Akwai Bishara Da Dukan Mutane Suke Bukata
“Bishara . . . ikon Allah ce zuwa ceto.”—ROM. 1:16.
1, 2. Me ya sa kake yin wa’azin “bishara ta mulki,” kuma waɗanne fannoninta ne kake nanatawa?
‘I NA farin cikin yin wa’azin bishara kowacce rana.’ Wataƙila ka taɓa yin irin wannan tunani ko kuma furuci. A matsayinka na Mashaidin Jehobah mai ƙwazo, ka san muhimmancin yin wa’azin “wannan bishara kuwa ta mulki.” Wataƙila za ka iya maimaita annabcin Yesu cewa mu yi hakan.—Mat. 24:14.
2 Sa’ad da kake yin wa’azin “bishara ta mulki,” kana ci gaba ne da aikin da Yesu ya soma. (Karanta Luka 4:43.) Babu shakka, ɗaya daga cikin abubuwan da ka fi nanatawa shi ne cewa ba da daɗewa ba Allah zai saka hannu a harkokin ’yan Adam. Ta hanyar “ƙunci mai-girma,” zai kawo ƙarshen addinin ƙarya kuma zai cire dukan mugunta daga duniya. (Mat. 24:21) Wataƙila kana nanata kuma cewa Mulkin Allah zai mai da duniya Aljanna don a yi yalwar salama da kuma farin ciki. Hakika, “bishara ta mulki” sashe ce ta “bishara [da aka sanar] ga Ibrahim tun dā, cewa, a cikinka dukan al’ummai za su sami albarka.”—Gal. 3:8.
3. Me ya sa za mu iya ce manzo Bulus ya nanata bisharar a littafin Romawa?
3 Shin zai iya yiwu cewa ba ma mai da hankali sosai ga sashen bisharar da mutane suke bukata? A wasiƙarsa ga Romawa manzo Bulus ya yi amfani da kalmar a asalin Helenanci “mulkin,” sau ɗaya kawai, amma ya yi amfani da furucin nan “bishara” sau goma sha biyu. (Karanta Romawa 14:17.) Wane fannin bisharar ne Bulus ya nanata sau da yawa a cikin littafin nan? Me ya sa wannan bisharar take da muhimmanci? Kuma me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga “bisharar Allah” sa’ad da muke yi wa mutane da ke yankinmu wa’azi?—Mar. 1:14; Rom. 15:16; 1 Tas. 2:2.
Abin da Waɗanda Suke Roma Suke Bukata
4. Bulus ya yi wa’azi game da mene ne sa’ad da yake fursuna a ƙasar Roma?
4 Yana da muhimmanci mu mai da hankali ga batutuwan da Bulus ya yi magana a kai sa’ad da yake cikin fursuna a ƙasar Roma. Mun karanta cewa sa’ad da Yahudawa da yawa suka ziyarce shi, ya ‘ba da shaida sosai game da (1) mulkin Allah kuma ya yi musu magana da rinjaya game da (2) Yesu.’ Da wanne sakamako? “Waɗansu suka gaskata abin da aka faɗi, waɗansu ba su gaskata ba.” Bayan hakan, Bulus ‘yana maraba da duk waɗanda suka je wurinsa, yana yi musu wa’azi game da (1) mulkin Allah kuma yana koyar da al’amuran (2) Ubangiji Yesu Kristi.’ (A. M. 28:17, 23-31) A bayyane yake cewa Bulus ya mai da hankali ga Mulkin Allah. Amma mene ne ya kuma nanata? Ya nanata wani abin da yake da muhimmanci ga Mulkin, wato, matsayin Yesu a nufin Allah.
5. Wace bukata ta musamman ce Bulus ya nanata a littafin Romawa?
5 Dukan mutane suna bukatar su san game da Yesu kuma su yi imani gare shi. Bulus ya yi magana game da wannan batun a littafin Romawa. Da farko ya rubuta game da ‘Allah, wanda nake bautarsa cikin ruhuna cikin bisharar Ɗansa.’ Ya daɗa: “Bishara ba abin kunya ba ce a gareni: gama ikon Allah ce zuwa ceto ga kowane mai-bada gaskiya.” Daga baya ya yi magana game da lokacin da “Allah za ya shara’anta asiran mutane, bisa ga bisharata, ta wurin Yesu Kristi.” Kuma ya ce: ‘Har na yi wa’azin bisharar Kristi sarai tun daga Urushalima, da kewayenta har zuwa Ilirikun.’a (Rom. 1:9, 16; 2:16; 15:19) Me kake tsammani ya sa Bulus ya nanata Yesu Kristi ga Romawa?
