Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 4/1 pp. 5-7
  • Albarkar Mulki Za ta Iya Zama Taka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Albarkar Mulki Za ta Iya Zama Taka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sakewa da Ya Kawo Albarka
  • Menene Za Ka Yi?
  • Da Akwai Taimako
  • Akwai Bishara Da Dukan Mutane Suke Bukata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Bisharar Mulki—Mecece Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 4/1 pp. 5-7

Albarkar Mulki Za ta Iya Zama Taka

KIRISTA manzo Bulus ya iya wasu harsuna na musamman na zamaninsa. Ya samu ilimi da ya yi daidai da na jami’a a yau. Ya more duka albarkar zama ɗan ƙasar Roma. (Ayukan Manzanni 21:37-40; 22:3, 28) Waɗannan iyawar da za su sa shi yin arziki kuma zama mashahuri. Duk da haka ya ce: “Duk da wannan abubuwan da su ke ribobi a gareni, waɗannan na lissafta su hasara sabili da Kristi . . . kamar najasa kuwa ni ke maishe su, domin in ribato Kristi.” (Filibbiyawa 3:7, 8) Me ya sa Bulus ya yi irin wannan maganar?

Dā an san shi da Shawulu na Tarsus da mai tsananta waɗanda “su ke na Tafarkin,” Bulus ya zama mai bi bayan da aka nuna masa wahayi na Yesu wanda aka ta da daga matattu kuma aka ɗaukaka shi. (Ayukan Manzanni 9:1-19) Ga Bulus, wannan abu da ya gani a hanyar Dimashka ya nuna sarai cewa Yesu ne Almasihu, ko Kristi da aka yi alkawarinsa, mai sarautar Mulki da aka yi alkawarinsa a nan gaba. Ya kuma kawo canji na ban mamaki a tafarkin rayuwar Bulus, yadda furcinsa mai ƙarfi ya nuna a saman nan. A wata sassa, a nuna gaskiya daga zuciya, Bulus ya tuba.—Galatiyawa 1:13-16.

A cikin Littafi Mai Tsarki, fi’ilin nan “tuba” sau da yawa ana fassara shi daga kalmar Helenanci da a zahiri ke nufin “bayan an sani,” da ke hamayyar “sanin nan gaba.” Da haka, tuba ta ƙunshi canji daga zuciyar mutum, hali, ko nufi, mutum ya ƙi hanyoyinsa na dā cewa ba masu gamsarwa ba ne. (Ayukan Manzanni 3:19; Ru’ya ta Yohanna 2:5) A zancen Bulus, bai bar wannan aukuwa mai girma a hanyar Dimashka ta zama masa damuwa ko kuma abin da ya fuskanci kawai na addini ba. A gare shi, an nuna masa cewa hanyar rayuwarsa ta dā cikin rashin sanin Kristi banza ne. Ya kuma gane cewa don ya amfana daga sabon sani da ya samo game da Kristi, dole ya yi abu don ya gyara tafarkin rayuwarsa.—Romawa 2:4; Afisawa 4:24.

Sakewa da Ya Kawo Albarka

A dā, ilimin Bulus game da Allah ya zo musamman daga ɗarikar Farisiyawa, yana ɗaya cikinsu. Imaninsu ya ƙunshi falsafar al’adar ’yan Adam da yawa ne. Saboda wariyar addini, himma da ƙoƙarin Bulus ya kauce hanya. Ko da yana jin yana bauta wa Allah, da gaske yana yaƙi da shi ne.—Filibbiyawa 3:5, 6.

Bayan ya samu cikakken sani game da Kristi da matsayinsa a nufin Allah, Bulus yana da zaɓe da zai yi: Zai ci gaba da zama Ba’farisi kuma ci gaba da moran matsayi da ɗaukaka, ko kuma zai canja tafarkin rayuwarsa kuma ya soma yin dukan abin da ake bukata don Allah ya amince da shi? Abin farin ciki, Bulus ya yi zaɓe da ke daidai, gama ya ce: “Gama bishara ba abin kunya ba ce a gareni: gama ikon Allah ce zuwa ceto ga kowane mai-bada gaskiya; ga Ba-yahudi tukuna, da kuma ga Ba-heleni.” (Romawa 1:16) Bulus ya zama mai wa’azin bishara mai himma game da Kristi da kuma Mulkin.

