Ku Koyar Da Yaranku
Dalilin da Ya Sa Mutane Suke Ƙaunar Dokas
DUKANMU muna so mutane su nuna mana ƙauna. Kana son hakan?—a Mun karanta labarin Dokas a cikin Littafi Mai Tsarki, wadda mace ce da mutane suke ƙauna sosai.
Dokas tana da zama ne a Yafa, wani gari da ke kusa da Bahar Rum. Urushalima tana da nisan kilomita 56 daga Yafa. Dokas tana ɗaya daga cikin almajiran farko na Yesu.
Mene ne ya sa ake ƙaunar Dokas sosai?— Littafi Mai Tsarki ya ce ta yi ayyuka masu kyau da yawa kuma ta ba da kyauta masu kyau. Babu shakka, ta yi wa gwauraye sitiru masu kyau, wato, matan da mazansu suka mutu. Ta kuma yi wa mutane da yawa magana game da Allah na gaskiya, Jehobah, kamar yadda Yesu ya yi.
Ka san mummunar abin da ya faru ga Dokas yanzu?— Ta yi rashin lafiya mai tsanani kuma ta mutu. Dukan abokanta sun yi baƙin ciki. Sai suka aika wasu mutane zuwa inda manzo Bitrus yake da zama, tafiyar wajen kilomita 16. Mutanen nan suka ce masa ya zo da wuri. Sa’ad da Bitrus ya iso, ya hau gidan sama inda Dokas take. Dukan matan suna kuka, kuma suka nuna masa sitiru da Dokas ta yi musu.
Sai Bitrus ya gaya wa kowa ya bar ɗakin. Bitrus da sauran manzanni sun taɓa yin mu’ujizai, amma babu wani a cikinsu da ya taɓa ta da wanda ya mutu. Me kake tsammani Bitrus zai yi yanzu?—
Bitrus ya durƙusa kusa da gawar kuma ya yi addu’a ga Jehobah. Sai ya gaya wa Dokas ta tashi. Sai kuwa ta tashi! Bitrus ya miƙa mata hannunsa don ya taimaka mata ta tashi tsaye. Bayan hakan, ya kira gwaurayen da sauran mutanen da ke wajen kuma ya nuna musu ita. Za ka iya yin tunanin irin farin ciki da suka yi?—
Bari mu ga abin da za ka iya koya daga wannan labarin na ta da Dokas daga matattu. Wani abin da labarin ya nuna shi ne, idan kana taimaka wa mutane, da yawa daga cikinsu za su so ka ƙwarai. Amma mafi muhimmanci shi ne, Allah zai tuna da kai kuma zai so ka. Ba zai taɓa mance abubuwa masu kyau da ka yi wa mutane ba. Kuma zai ba ka rai madawwami cike da farin ciki a sabuwar duniyarsa.
Ka karanta wuraren nan a cikin naka Littafi Mai Tsarki
Ru’ya ta Yohanna 21:3-5
[Hasiya]
a Idan kana karatun ne da yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.