6, 7. Mene ne za mu iya cewa game da waɗanda suke cikin ikilisiyar Roma da kuma yadda ta soma?
6 Ba mu san yadda ikilisiyar Roma ta soma ba. Shin Yahudawa ko shigaggu da suka kasance a wurin a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z. sun zama Kiristoci ne sa’ad da suka koma ƙasar Roma? (A. M. 2:10) Ko kuwa Kiristoci attajirai da masu tafiye-tafiye ne suka yaɗa gaskiya a ƙasar Roma? Ko yaya ya faru, an riga an ƙafa ikilisiyar da daɗewa kafin Bulus ya rubuta littafin a misalin shekara ta 56 A.Z. (Rom. 1:8) Daga ina ne mutanen da suke cikin ikilisiyar suka fito?
7 Wasu cikinsu Yahudawa ne. Bulus ya gai da Andarunikus da Yuniyus a matsayin “dangina,” wataƙila yana nufin danginsa da Yahudawa ne. Akila wanda yake yin tanti a ƙasar Roma da matarsa Biriskilla ma Yahudawa ne. (Rom. 4:1; 9:3, 4; 16:3, 7; A. M. 18:2) Amma wataƙila ’yan’uwa maza da mata da yawa waɗanda Bulus ya aika wa gaisuwa ’yan Al’ummai ne. Wataƙila wasu daga “gidan Kaisar” ne, wanda ƙila yana nufin bayin Kaisar da ƙananan ma’aikata.—Filib. 4:22; Rom. 1:6; 11:13.
8. Waɗanne ƙalubale ne waɗanda ke Roma suka fuskanta?
8 Kowane Kirista da ke Roma ya fuskanci yanayi mai wuya da mu ma muke fuskanta a yau. Ga bayanin da Bulus ya yi: “Dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Rom. 3:23) Hakika, dukan waɗanda Bulus ya rubuta wa wasiƙar suna bukatar su fahimci cewa su masu zunubi ne kuma suna bukatar su yi imani ga yadda Allah zai yi maganin wannan yanayin.
Mutane Suna Bukatar Su Fahimci Su Masu Zunubi Ne
9. Bulus ya jawo hankali ga wanne sakamakon bishara?
9 Da farko a wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya ambata yadda bisharar da yake faɗa zai iya shafar mutane sosai: ‘Bishara ba abin kunya ba ce a gareni: gama ikon Allah ce zuwa ceto ga kowane mai-bada gaskiya; ga Ba-yahudi tukuna, da kuma ga Ba-helleni.’ E, zai yiwu a samu ceto. Amma dai, ana bukatar bangaskiya bisa ga muhimmiyar gaskiya da ke cikin littafin Habakkuk 2:4: “Adali ta wurin bangaskiyatasa za ya rayu.” (Rom. 1:16, 17; Gal. 3:11; Ibran. 10:38) Amma ta yaya bisharar, wadda za ta iya sa mutum ya samu ceto, ta shafi gaskiya cewa “dukan mutane sun yi zunubi”?
10, 11. Me ya sa wasu mutane sun fahimci abin da ke Romawa 3:23 amma wasu ba su fahimta ba?
10 Kafin mutum ya samu bangaskiya da za ta sa ya samu ceto, wajibi ne ya amince cewa shi mai zunubi ne. Hakan ba zai kasance da wuya ga waɗanda suka gaskata da wanzuwar Allah tun suna yara kuma sun ɗan fahimci Littafi Mai Tsarki ba. (Karanta Mai-Wa’azi 7:20.) Ko sun yarda ko kuma suna shakka, sun fahimci abin da Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: “Dukan mutane sun yi zunubi.” (Rom. 3:23) Amma sa’ad da muke hidima, za mu iya tarar da mutane da yawa da ba su fahimci wannan furucin ba.
11 Mutane a wasu ƙasashe ba su san cewa an haife su cikin zunubi ba, wato, sun gāji zunubi. Kuma wataƙila sun fahimci cewa suna kuskure kuma suna da halaye marasa kyau kuma wataƙila sun yi wasu laifuffuka. Sun kuma lura cewa wasu ma suna cikin irin wannan yanayin. Amma saboda yanayin da suka yi girma, ba su fahimci dalilin da ya sa su da wasu suke irin wannan yanayin ba. Hakika, a wasu harsuna, idan ka ce wani mai zunubi ne, wasu mutane za su yi zato cewa kana nufin cewa mutumin mugu ne ko kuma mai ƙarya dokoki ne. Hakika, mutumin da ya yi girma a irin wannan yanayin ba zai ɗauki kansa kamar mai zunubi ba yadda Bulus yake nufi.