Shekaru da yawa daga baya, Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci: “ ’Yan’uwa, ni ban maida kaina na ruska ba tukuna: amma abu ɗaya ni ke yi, ina manta da abubuwan da ke baya, ina kutsawa zuwa ga waɗanda ke gaba, ina nace bi har zuwa ga [buri], in kai ga ladan nasara na maɗaukakiyar kira ta Allah cikin Kristi Yesu.” (Filibbiyawa 3:13, 14) Bulus ya amfana daga bisharar domin da son rai ya ƙyale abin da yake jan shi daga Allah kuma da duka zuciyarsa ya biɗi makasudai da ke daidai da nufin Allah.

Menene Za Ka Yi?

Wataƙila a baya bayan nan ne ka ji bisharar mulki. Kana murna da begen rayuwa na har abada cikin kamilcacciyar aljanna? Ya kamata, da yake dukanmu muna da sha’awar rayuwa kuma muna more rayuwa cikin salama da kwanciyar rai. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya sa “madawwaman zamanai” a cikin zuciyarmu. (Mai-Wa’azi 3:11) Saboda haka, daidai ne muna begen lokacin da mutane za su yi rayuwa har abada cikin salama da farin ciki. Kuma abar da bisharar Mulki take bayarwa ke nan.

Amma don wannan begen ya zama gaskiya, kana bukatar ka bincika kuma ka san abar da bisharar take maganarta. Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Ku gwada [kanku] ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” (Romawa 12:2) Saboda haka, kamar Bulus bayan ka samu sani da fahimta, dole ka yi zaɓe.

A wata sassa, wataƙila ka riga kana da wasu imani game da nan gabanka. Ka tuna cewa Shawulu yana da nasa ra’ayoyi game da nufin Allah kafin ya zama manzo Bulus. Amma maimako kana zaton wahayi na mu’ujiza daga Allah, me ya sa ba za ka bincika al’amarin sosai ba? Ka tambayi kanka: ‘Na san abin da nufin Allah yake game da ’yan Adam da kuma duniya? Wane dalili zan iya bayarwa don goyon bayan imanina? Dalilina ƙaƙarfa ne idan aka bincika bayanin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki?’ Ba za ka yi hasarar kome ba idan ka bincika imanin addininka a wannan hanyar. Hakika, ya kamata ka yi hakan domin Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku auna abu duka; ku riƙe mai-kyau.” (1 Tassalunikawa 5:21) Ballantana ma, ba amincewar Allah ba ne ya fi muhimmanci?—Yohanna 17:3; 1 Timothawus 2:3, 4.

Shugabannan addinai za su iya yi mana alkawarin nan gaba madawwami. Sai dai wannan alkawarin ya dangana a koyarwar Littafi Mai Tsarki, ba zai taimake mu samun albarkar Mulkin Allah ba. A sanannen Hudubarsa na Bisa Dutse, Yesu ya yi kashedi sosai: “Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aika nufin Ubana wanda ke cikin sama.”—Matta 7:21.

Ka lura da cewa Yesu ya nanata yin nufin Ubansa shi ne abin da samun albarkar Mulkin Allah ya dangana a kai. A wata sassa, Allah ba zai amince da abar da ke lamunin ibada ba. Hakika, Yesu ya ci gaba da cewa: “A cikin wannan rana mutane dayawa za su ce mini, Ubangiji, Ubangiji, ba mu yi annabci da sunanka ba, da sunanka kuma muka fitarda aljanu, da sunanka kuma muka yi ayyuka dayawa masu-iko? Sa’annan zan furta masu Ban taɓa saninku ba daɗai: rabu da ni, ku masu-aika mugunta.” (Matta 7:22, 23) A bayyane, abin da yake da muhimmanci shi ne, mu tabbata cewa mun fahimci abin da bishara ta Mulkin take sosai kuma mu aikata cikin jituwa da ita.—Matta 7:24, 25.

Da Akwai Taimako

Fiye da shekara 100, Shaidun Jehovah suna wa’azin bishara ta Mulkin Allah. Ta wurin littattafai da aka buga da kuma ta maganar baki, suna taimakon mutanen duniya kewaye su samu cikakken sani game da abin da Mulkin yake, albarka da zai kawo, kuma abin da mutum dole ya yi don ya samu irin wannan albarkar.

Muna ƙarfafa ka ka saurara ga wa’azin da Shaidun Jehovah suke yi. Ta wurin karɓa da kuma aika a kan bisharar, za ka iya samun albarka mai girma—ba yanzu kawai ba amma kuma a gaba lokacin da Mulkin Allah zai yi sarautar dukan duniya.—1 Timothawus 4:8.

Ka aikata abin da ya kamata yanzu, domin albarkar Mulkin Allah ta kusa!

[Hotuna a shafi na 7]

Ta wurin littattafai da aka buga da kuma maganar baki, Shaidun Jehovah suna wa’azin bishara ta Mulkin Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba