Ka Koya Daga Kalmar Allah
Mene Ne Mulkin Allah?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Mene ne Mulkin Allah?
Mulkin Allah gwamnati ce ta samaniya. Zai sauya dukan gwamnatoci kuma zai sa a yi nufin Allah a sama da duniya. Saboda haka, Mulkin Allah ne zai biya bukatar da muke da ita na gwamnati mai kyau.—Karanta Daniyel 2:44; Matta 6:9, 10.
Dole ne mulki ya kasance da sarki. Jehobah ya naɗa Ɗansa, Yesu, ya zama Sarkin Mulkinsa.—Karanta Luka 1:30-33.
2. Me ya sa Yesu ne Sarkin da ya dace?
Ɗan Allah ne Sarkin da ya dace domin yana da kirki, yana tashi tsaye a kan abin da ke da kyau, kuma yana da isashen ikon taimaka wa mutane. (Matta 11:28-30) Bayan da aka ta da shi daga matattu, Yesu ya koma sama kuma ya yi jira a hannun damar Jehobah. (Ibraniyawa 10:12, 13) A ƙarshe, Allah ya ba shi ikon yin sarauta daga sama.—Karanta Daniyel 7:13, 14.
3. Su waye ne kuma za su yi sarauta tare da Yesu?
Wani rukuni da ake kira ‘tsarkakku’ waɗanda Allah ya zaɓa ne za su yi mulki tare da Yesu a sama. (Daniyel 7:27) Waɗanda aka soma zaɓa domin su zama tsarkakku su ne amintattun manzannin Yesu. Har zuwa wannan lokaci Jehobah yana ci gaba da zaɓan amintattun maza da mata a matsayin tsarkakku. Kamar Yesu, ana ta da su ne daga matattu a matsayin ruhu.—Karanta Yohanna 14:1-3; 1 Korintiyawa 15:42-45.
Mutane nawa ne za su je sama? Yesu ya kira su “ƙaramin garke.” (Luka 12:32) A ƙarshe, adadinsu zai kai 144,000, kuma za su yi sarauta a kan duniya tare da Yesu.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1.
4. A yaushe ne Mulkin Allah ya soma sarauta?
Yesu ya zama Sarki ne a shekara ta 1914.a Jim kaɗan bayan haka, ya jefo Shaiɗan tare da aljanunsa zuwa duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-10, 12) Tun daga lokacin, matsalolin ’yan Adam suka ƙaru sosai. Yaƙe-yaƙe, girgizar ƙasa, yunwa, annoba da kuma aikata laifi suna cikin alamun da ke nuna cewa zamanin nan yana kwanakinsa na ƙarshe. (2 Timotawus 3:1-5) Dukan waɗanda suke so su amfana daga Mulkin Allah suna bukatar su koyi yadda za su zama mabiyan Sarkin, Yesu.—Karanta Luka 21:7, 10, 11, 31, 34, 35.
5. Mene ne Mulkin Allah zai cim ma?
Ta wajen aikin wa’azin da ake yi a dukan duniya, Mulkin Allah yana taimaka wa miliyoyin mutane daga dukan al’ummai su koyi hanyoyin Allah. (Matta 24:14) Zai kāre “taro mai-girma” na amintattun talakawan Yesu yayin da yake halaka wannan mugayen al’amuran da ke faruwa a wannan duniyar.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, 13-17.
A cikin shekara dubu, da sannu a hankali Mulkin zai mai da duniya aljanna. A ƙarshe, Yesu zai miƙa Mulkin ga Ubansa. (1 Korintiyawa 15:24-26) Ka san wani da za ka so ka gaya masa game da Mulkin Allah?—Karanta Zabura 37:10, 11, 29.
Domin samun ƙarin bayani ka duba babi na 8 da na 9 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hasiya]
a Domin samun cikakken bayani game da yadda annabci na Littafi Mai Tsarki yake nuni ga shekara ta 1914, ka duba shafuffuka na 215-218 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.