An Ƙarfafa Mu Mu Sha Kan Kowane Gwaji
“Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.” —FILIB. 4:13.
1. Me ya sa mutanen Jehobah suke fuskantar matsaloli?
MUTANEN Jehobah ba baƙi ba ne ga matsaloli iri iri. Muna fuskantar wasu gwaje-gwaje don ajizancinmu ko kuma saboda wannan zamanin da muke ciki. Wasu kuma saboda magabtaka da ke tsakanin waɗanda suke bauta wa Allah da waɗanda ba sa bauta masa. (Far. 3:15) Tun farkon tarihin ’yan Adam, Allah ya taimaka wa bayinsa amintattu su jimre da tsanani na addini, su jimre da matsi na tsara marar kyau, kuma su jimre da kowanne irin matsaloli. Ruhunsa mai tsarki zai iya ƙarfafa mu mu yi hakan.
Ruhu Mai Tsarki Yana Taimaka Mana Mu Jimre da Tsanantawa na Addini
2. Mene ne manufar tsanantawa ta addini, kuma zai iya tahowa ta wacce hanya?
2 Tsanantawa na addini yana nufin a kawar da imani, a hana yaɗa su, ko kuma a sa mutane su rabu da abin da suka gaskata. Za a iya tsananta mana kai tsaye ko da dabara. Littafi Mai Tsarki ya kamanta farmakin Shaiɗan da na zaki da kuma maciji.—Karanta Zabura 91:13.
3. Waɗanne tsanantawa ne ke kamar na zaki da maciji?
3 Kamar mugun zaki, Shaiɗan ya daɗe yana kai wa mutanen Jehobah farmaki gaba da gaba ta nuna ƙarfi, saka su a kurkuku, ko hana aikinsu. (Zab. 94:20) Labaran Yearbook da ke bayyana ayyukan Shaidun Jehobah na zamani yana ɗauke da labarai da yawa na irin waɗannan farmakin. Taron ’yan iska, wasu da limamai ko ’yan siyasa suke ja-gorarsu, sun tsananta wa mutanen Allah a wurare da yawa. Wannan farmaki irin na zaki ya sa kalilan su daina bauta wa Jehobah. Kamar maciji, Iblis yana kuma kai wa mutane farmaki a ɓoye don ya gubatar da zukatarsu kuma ya rinjayi mutane su yi nufinsa. Yana kai irin wannan farmakin ne don ya raunana ko ya ɓata mu a ruhaniyance. Ta ruhu mai tsarki na Allah, za mu iya tsayayya wa irin waɗannan tsanantawa biyu.
4, 5. Mene ne hanya mafi kyau na shirya fuskantar tsanantawa, kuma me ya sa? Ka ba da misali.
4 Yin tunani game da ire-iren tsanantawa da za mu iya fuskanta a nan gaba ba hanya mafi kyau ba ne na yin shirin jimrewa da gwaji. Gaskiya ita ce ba za mu iya sanin tsanantawa da za mu fuskanta ba, saboda haka ba za mu cim ma abu mai yawa ba idan muna damuwa game da abin da wataƙila ba zai taɓa faruwa ba. Amma akwai abin da za mu iya yi. Yawancin waɗanda suka yi nasara wajen jimre da tsanantawa sun yi hakan ta yin bimbini a kan tafarkin amintattu masu nagarta kamar yadda aka rubuta a cikin Nassosi, koyarwa da kuma misalin Yesu. Hakan ya sa su zurfafa ƙaunarsu ga Jehobah. Ƙaunar nan kuma ta taimaka musu su jimre da kowanne gwaje-gwaje da suka fuskanta.
5 Ku yi la’akari da ’yan’uwanmu mata biyu a ƙasar Malawi. Taron ’yan iska da suke ƙoƙari su tilasta su su sayi katin siyasa sun yi musu duka, sun tsiraita su, kuma sun nemi su yi musu fyaɗe. Taron ’yan iskan sun yi musu ƙarya cewa ’yan’uwa da suke hidima a Bethel ma sun sayi katin siyasar. Mene ne ’yan’uwan mata suka ce? “Muna bauta wa Jehobah Allah kaɗai. Saboda haka idan ’yan’uwan da ke ofishin reshe sun sayi katin, hakan bai shafe mu ba. Ba za mu ja da baya ba, ko idan kun kashe mu!” Bayan sun ɗauki wannan mataki na gaba gaɗi, sai aka sako su.
6, 7. Ta yaya Jehobah yake ƙarfafa bayinsa su jimre da tsanantawa?
