Tambayoyi Daga Masu Karatu
Me ya sa Musa ya yi fushi da ’ya’yan Haruna Eleazar da Ithamar bayan mutuwar ’yan’uwansu Nadab da Abihu, kuma me aka yi don fushin ya huce?—Lev. 10:16-20.
Ba da daɗewa ba bayan da aka naɗa firistoci don su riƙa hidima a mazauni, Jehobah ya halaka ’ya’yan Haruna Nadab da Abihu domin sun miƙa haramtacciyar wuta a gabansa. (Lev. 10:1, 2) Musa ya umurci ’ya’yan Haruna da suka tsira kada su yi wa ’yan’uwansu da suka rasu makoki. Ba da daɗewa ba bayan hakan, Musa ya yi fushi da Eleazar da Ithamar domin ba su ci bunsurun hadayar zunubi ba. (Lev. 9:3) Me ya sa Musa ya aikata hakan?
Dokokin da Jehobah ya ba Musa sun faɗi cewa firist da ya miƙa hadayar zunubi zai ci wasu cikin hadayar a cikin farfajiya na tantin taro. Ana ɗaukan yin hakan a matsayin ɗaukan nauyin zunuban waɗanda suka miƙa hadayan. Amma, idan aka kai wasu cikin jinin hadayar zuwa Wuri Mai Tsarki, wato, ɗaki na farko na wuri mai-tsarkin, ba za a ci hadayar ba. Maimakon haka, za a ƙone ta.—Lev. 6:24-26, 30.
Kamar dai bayan mummunar aukuwa na ranar, Musa ya ga bukatar tabbata cewa an bi dukan dokokin Jehobah. Da ya fahimci cewa an ƙone bunsurun hadaya na zunubi, ya tambayi Eleazar da Ithamar da fushi dalilin da ya sa ba su ci ba kamar yadda aka umurce su, domin ba a miƙa jininsa a gaban Jehobah a Wuri Mai Tsarki ba.—Lev. 10:17, 18.
Haruna ya amsa tambayar Musa, tun da yake firistoci da suka tsira sun yi hakan ne da amincewarsa. Game da rasuwar ’ya’yansa maza biyu, Haruna zai iya yin mamaki ko akwai wani cikin firistoci da zai kasance da lamiri mai kyau ya ci hadayar zunubi a wannan ranar. Wataƙila yana ganin cewa idan suka ci hadayar ba za su faranta wa Jehobah rai ba, ko da yake ba su da alhakin zunubin da Nadab da Abihu suka yi.—Lev. 10:19.
Wataƙila Haruna ya yi tunani cewa a wannan ranar da waɗanda suke cikin iyalinsa suka fara yin ayyukansu na firist, ya kamata su mai da hankali sosai don su faranta wa Allah rai ko ma a ƙaramin abu. Amma dai, Nadab da Abihu sun ɓata sunan Jehobah, kuma Allah ya yi fushi da su sosai. Wataƙila Haruna ya yi tunanin cewa bai kamata iyalin da zunubin ya shafa su ci daga cikin hadaya mai tsarkin ba.
Kamar dai Musa ya amince da amsar ɗan’uwansa, gama ayar ta kammala: “Sa’anda Musa ya ji wannan ya gamshe shi.” (Lev. 10:20) Babu shakka, Jehobah ma ya gamsu da amsar da Haruna ya bayar.