12. Me ya sa mutane da yawa ba su amince cewa kowane mutum yana zunubi ba?
12 Ko ma a ƙasashen Kiristendam, mutane da yawa ba su amince cewa suna zunubi ba. Me ya sa? Ko da suna zuwan coci a wasu lokatai, suna ɗaukan labari na Littafi Mai Tsarki game da Adamu da Hauwa’u kamar tatsuniya ko ƙage. Wasu sun taso a wuraren da ake magabtaka da Allah. Sun yi shakka cewa Allah ya wanzu kuma ba su fahimci cewa Mafifici ya kafa mizani na ɗabi’a ga ’yan Adam ba kuma ƙin bin waɗannan mizanan zunubi ne. A wani azancin kuma, suna kamar waɗanda Bulus ya bayyana a ƙarni na farko a matsayin “marasa bege” da kuma “marasa-Allah cikin duniya.”—Afis. 2:12.
13, 14. (a) Wanne dalili ɗaya ne ya sa waɗanda ba su amince da wanzuwar Allah ba da kuma zunubi ba su da hujja? (b) Mene ne sakamakon wannan rashin aminci?
13 Bulus ya bayyana dalilai biyu a cikin wasiƙarsa ga Romawa da suka sa hakan ba hujja ba ce a lokacin da kuma a yau. Dalili na farko shi ne cewa halitta ta shaida wanzuwar Mahalicci. (Karanta Romawa 1:19, 20.) Hakan ya jitu da abin da Bulus ya lura da shi sa’ad da yake rubuta zuwa ga Ibraniyawa daga Roma: “Kowane gida akwai mai-kafa shi; amma wanda ya kafa dukan abu Allah ne.” (Ibran. 3:4) Hakan ya nuna cewa akwai Mahalicci da ya halicci sararin samaniya gabaki ɗaya.
14 Saboda haka, Bulus yana da ƙwaƙƙwarar tabbaci sa’ad da ya rubuta wa Romawa cewa, kowanne, haɗe da Isra’ilawa na dā, wanda ya bauta wa gumaka marasa rai ba su da “hujja.” Hakan ma yake da waɗanda suka faɗa wa zunubin fasikanci, sun sauya ɗabi’a tasu ta halal tsakanin namiji da ta mace. (Rom. 1:22-27) Da yake magana game da wannan, Bulus ya kammala cewa “Yahudawa duk da Hellenawa, ƙarƙashin zunubi su ke duka.”—Rom. 3:9.
Mai ‘Ba da Shaida’
15. Su wane ne suke da lamiri, kuma da wane sakamako?
15 Littafin Romawa ya ambata wani dalilin da ya sa ya kamata mutane su fahimci cewa su masu zunubi ne kuma suna bukatar mafita. Game da dokar da Allah ya ba Isra’ilawa na zamanin dā, Bulus ya rubuta: “Dukan waɗanda sun yi zunubi a cikin shari’a, bisa ga shari’a za a hukunta masu.” (Rom. 2:12) Ya ci gaba da bayaninsa cewa mutanen al’umma da sun saba da shari’ar Allah sukan yi abu “bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a.” Me ya sa waɗannan suke ƙyamar jima’i tsakanin dangi da kisa da kuma sata? Bulus ya faɗi dalilin: Suna da lamiri.—Karanta Romawa 2:14, 15.
16. Me ya sa samun lamiri kaɗai ba zai hana mutum yin zunubi ba?
16 Wataƙila ka ga cewa samun lamiri da ke shari’anta mutum ba ya nufin cewa lallai sai mutum ya bi ja-gorancin lamirin ba. Abin da ya faru a Isra’ila ta dā ya nuna hakan. Ko da yake Isra’ilawa suna da lamiri da Allah ya ba su da kuma dokoki daga Allah game da sata da zina, amma sau da yawa ba su yi biyayya ga wannan lamiri da kuma Dokar Jehobah ba. (Rom. 2:21-23) Laifinsu yana da tsanani don hakan su masu zunubi ne, sun kasa yin rayuwa da ta jitu da mizani da kuma nufin Allah. Hakan ya ɓata dangantakarsu da Mahaliccinsu.—Lev. 19:11; 20:10; Rom. 3:20.