6 Manzo Bulus ya lura cewa Kiristoci a Tasalonika sun karɓi saƙon gaskiya “cikin ƙunci mai-yawa, tare da farin zuciya na Ruhu Mai-tsarki.” (1 Tas. 1:6) Hakika, Kiristoci da yawa, a dā da kuma yanzu, waɗanda suka fuskanci da kuma jimre da tsanantawa sun faɗa cewa sa’ad da gwaje-gwajensu ya yi tsanani sosai, sun samu salama na zuci, wadda sashe ɗaya ne na ’yar ruhu mai tsarki na Allah. (Gal. 5:22) Wannan salamar kuma ta taimaka musu su kiyaye zuciyarsu da kuma hankalinsu. Hakika, Jehobah yana amfani da ƙarfin ikonsa don ƙarfafa bayinsa su jimre da gwaje-gwaje kuma su aikata da hikima sa’ad da suke fuskantar matsala.a
7 Mutane da suke kallonmu sun yi mamaki game da tsayin daka da mutanen Allah suka yi a nagartarsu duk da tsanantawa. Shaidu suna cike da ikon Allah. Manzo Bitrus ya tabbatar mana: “Idan kuna shan zargi sabili da sunan Kristi masu-albarka ne ku; domin Ruhu na daraja da Ruhu na Allah yana zaune a kanku.” (1 Bit. 4:14) Da yake ana tsananta mana saboda muna ɗaukaka mizanai na adalci ya nuna cewa muna da goyon bayan Allah. (Mat. 5:10-12; Yoh. 15:20) Wannan albarkar Jehobah tana kawo farin ciki!
An Taimaka Mana Mu Yi Tsayayya da Matsi na Tsara
8. (a) Mene ne ya taimaka wa Joshua da Kaleb su yi tsayayya da matsi na tsara? (b) Mene ne za mu iya koya daga misalin Joshua da Kaleb?
8 Hamayya mafi rinjaya da Kiristoci suke jimrewa, ita ce matsi na tsara marar kyau. Amma dai, domin ruhun Jehobah ya fi ruhun duniya ƙarfi, za mu iya guje wa mutane masu mana ba’a, suna yaɗa ƙarya game da mu, ko kuma suke tilasta mana mu bi nasu mizanai. Alal misali, mene ne ya taimaki Joshua da Kaleb su ƙi yarda da ra’ayoyin sauran masu leƙen asiri goma da aka aika zuwa ƙasar Ka’anan? Ruhu mai tsarki ne ya motsa su su kasance da ‘ra’ayi’ dabam.—Karanta Littafin Lissafi 13:30; 14:6-10, 24.
9. Me ya sa wajibi ne Kiristoci su aikata dabam da sauran mutane?
9 Ruhu mai tsarki ya kuma ƙarfafa almajiran Yesu su yi biyayya ga Allah maimakon mutanen da ake ɗaukaka a matsayin malamai na addinin gaskiya. (A. M. 4:21, 31; 5:29, 32) Yawancin mutane sun gwammace su yi abubuwan da mutane da yawa suke yi, don su guji wahala. Sau da yawa, Kiristoci na gaskiya, suna tsai da shawara game da abin da suka san cewa yana da kyau. Duk da haka, muna godiya ga ƙarfin da ruhun Allah yake ba su, ba sa jin tsoron kasancewa dabam. (2 Tim. 1:7) Ka yi la’akari da sashe ɗaya da wajibi ne mu ƙi faɗa wa matsi na tsara.
10. Wacce matsala ce wasu Kiristoci za su iya fuskanta?
10 Wasu matasa za su iya fuskantar matsala idan sun san cewa abokinsu ya yi abu marar kyau. Suna iya jin cewa za su ci amanar abokinsu idan sun tona abu marar kyau da ya yi, saboda haka, sun ƙi yin magana a kan batun domin wai suna son su kasance da aminci. Mai zunubi zai iya matsa wa abokansa cewa kada ya faɗa wa kowa abin da ya yi. Ko da yake ba matasa kaɗai ba ne suke fuskantar irin wannan matsala. Yana iya wa wasu manya ma wuya su faɗa wa dattawan ikilisiya game da abu marar kyau da abokinsu ko wani a iyalinsu ya yi. Amma yaya ya kamata Kiristoci na gaskiya su aikata game da irin wannan matsin?
11, 12. Wane amsa mafi kyau ne ya kamata ka ba wa ɗan’uwa a cikin ikilisiya da ya ce kada ka tona zunubinsa, kuma me ya sa?
