Kana Nuna Godiya ga Dukan Albarka da Ka Samu Kuwa?
DA YAKE an ’yantar da su ta mu’ujiza daga bauta a ƙasar Masar, Isra’ilawa a dā sun yi farin cikin samun ’yanci don su bauta wa Jehobah. (Fit. 14:29–15:1, 20, 21) Amma, ba da daɗewa ba ra’ayinsu ya canja. Suka fara gunaguni game da yanayinsu. Me ya sa? Domin sun soma yin tunani game da matsalolin da ke tattare da zama a jeji fiye da abin da Jehobah ya yi musu. Sun gaya wa Musa: “Don me kuka fito da mu daga Masar mu mutu a cikin jeji? gama babu abinci, babu ruwa, ranmu ya gundura da wannan mummunan abinci [manna].”—Lit. Lis. 21:5.
Ƙarnuka da yawa bayan hakan, Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya rera waƙa: “Amma na dogara ga jinƙanka; Zuciyata za ta yi murna cikin cetonka: Zan raira waƙa ga Ubangiji, Gama ya kyauta mani.” (Zab. 13:5, 6) Dauda bai manta da ayyukan alheri da ƙauna ta motsa Jehobah ya yi a gare shi ba. Akasin haka, yana keɓe lokaci a kai a kai don ya yi tunani game da su. (Zab. 103:2) Jehobah ya kyautata mana ma, kuma yana da kyau kada mu yi wasa da abin da ya yi a madadinmu. Saboda haka, bari mu bincika wasu albarka da Allah ya yi mana da muke morewa a yau.
‘Dangantaka da Ubangiji’
Marubucin wannan zabura ya rera waƙa: “Asirin Ubangiji ga masu-tsoronsa ya ke.” (Zab. 25:14) Gata ce sosai ’yan Adam ajizai su kasance da dangantaka na kud da kud da Jehobah! Amma, idan mun shagala a ayyukan rayuwa na yau da kullum kuma mun kasa samun isashen lokaci don yin addu’a kuma fa? Ka yi tunanin abin da zai faru da dangantakarmu mai kyau da Jehobah. A matsayin abokinmu, Jehobah yana son mu dogara a gare shi kuma mu gaya masa dukan abin da ke damunmu a cikin addu’a, mu gaya masa tsoron da muke ji da sha’awoyinmu da kuma alhininmu. (Mis. 3:5, 6; Filib. 4:6, 7) Saboda haka, ya kamata mu yi la’akari da ingancin addu’o’inmu.
Sa’ad da wani Mashaidi matashi mai suna Paul ya yi tunani game da addu’o’insa, ya fahimci cewa yana bukata ya kyautata addu’o’insa.a Ya ce, “Na saba yin amfani da kalamai iri ɗaya a kai a kai sa’ad da nake yin addu’a ga Jehobah.” Yayin da Paul ya yi bincike a kan batun a cikin Watch Tower Publications Index, ya ga cewa da akwai misalan addu’o’i 180 da suke a rubuce cikin Littafi Mai Tsarki. Bayin Jehobah a dā sun furta yadda suke ji. Paul ya ce: “Ta wurin yin bimbini a kan irin waɗannan misalai na Nassi, na koya na faɗa abubuwa takamammu sa’ad da nake addu’a. Hakan ya taimaka mini na gaya wa Jehobah abin da ke zuciyata. Yanzu ina farin cikin kusantarsa a cikin addu’a.”
‘Abinci a Lotonsa’
Wata albarka da Jehobah ya yi mana ita ce gaskiyar da muka koya daga cikin Nassosi. Yayin da muke cin abinci na ruhaniya a yalwace, muna da dalilin “rairawa domin murna a zuci.” (Isha. 65:13, 14) Amma, dole ne mu mai da hankali don kada mu ƙyale tasiri marar kyau su sa mu yi rashin himma don gaskiya. Alal misali, saurarar ra’ayi da ’yan ridda suke yaɗawa zai iya shafan tunaninmu kuma ya sa ba za mu ga amfanin abinci na ruhaniya “a lotonsa” da Jehobah yake tanadinsa ta “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ba.—Mat. 24:45-47.
André, wanda ya daɗe yana bauta wa Jehobah, ya shaida mugun sakamako don ya ƙyale ra’ayin ’yan ridda ya yaudare shi. Yana ganin cewa kallon Yanar gizo ta ’yan ridda na ɗan lokaci ba zai kasance da lahani ba. Ya tuna: “Da farko, koyarwar ’yan ridda ta jawo hankalina. Yayin da nake ƙara bincika abin da suka ce, ina ƙara ganin cewa ina da ƙwaƙƙwarar dalili na barin ƙungiyar Jehobah. Amma daga baya, sa’ad da na yi wasu bincike a kan gardama da ’yan ridda suke yi game da Shaidun Jehobah, sai na fahimci cewa waɗannan malaman ƙarya masu makirci ne. Bayanai daga littattafanmu da suka jujjuya ne suke kiran ‘ƙwaƙƙwarar tabbaci’ da suke da shi. Saboda haka, na tsai da shawara na soma karanta littattafanmu da kuma halartar tarurruka. Ba da daɗewa ba, na fahimci cewa akwai abubuwa da yawa da ban sani ba.” Abin farin ciki, André ya dawo cikin ikilisiya.