17. Wanne ƙarfafa ne muka samu a littafin Romawa?
17 Kamar dai abin da muka tattauna daga littafin Romawa yana kwatanta yanayin ’yan Adam a gaban Maɗaukaki duka, haɗe da mu. Amma dai, ba shi ke nan abin da Bulus ya faɗa ba. Da yake ƙaulin kalaman Dauda a littafin Zabura 32:1, 2, manzon ya rubuta: “Masu-albarka ne su waɗanda an gafarta tawayensu waɗanda an rufa zunubansu. Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba zai lissafta zunubi gare shi ba.” (Rom. 4:7, 8) Hakika, Allah ya sa ya yiwu a gafarta zunubinmu ba tare da ƙarya mizanansa ba.
Bisharar Game da Yesu Ne
18, 19. (a) Ga wane fanni na bishara ne Bulus ya mai da wa hankali a littafin Romawa? (b) Me ya kamata mu ankara don mu samu albarkar Mulkin?
18 Za ka iya cewa, “Lallai wannan bishara ce!” Hakika hakan gaskiya ne, kuma ya mai da hankalinmu ga sashen bisharar da Bulus ya nanata a littafin Romawa. Kamar yadda aka ambata, Bulus ya rubuta: “Bishara ba abin kunya ba ce a gareni: gama ikon Allah ce zuwa ceto.”—Rom. 1:15, 16.
19 Bisharar ta mai da hankali ga matsayin Yesu a cikar nufin Allah. Bulus ya yi ɗokin ‘rana da Allah za ya shara’anta asiran mutane, bisa ga bisharar.’ (Rom. 2:16) Ta wajen faɗan hakan, bai rage muhimmancin “mulkin Kristi da na Allah” ba ko kuma abin da Allah zai cim ma ta Mulkin. (Afis. 5:5) Amma ya nuna cewa don mu rayu kuma mu more albarkar da za ta kasance a ƙarƙashin Mulkin Allah, wajibi ne mu ankara cewa (1) a gaban Allah mu masu zunubi ne da (2) dalilin da ya sa ya kamata mu yi imani ga Yesu Kristi don a gafarta zunubanmu. Idan mutum ya fahimci kuma ya amince da wannan fanni na nufin Allah kuma ya ga yadda hakan ya ba shi bege, zai iya furtawa, “Hakika, wannan bishara ce!”
20, 21. Me ya sa ya kamata mu tuna da bisharar da aka ambata a littafin Romawa a hidimarmu, kuma da wane sakamako?
20 Ya kamata mu tuna da wannan fanni na bishara sa’ad da muka fita hidimar Kirista. Sa’ad da yake kwatanta Yesu, Bulus ya yi ƙaulin kalaman Ishaya: “Dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ba za ya kunyata ba.” (Rom. 10:11; Isha. 28:16) Wataƙila ainihin saƙo game da Yesu ba zai kasance sabon abu ba ga waɗanda suka san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da zunubi. Amma ga wasu wannan saƙon sabon abu ne, abin da ba su sani ko amince a al’adarsu ba. Yayin da irin waɗannan mutanen suka gaskata ga Allah kuma suka dogara ga Nassosi, za mu bukaci mu bayyana musu matsayin Yesu. Talifi na gaba zai tattauna yadda Romawa sura ta 5 ta bayyana wannan fanni na bisharar. Wataƙila, wannan nazarin zai taimake ka a hidimarka.
21 Yana da kyau sosai a taimaka wa masu zukatan kirki su fahimci bisharar da aka ambata sau da yawa a littafin Romawa, wato, bisharar wadda “ikon Allah ce zuwa ceto ga kowane mai-bada gaskiya.” (Rom. 1:16) Fiye da albarkar da za mu samu, za mu ga mutane suna amincewa da kalaman da Bulus ya yi ƙaulinsa a Romawa 10:15: “Ina misalin darajan ƙafafu na masu-kawo bishara ta alheri!”—Isha. 52:7.
[Hasiya]
a Irin waɗannan furucin sun bayyana a wasu hurarrun littattafai.—Mar. 1:1; A. M. 5:42; 1 Kor. 9:12; Filib. 1:27.
Ka Tuna?
• Wanne fannin bisharar ne littafin Romawa ya nanata?
• Wace gaskiya ce ya kamata mu taimaka wa mutane su fahimta?
• Ta yaya “bishara game da Kristi” za ta iya kawo mana da kuma wasu albarka?
[Bayanin da ke shafi na 8]
Bisharar da aka ambata a littafin Romawa ta haɗa da matsayi mai muhimmanci na Yesu a nufin Allah
[Hoto a shafi na 9]
An haife mu duka da tabo mai tsanani, wato, zunubi!