11 Ka yi la’akari da wannan yanayin. A ce wani ɗan’uwa matashi mai suna Alex ya samu labari cewa abokinsa a cikin ikilisiya mai suna Steve, ya saba kallon hotunan batsa. Alex ya gaya wa Steve cewa ya damu ƙwarai game da abin da yake yi. Amma dai, Steve bai damu da abin ya ce ba. Da Alex ya ce wa abokinsa ya gaya wa dattawa game da abin da ya faru, Steve ya ce masa idan lallai shi abokinsa ne, ba zai gaya wa kowa abin da ya faru ba. Shin ya kamata Alex ya ji tsoro cewa za su daina abuta da juna? Zai iya tunani ko dattawa za su amince da abin da ya ce idan Steve ya musanci kome. Duk da haka, yanayin ba zai kyautu ba idan Alex ya yi shuru. Hakika, zai iya sa Steve ya rasa dangantakarsa da Jehobah. Zai dace Alex ya tuna cewa “tsoron mutum ya kan kawo tarko, amma wanda ya sa danganarsa ga Ubangiji za ya zauna lafiya.” (Mis. 29:25) Mene ne kuma Alex zai iya yi? Zai iya sake zuwa wurin Steve cikin ƙauna ya faɗa masa laifin da ya yi. Hakan zai bukaci yin gaba gaɗi. A wannan lokacin, zai iya zama cewa Steve zai so su tattauna game da matsalar. Alex ya sake ƙarfafa shi ya tattauna batun da dattawa kuma ya gaya masa cewa idan bai yi hakan ba bayan ’yan kwanaki, shi da kansa zai kai ƙaransa.—Lev. 5:1.
12 Idan hakan ya taɓa faruwa da kai, wataƙila abokinka bai ji daɗin ƙoƙarce-ƙoƙarcen da kake yi don ka taimaka masa ba. Amma daga baya zai iya sanin cewa ƙaunar da kake masa ne ya sa ka aikata hakan. Idan wanda ya yi laifin ya amince da taimakon, zai ci gaba da nuna godiya don gaba gaɗi da kuma amincinka. A wani ɓangare kuma, idan ya ci gaba da yin fushi da kai don ka kai ƙaransa, kana zato shi aboki nagari ne kuwa? Faranta ran Abokinmu mafi girma, Jehobah a koyaushe shi ne abu mafi kyau. Idan mun sa shi farko, waɗanda suke ƙaunarsa za su daraja mu don amincinmu kuma za su zama abokanmu na gaske. Kada mu taɓa ba Iblis dama a cikin ikilisiyar Kirista. Idan mun yi hakan, za mu ɓata wa ruhu mai tsarki na Jehobah rai. Za mu aikata bisa wannan, ta wurin yin ƙoƙari don mu tsabtace ikilisiyar Kirista.—Afis. 4:27, 30.
An Ƙarfafa Mu Mu Jimre da Matsaloli Iri-Iri
13. Waɗanne irin matsaloli ne mutanen Jehobah suke fuskanta, kuma me ya sa waɗannan abubuwan gama gari ne?
13 Za a iya samun matsaloli iri-iri, kamar noƙewar tattalin arziki, rashin aiki, bala’i, mutuwar ƙaunatacce, rashin lafiya, da sauransu. Tun da muna rayuwa a “miyagun zamanu” ya kamata mu yi tsammani cewa ko badaɗe ko bajima dukan mu za mu fuskanci gwaji iri-iri. (2 Tim. 3:1) Idan hakan ya faru, bai kamata mu yi rawan jiki ba. Ruhu mai tsarki zai iya ƙarfafa mu mu jimre da kowanne irin matsala.
14. Mene ne ya ƙarfafa Ayuba ya jimre da matsalolinsa?
14 Ayuba ya sha wahala ɗaya bayan ɗaya. Ya rasa dabbobinsa da yaransa da abokansa da lafiyarsa kuma matarsa ta rasa dogararta ga Jehobah. (Ayu. 1:13-19; 2:7-9) Duk da haka, Elihu ya ƙarfafa Ayuba sosai. Saƙonsa da kuma ainihin abin da Jehobah ya ce wa Ayuba shi ne: “Tsaya kurum, ka tuna da ayyukan Allah masu-ban al’ajabi.” (Ayu. 37:14) Mene ne ya taimaki Ayuba ya jimre da gwaje-gwajensa? Kuma mene ne zai iya taimaka mana mu jimre da namu? Tunawa da kuma yin tunani a kan hanyoyi dabam dabam da ruhu mai tsarki da kuma ikon Jehobah yake aiki. (Ayu. 38:1-41; 42:1, 2) Wataƙila za mu iya tunawa da lokatai a rayuwarmu da muka ga alamar cewa Allah yana ƙaunarmu ɗaɗɗaya. Har ila, yana ƙaunarmu.
15. Mene ne ya ƙarfafa manzo Bulus ya jimre matsaloli?
15 Imanin manzo Bulus ne ya sa ya jimre da matsaloli da suka kusan sa ya rasa ransa. (2 Kor. 11:23-28) Ta yaya ya kasance da daidaita da kwanciyar rai a waɗannan yanayi masu cike da matsaloli? Ta dogara ga Jehobah cikin addu’a. A lokacin gwajin da ya sa a ƙarshe aka kashe shi, Bulus ya rubuta: “Amma Ubangiji ya tsaya wurina, ya kuwa ƙarfafa ni; domin ta wurina shela ta watsu sarai, dukan Al’ummai kuma su ji: aka cece ni kuma daga bakin zaki.” (2 Tim. 4:17) Saboda haka, daga abubuwan da Bulus ya fuskanta, ya tabbatar wa ’yan’uwansa cewa babu amfanin ‘yin alhini cikin kowane abu.’—Karanta Filibiyawa 4:6, 7, 13.
