Tambayoyi Daga Masu Karatu
Littafin Farawa 6:3 ya ce: “Ruhuna ba za ya riƙa ja da mutum har abada ba, gama shi kuma nama ne: amma kwanakin ransa shekara ɗari da ashirin za su zama.” Shin Jehobah ya rage tsawon ran ’yan Adam ne zuwa shekara 120, kuma shin Nuhu ya yi wa’azi na tsawon wannan shekarun ne?
Amsa ga waɗannan tambayoyi biyu a’a ne.
Kafin Rigyawar, ’yan Adam da yawa sun yi rayuwa na tsawon ƙarnuka da yawa. Nuhu yana da shekara 600 sa’ad da aka yi Rigyawar, kuma ya rayu har tsawon shekara 950. (Far. 7:6; 9:29) Wasu mutane da aka haifa bayan Rigyawar sun yi rayuwa fiye da shekara 120, Arpachshad ya rasu sa’ad da yake da shekara 438, Shelah kuma sa’ad da yake da shekara 433. (Far. 11:10-15) Duk da haka, a zamanin Musa, tsawon rayuwar mutane ya ragu zuwa shekara 70 ko kuma 80. (Zab. 90:10) Saboda haka, Farawa 6:3 ba ta kafa wa ’yan Adam tsawon rayuwa na shekara 120 ba.
To, Allah ne ya gaya wa Nuhu kalamai da ke cikin wannan ayar cewa ya faɗakar da mutane game da halakar da za a yi shekara 120 nan gaba? A’a. Allah ya yi magana ga Nuhu lokatai da yawa. Mun karanta ayoyi goma cikin wannan labarin cewa ‘Allah kuma ya ce wa Nuhu, Matuƙar dukan abu mai-rai a gare mu ta yi; gama duniya cike ta ke da zalunci.’ A shekaru bayan hakan, Nuhu ya gama aiki mai girma na gina jirgin, kuma a wannan lokacin ‘Ubangiji ya ce wa Nuhu, ka zo kai da dukan gidanka cikin jirgi.’ (Far. 6:13; 7:1) Kuma akwai wasu misalai sa’ad da Jehobah ya gaya wa Nuhu wasu abubuwa.—Far. 8:15; 9:1, 8, 17.
Amma abin da muka karanta a Farawa 6:3 dabam ne don bai ambata Nuhu ba kuma bai ce Allah yana masa magana ba. Ana iya fahimta cewa Allah ya furta nufinsa ko kuma ƙudurinsa kawai. (Gwada Farawa 8:21.) Yana da muhimmanci a lura cewa a rubuce-rubucen tarihi na abubuwa da suka faru da daɗewa kafin zamanin Adamu, mun samu furci kamar su: “Allah kuma ya ce.” (Far. 1:6, 9, 14, 20, 24) Hakika, Jehobah bai yi magana ga ’yan Adam a duniya ba, don ba a halicce mutum ba tukuna.
Saboda haka, ya dace a kammala cewa Farawa 6:3 yana maganar ƙudurin Allah na kawar da lalatacen zamani a duniya. Jehobah ya yi ƙudurin yin hakan cikin shekaru 120, ko da yake Nuhu bai san da hakan ba tukuna. Amma me ya sa ya kafa iyakar wannan lokaci? Me ya sa za a jira?
Manzo Bitrus ya ba da dalilan: “Haƙurin Allah yana jinkiri a zamanin Nuhu, tun ana shirin jirgi, inda mutane kima, watau masu-rai takwas, suka tsira ta wurin ruwa.” (1 Bit. 3:20) Hakika, sa’ad da Allah ya tsai da shawara game da shekaru 120, da sauran abubuwa da za a yi. Bayan shekaru 20, Nuhu da matarsa suka soma haifan ’ya’ya. (Far. 5:32; 7:6) Yaransu maza uku suka yi girma kuma suka yi aure, hakan ya sa adadin waɗanda suke cikin iyalin ya kai “masu-rai takwas.” Za su kuma gina jirgin, wanda ba aikin da za a gama da sauri ba ne idan aka yi la’akari da girmansa da kuma girman iyalin Nuhu. Hakika, haƙurin da Allah ya yi na shekara 120 ya sa aka cim ma waɗannan abubuwa kuma ya sa ya yiwu a ceci rayuka, da ya sa mutane takwas masu aminci “suka tsira ta wurin ruwa.”
Littafi Mai Tsarki bai faɗa ainihin shekarar da Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa Rigyawar za ta faru ba. Da yake an haifi ’ya’yansa maza kuma sun yi girma kuma suka yi aure, wataƙila shekaru 40 ko 50 ne ya rage kafin Rigyawar. Sai Jehobah ya gaya wa Nuhu: “Matuƙar dukan abu mai-rai a gare mu ta yi.” Ya daɗa cewa Nuhu zai gina jirgi mai girma kuma ya shiga ciki da iyalinsa. (Far. 6:13-18) A shekaru da suka rage, Nuhu ya nuna misali mai kyau na adalci ta hanyar rayuwarsa. Ya zama “mai-shelan adalci” wanda ya sanar da saƙon kashedi da ya fita sarai, wato, ƙudurin Allah na halakar da waɗanda ba sa rayuwa da ta jitu da mizanan Allah a lokacin. Nuhu bai san tsawon shekarar da hakan zai faru ba, amma babu shakka ya san cewa halakar za ta zo. Kuma ka san cewa hakan ya faru.—2 Bit. 2:5.