Mene Ne Mulkin Allah?
“Wannan bishara kuwa ta mulki . . . ”—MATTA 24:14.
A SANANNEN Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya yi addu’ar misali, wadda ta haɗa da wannan roƙon ga Allah: “Mulkinka shi zo.” Miliyoyin mutane sun haddace wannan addu’ar kuma sun maimaita ta sau da yawa. In ji wani kundin sani, “wannan ita ce addu’ar da dukan Kiristoci suke yawan amfani da ita a bautarsu ta yau da kullum.” Amma, mutane da yawa da suke maimaita ta ba su san ma’anar Mulkin ba ko kuma abin da zai yi idan ya zo.—Matta 6:9, 10.
Wannan ba abin mamaki ba ne. Shugabannin Kiristendom suna gabatar da bayanan da suka saɓa wa juna game da ma’anar Mulkin, kuma waɗannan bayanan suna rikitar da mutane. Wani ya rubuta cewa Mulkin Allah “wani abin al’ajabi ne daga sama, . . . dangantakar da mutum yake da ita da Allah mai rai . . . , wato, dangantaka da Allah wadda ta hanyarta ce maza da mata suke samun ceto.” Wani ya bayyana ma’anar bisharar Mulkin a matsayin “umurni game da coci.” Kuma littafin nan The Catholic Encyclopedia ya ce: “Mulkin Allah yana nufin . . . sarautar Allah a zukatanmu.”
Za ka samu cikakken bayani a shafi na 2 na wannan mujallar. Ya ce: “Mulkin Allah, wanda gwamnati ce ta gaske a samaniya, ba da daɗewa ba za ta kawo ƙarshen dukan mugunta kuma ta mai da duniya ta zama aljanna.” Bari mu ga yadda Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan wannan fahimin.
Waɗanda Za Su Yi Mulki Bisa Dukan Duniya a Nan Gaba
Mulki, gwamnati ce da take da sarki. Sarkin Mulkin Allah shi ne Yesu Kristi wanda aka ta da daga matattu. An kwatanta wa annabi Daniyel a cikin wahayi yadda aka naɗa shi a sama, kuma ya rubuta: “A cikin ru’yai na dare na gani, ga shi, tare da gizagizan sama wani ya zo mai-kama da ɗan mutum [Yesu]; ya zo kuma har wurin mai-zamanin dā [Jehobah Allah], aka kawo shi a gabansa har ya yi kusa. Aka ba shi sarauta da daraja, da mulki, domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa; sarautarsa madawwamiya ce, wanda ba za ta shuɗe ba, mulkinsa kuma wanda ba shi hallakuwa.”—Daniyel 7:13, 14.
Littafin Daniyel ya nuna cewa Allah ne zai kafa Mulkin da zai kawo ƙarshen dukan gwamnatocin ’yan Adam, kuma ba za a rushe shi ba har abada. Sura ta 2 ta kwatanta wani hurarren mafarki da sarkin Babila ya yi, inda ya ga babban gunki, wanda yake wakiltar ƙasashen duniya masu iko bi da bi. Annabi Daniyel ya bayyana ma’anar mafarkin. Ya rubuta cewa a “kwanaki na ƙarshe, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar wa wata al’umma ba; amma za ya parpashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniyel 2:28, 44.
Sarkin Mulkin Allah ba zai yi sarauta shi kaɗai ba. A lokacin hidimarsa a duniya, Yesu ya tabbatar wa manzanninsa masu aminci cewa za a ta da su, tare da wasu mutane, zuwa sama kuma za su zauna bisa kursiyai. (Luka 22:28-30) Yesu ba ya nufin kursiyai na zahiri, amma kamar yadda ya ce, Mulkin zai kasance ne a sama. Littafi Mai Tsarki ya ce waɗannan abokan sarautar sun fito ne “daga cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma iri-iri.” Za su zama “mulki da firistoci ga Allahnmu; suna kuwa mulki bisa duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.
Dalilin da ya Sa Bisharar Mulkin Take da Kyau
Za ka lura cewa an ba Kristi Yesu sarauta bisa dukan “mutane daga cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, iri-iri” kuma waɗanda suke tare da shi za su yi “mulki bisa duniya.” Su wane ne za su zama talakawan wannan Mulkin? Waɗanda suka yi biyayya ga bisharar da ake yin wa’azinta a yau. Talakawan sun haɗa da waɗanda za a ta da daga matattu a duniya, waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada.
Da babbar murya, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta albarkar da mutane za su more a ƙarƙashin Mulkin. Ga kaɗan daga cikinsu:
“Ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya; Ya karya baka, ya daddatse māshi; Ya ƙoƙone karusai cikin wuta.”—Zabura 46:9.
“Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba.”—Ishaya 65:21, 22.
“[Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
“Sa’annan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe. Sa’annan gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa, harshen bebe kuma za ya rera waƙa.”—Ishaya 35:5, 6.
“Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma: waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai”—Yohanna 5:28, 29.
“Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:11.
Hakika, wannan bishara ce mai daɗi! Ƙari ga haka, annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika sun nuna cewa lokaci ya kusa da Mulkin zai kafa sarautarsa ta adalci bisa dukan duniya.