“’Yan’uwanci”
’Yan’uwanmu masu ƙauna da haɗin kai a dukan duniya albarka ne daga Jehobah. (Zab. 133:1) Da dalili mai kyau, manzo Bitrus ya rubuta: “Ku ƙaunaci ’yan’uwanci.” (1 Bit. 2:17) Da yake muna cikin ’yan’uwancin Kirista, muna amfana daga alheri da tallafawar waɗanda suke kama da ubanni da gyatumai da ’yan’uwa maza da mata a cikin gaskiya.—Mar. 10:29, 30.
Duk da haka, yanayi dabam dabam a wani lokaci yakan kawo matsala a dangantakarmu da ’yan’uwanmu maza da mata. Alal misali, yana da sauƙi mu yi fushi don ajizancin wani kuma mu soma kushe wa wannan. Idan hakan ya faru, zai fi kyau mu tuna cewa Jehobah yana ƙaunar bayinsa duk da ajizancinsu. Bugu da ƙari, “Idan mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu mu ke yi, gaskiya kuwa ba ta cikinmu ba.” (1 Yoh. 1:8) Ya kamata mu yi ƙoƙari mu riƙa ‘haƙuri da juna muna gafarta ma juna.’—Kol. 3:13.
Wata matashiya mai suna Ann ta koyi amfanin yin cuɗanya da ’yan’uwa Kiristoci don matsalolin da ta fuskanta a rayuwa. Ta aikata kamar ɗa mubazzari na kwatancin Yesu, kuma ta bijire daga ikilisiyar Kirista. Daga baya, ta dawo cikin hankalinta kuma ta dawo cikin gaskiya. (Luk 15:11-24) Mene ne Ann ta koya daga wannan? Ta ce: “Yanzu da na dawo ƙungiyar Jehobah, ina daraja dukan ’yan’uwana maza da mata duk da ajizancinsu. A dā ina saurin kushe musu. Amma na ƙuduri aniya ba zan ƙyale kome ya hana ni albarka da nake morewa tsakanin ’yan’uwa masu bi ba. Babu kome a cikin duniya da ya cancanci ya sa mu yasar da aljannarmu ta ruhaniya.”
Ka Ci Gaba da Nuna Godiya don Albarkarka
Begenmu cewa Mulkin Allah ne zai magance dukan matsalolin ’yan Adam dukiya ce da ba za a iya kwatanta da kome ba. Sa’ad da muka samu wannan begen da farko, mun yi farin ciki sosai! Mun ji kamar attajiri da ke cikin almarar Yesu wanda ya “sayarda dukan abin da ya ke da shi” domin ya sayi ‘lu’u-lu’u ɗaya mai tamani da yawa.’ (Mat. 13:45, 46) Yesu bai faɗa cewa attajirin ya taɓa daina ɗaukan lu’u-lu’un da tamani ba. Haka nan ma, kada mu daina nuna godiya don begenmu mai ban al’ajabi.—1 Tas. 5:8; Ibran. 6:19.
Ka yi la’akari da Jean, wadda take bauta wa Jehobah fiye da shekaru 60. Ta ce: “Abin da ya taimaka mini na ci gaba da sa Mulkin Allah a zuciyata shi ne gaya wa mutane game da shi. Sa’ad da na ga yadda suka aikata yayin da suka fahimci abin da Mulkin zai yi, hakan yana kawo mini tasiri mai kyau. Ganin yadda gaskiyar Mulkin take sa ɗaliban da nake nazarin Littafi Mai Tsarki da su su canja rayuwarsu yana sa na yi tunani, ‘Gaskiyar da nake koya wa mutane mai ban al’ajabi ce!’”
Muna da ƙwaƙƙwarar dalili na nuna godiya ga albarka na ruhaniya masu yawa da muke morewa. Ko da yake muna fuskantar gwaje-gwaje irin su hamayya da rashin lafiya da tsufa da baƙin ciki da rashin waɗanda muke ƙauna da kuma shan wahalar tattalin arziki, mun san cewa na ɗan lokaci ne kawai. A cikin Mulkin Allah, za mu sami ƙarin albarka a kan waɗanda muke da su a zahiri. A sabuwar duniya, za a kawo ƙarshen duk wata wahala da muke sha a yanzu.—R. Yoh. 21:4.
A yanzu, bari mu riƙa nuna godiya ga albarkarmu ta ruhaniya kuma mu nuna irin godiyar da marubucin wannan zaburar ya rera: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka; ko da ni ke so in bayyana su in bada labarinsu, sun fi gaban lissafi.”—Zab. 40:5.
[Hasiya]
a An canja sunayen.
[Hoton da ke shafi na 18]
An albarkace mu da tallafawa na ruhaniya a lokacin da muke fuskantar gwaji