Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 4/1 pp. 3-5
  • Bisharar Mulki—Mecece Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bisharar Mulki—Mecece Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Mulkin?
  • “Mulkin Sama Ya Kusa”
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Albarkar Mulki Za ta Iya Zama Taka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Akwai Bishara Da Dukan Mutane Suke Bukata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 4/1 pp. 3-5

Bisharar Mulki—Mecece Ce?

Bara a ƙasashe 235 kewaye da duniya, mutane 6,035,564, manya da yara, sun ba da sa’o’i 1,171,270,425 wajen yi wa wasu magana game da ita. Ƙari ga idar ta maganar baki, sun saka a hannun mutane littattafai fiye da miliyan 700 don su sanar kuma su bayyana ta. Sun kuma rarraba dubban kaset da tef na bidiyo don su yi shelarta. Mecece ce?

BISHARAR Mulkin Allah ce. Da gaske, ba a taɓa yin wa’azin “wannan bishara kuwa ta mulki” a tarihin ’yan Adam yadda muke ganinta a yau ba.—Matta 24:14.

Waɗanda suke wannan aikin wa’azi da koyarwa a dukan duniya dukansu waɗanda suka ba da kansu ne. A tunanin mutanen duniya, kamar ba su kai mizanin iya aiki ba. To, menene ke sa su gaba gaɗi da nasara? Ikon bisharar Mulki shi ne abu na musamman, labari ne game da albarka da za ta zo wa mutane. Albarka ce da dukan mutane suke sauraranta—farin ciki, ’yanci daga tattalin arziki, gwamnati mai kyau, salama da kwanciyar rai, da wani abu da yawancin mutane suke gani ba zai yiwu ba—rai madawwami! Hakika wannan albishiri ne mai daɗi ga mutane masu neman ma’ana ga manufar rayuwa. Hakika, duka waɗannan albarka da wasu za su zama naka idan ka saurara kuma ka aikata abin da yake da kyau ga shelar bisharar Mulkin.

Menene Mulkin?

To, menene Mulkin da ake sanar da bishararsa? Mulki ne da aka koya wa miliyoyin mutane su yi addu’a dominsa a waɗannan kalmomi da aka sani sosai: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Matta 6:9, 10.

Mulki ne da annabi Daniel Ba’ibrane ya yi maganarsa fiye da ƙarnuka 25 yayin da ya rubuta: “Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.

Da haka, bisharar game da Mulkin ne, ko gwamnati, ta Allah da za ta kawar da dukan mugunta sai ta yi sarauta bisa duka duniya cikin salama. Zai sa nufi na asali na Mahaliccin ga ’yan Adam da kuma duniya ya zama gaskiya.—Farawa 1:28.

“Mulkin Sama Ya Kusa”

Kusan shekara 2,000 da ta shige, wani mutumin da ya keɓe kansa ne ya fara sanar da bisharar Mulkin a fili wanda yadda yake da kuma halinsa ya jawo hankalin mutane. Wannan mutumin Yohanna Mai Baftisma ne, ɗan firist Zakariya Ba’yahude da matarsa, Alisabatu. Yohanna na sanye da tufa ta gashin raƙumi, yana ɗaura ɗamara ta fata, yadda annabi Iliya dā yake, wanda ke wakilta shi. Amma saƙonsa ne ya jawo hankalin mutane da yawa. Yana cewa, “Ku tuba; gama mulkin sama ya kusa.”—Matta 3:1-6.

Yahudawa da suke da’awar suna bauta wa Allah na gaskiya, Jehovah, sune masu sauraron Yohanna. Su al’umma, sun karɓi Doka ta alkawari ta wurin Musa misalin shekara 1,500 a farko. Haikali mai girma har ila yana tsaye a Urushalima, inda ake miƙa hadayu daidai da Dokar. Yahudawa sun tabbata cewa bautarsu daidai ce a gaban Allah.

Amma, da suke saurarar Yohanna, wasu mutane suka soma fahimta cewa addininsu ba yadda suke tsammaninsa yake ba. Al’adar Helenanci da falsafa sun ɓata koyarwar addinin Yahudawa. Aka surka doka da ta zo daga Allah ta bakin Musa, har aka sa ba ta da daraja, ta wajen imanin da mutane suka kafa da kuma al’adu. (Matta 15:6) Da yake shugabanan addinai masu taurin zuciya da marar tausayi sun yaudare su, yawancin mutane ba sa yi wa Allah sujjada da yake gamsar da shi. (Yaƙub 1:27) Suna bukatar su tuba daga zunubansu ga Allah da kuma ga Doka ta alkawari.

A lokacin nan, Yahudawa da yawa suna jiran Almasihu, ko Kristi da aka yi alkawarinsa ya bayyana, wasu suna mamaki game da Yohanna: “Ko wataƙila shi Kristi ne.” Amma Yohanna ya ce ba shi ba ne kuma ya nuna musu wani, wanda game da shi ya ce: “Maɓallin takalmansa ban isa in kwance shi ba.” (Luka 3:15, 16) Da yake gabatar da Yesu ga almajiransa, Yohanna ya sanar: “Duba, ga Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya!”—Yohanna 1:29.

Wannan kuwa labari mai daɗi ne, wato, Yohanna yana nuna wa duka mutanen hanyar rai da farin ciki—Yesu, wanda “yana ɗauke da zunubin duniya.” Da yake su zuriyar Adamu da Hauwa’u ne, an haife dukan mutane a ƙarƙashin tasku na zunubi da mutuwa. Romawa 5:19 ta bayyana: “Kamar yadda ta wurin kangarar ɗayan nan [Adamu] masu-yawa suka zama masu zunubi, hakanan ta wurin biyayyar ɗayan [Yesu] masu-yawa za su barata.” Yesu, ɗan rago na hadaya, zai ‘ɗauke zunubi’ kuma zai sake mummunar yanayi na harkokin mutane. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa, “hakkin zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”—Romawa 6:23.

Kamilcaccen mutum—hakika, mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa—Yesu ya soma yin wa’azin bisharar. Labarin Littafi Mai Tsarki a Markus 1:14, 15 ya gaya mana: “Bayanda aka bada Yohanna, Yesu ya taho cikin Galili, yana wa’azin bishara ta Allah, ya ce, Zamani ya cika, mulkin Allah kuwa yana nan: ku tuba ku bada gaskiya ga bisharan.”

Waɗanda suka saurari saƙon Yesu kuma ba da gaskiya a bisharar an albarkace su sosai. Yohanna 1:12 ya ce: “Iyakar waɗanda suka karɓe shi [Yesu], ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah, watau waɗannan da su ke bada gaskiya ga sunansa.” Da yake sun zama ’ya’yan Allah, suna cikin layin samun ladar rai madawwami.—1 Yohanna 2:25.

Amma gatar samun albarkar Mulki ba ga mutane a ƙarni na farko kawai ba. Yadda aka ambata a sama, ana shela kuma koyar da bisharar Mulkin Allah a duniya duka. Saboda haka, albarkar Mulki har ila yau akwai ta. Menene dole ka yi don ka sami irin albarkar nan? Talifi na biye zai bayyana.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba