗanda suka halarci taron Jibin Maraice na Ubangiji suke cin isharar.
19 A talifi na gaba, za mu ga abin da Tuna mutuwar Yesu take nufi ga Kiristocin da suke da begen zuwa sama. Kuma za mu koyi abin da ya sa miliyoyi da suke da begen rayuwa a duniya suke son su san abin da Tuna mutuwar take nunawa.
[Hasiya]
a Sunan Allah yana nufin “Yana sa Shi Zama.” Jehobah yana iya zama ko menene don ya cika nufinsa.—Fitowa 3:14.
b Kalmar Bulus ta nuna cewa “wakilci” ya fara ne a zamaninsa, amma Nassosi sun nuna cewa Mulkin Almasihu ya fara ne a shekara ta 1914.
c Don ƙarin bayani game da yadda alkawarin nan ya shafi manufar Allah, dubi Hasumiyar Tsaro ta 1, ga watan Fabrairu shekara ta 1989, shafuffuka na 10-15 na Turanci.
Domin Maimaitawa
• Me ya sa Jehobah ya halicci duniya ya saka mutum a cikinsa?
• Me ya sa ya dace a gwada ɗan makaɗaici a duniya?
• Me ya sa Jehobah ya zaɓi waɗanda za su yi sarauta da Yesu daga cikin mutane?