16, 17. Ka ba da misali da ya nuna yadda Jehobah yake ƙarfafa mutanensa su jimre da matsaloli a yau.
16 Wata majagaba mai suna Roxana wata ce da ta ga yadda Jehobah yake wa mutanensa tanadi. Sa’ad da ta nemi izini daga wurin shugaban aikinta don ta halarci taron gunduma, ya faɗa da fushi cewa idan ta je, zai kore ta daga aiki. Roxana ta tafi, kuma ta yi addu’a cewa Allah ya taimaka mata kada ta rasa aikinta. Bayan hakan, hankalinta ya kwanta. Kuma daidai yadda ya faɗa, a ranar Litinin bayan taron gundumar, ya kore ta daga aiki. Roxana ta damu sosai. Ta so aikin don ta tallafa wa iyalinta da shi, ko da yake ba a biyanta kuɗi mai yawa. Sai ta sake yin addu’a, kuma ta yi tunani cewa Allah ya yi mata tanadi na ruhaniya a wurin taron gundumar, don hakan babu shakka zai yi mata tanadi na zahiri. Yayin da take tafiya gida, Roxana ta ga wata alama da aka sa “Ana Neman Masu Aiki” da suka ƙware a aikin ɗinki, sai ta saka takardar neman aiki. Manaja ɗin ya san cewa ba ta ƙware ba amma ya karɓe ta, kuma yana biyanta albashin da ya kusan ninka na wancan wurin aikin. Roxana ta ji cewa an amsa addu’arta. Albarka mafi muhimmanci shi ne cewa ta samu tattauna bishara da abokan aikinta da yawa. Mutane biyar cikinsu har da manajan suka karɓi gaskiya kuma suka yi baftisma.
17 A wasu lokatai, za mu iya ga kamar ba a amsa addu’o’inmu ba, wataƙila ba nan da nan ba ko yadda muke zato. Idan haka ne, akwai dalili mai kyau da ya sa hakan ya faru. Jehobah ya san da hakan, amma wataƙila za mu ankara hakan a nan gaba. Abu ɗaya da muka tabbata da shi ne cewa, Allah ba ya yin watsi da bayinsa amintattu.—Ibran. 6:10.
An Taimaka Mana Mu Sha Kan Gwaji da Jarrabobi
18, 19. (a) Me ya sa za mu sa rai cewa za mu fuskanci gwaje-gwaje da jarrabobi? (b) Ta yaya za ka iya yin nasara wajen jimre da gwaje-gwaje?
18 Mutanen Jehobah ba sa mamakin fuskantar jarraba da sanyin gwiwa da tsanantawa da kuma matsi na tsara. Duniya ba ta sonmu ko kaɗan. (Yoh. 15:17-19) Duk da haka, ruhu mai tsarki zai iya sa mu jimre da kowanne ƙalubale da za mu iya fuskanta a hidimarmu ga Allah. Jehobah ba zai ƙyale a jarraba mu fiye da yadda za mu iya jimrewa ba. (1 Kor. 10:13) Ba zai taɓa barinmu ko kuma ya yashe mu ba. (Ibran. 13:5) Yin biyayya ga hurarriyar Kalmar Allah tana kāre mu kuma yana ƙarfafa mu. Bugu da ƙari, ruhu mai tsarki na Allah zai iya motsa ’yan’uwanmu su taimaka mana sa’ad da muke da bukata.
19 Bari dukanmu mu ci gaba da neman ruhu mai tsarki ta wurin addu’a da nazarin Nassosi. Bari mu ci gaba da zama “ƙarfafaffu da dukan iko, bisa ga ikon ɗaukakar [Allah], zuwa dukan haƙuri da jimrewa tare da farinciki.”—Kol. 1:11.
[Hasiya]
a Don ganin misalai, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu 2001 shafi na 28; da Awake! na 8 ga Fabrairu, shafuffuka na 21 da 22.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za ka shirya jimre da tsanantawa?
• Ya yaya ya kamata ka aikata idan wani ya ce kada ka tona zunubin da ya yi?
• Wane tabbaci ne za ka iya samu sa’ad da kake fuskantar matsaloli?
[Hoton da ke shafi na 28]
Mene ne za mu iya koya daga Joshua da Kaleb?
[Hoton da ke shafi na 29]
Ta yaya za ka iya taimaki aboki da ya yi wani zunubi?