Ka Bi Tafarkun Jehobah
“Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda ke zamansa bisa ga umarninsa!”—Zab. 128:1, Littafi Mai Tsarki.
1, 2. Me ya sa za mu tabbata cewa zai yiwu a sami farin ciki?
KOWA yana son ya yi farin ciki. Amma za ka yarda cewa neman farin ciki ba ya nufin cewa mutum yana farin ciki.
2 Duk da haka, za a iya samun farin ciki. “Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda ke zamansa bisa ga umarninsa!” in ji Zabura 128:1. Za mu yi farin ciki idan muka bauta wa Allah kuma muka bi tafarkunsa ta wajen yin nufinsa. Ta yaya ne hakan zai shafi halinmu?
Ka Kasance Mai Gaskiya
3. Ta yaya ne gaskiya ya jitu da keɓe kanmu da muka yi ga Allah?
3 Waɗanda suke jin tsoron Jehobah suna yin gaskiya kamarsa. Jehobah ya cika dukan alkawarin da ya yi wa Isra’ila ta dā. (1 Sar. 8:56) Keɓe kai da muka yi ga Allah shi ne alkawari mafi muhimmanci da muka ɗauka, kuma yin addu’a a kowane lokaci zai taimake mu mu cika ta. Muna iya yin addu’a kamar yadda mai zabura Dauda ya yi: “Gama ka ji wa’adodina, ya Allah. . . . Hakanan zan raira yabo ga sunanka tuttur, Domin in cika wa’adodina kowace rana.” (Zab. 61:5, 8; M. Wa. 5:4-6) Idan muna son mu kasance abokan Allah, dole ne mu kasance masu gaskiya.—Zab. 15:1, 4.
4. Ta yaya ne Jephthah da ɗiyarsa suka ɗauki alkawarin da ya yi wa Jehobah?
4 A zamanin Alƙalan Isra’ila, Jephthah ya ɗauki alkawari cewa idan Jehobah ya sa ya yi nasara a kan Ammoniyawa, zai ba da mutumin da ya fara yi masa maraba sa’ad da ya dawo daga yaƙi a matsayin “hadaya ta ƙonawa.” Ɗiyar Jephthah ce ta fara fitowa, kuma ita kaɗai ce kawai ya haifa. Domin sun ba da gaskiya ga Jehobah, Jephthah da ɗiyarsa budurwa sun cika wannan alkawarin. Ko da yake ana ɗaukan aure da haihuwa da muhimmanci sosai a Isra’ila, ɗiyar Jephthah da son rai ta ƙi yin aure kuma ta more gatan yin hidima mai tsarki a gidan Allah.—Alƙa. 11:28-40.
5. A wane ɓangare ne Hannatu ta kasance mai gaskiya?
5 Hannatu mace mai tsoron Allah ta kasance mai gaskiya. Tana zaune ne ita da mijinta Elkanah, Balawi, da kuma kishiyarta, Peninnah, a tuddan Ifraimu. Peninnah ta haifi yara da yawa kuma tana yi wa Hannatu wadda ba ta taɓa haihuwa ba dariya musamman sa’ad da iyalin ta tafi mazauni. Wata rana, Hannatu ta ɗauki alkawari cewa idan ta haifi ɗa, za ta ba da shi ga Jehobah. Ba da daɗewa ba ta sami ciki kuma ta haifi ɗa wanda aka sa wa suna Sama’ila. Bayan ta yaye shi, Hannatu ta miƙa shi ga Allah a Shiloh, kuma ta ba da Sama’ila ga Jehobah a “dukan kwanakinsa.” (1 Sam. 1:11, Littafi Mai Tsarki.) Da haka, ta cika alkawarinta ko da yake ba ta san cewa za ta sake haifan wasu yaran ba.—1 Sam. 2:20, 21.
6. Ta yaya ne Tikikus ya nuna cewa shi mai aminci ne?
6 Kirista na ƙarni na farko Tikikus shi ma ya kasance mutum mai gaskiya da kuma “mai-hidima mai-aminci.” (Kol. 4:7) Tikikus ya bi manzo Bulus daga Hellas har Makidoniya, zuwa Asiya Ƙarama, wataƙila ma har zuwa Urushalima. (A. M. 20:2-4) Wataƙila shi ne ‘ɗan’uwan’ da ya taimaka wa Titus su shirya kayan Kiristoci mabukata a Yahudiya. (2 Kor. 8:18, 19; 12:18) Sa’ad da aka fara jefa Bulus a cikin kurkuku a ƙasar Roma, ya aiki Tikikus amintacce ya kai wasiƙu ga ’yan’uwa masu bi da ke Afisa da Kolosi. (Afis. 6:21, 22; Kol. 4:8, 9) Sa’ad da aka sake ɗaure Bulus a ƙasar Roma, ya aika Tikikus zuwa Afisa. (2 Tim. 4:12) Idan mu mutane ne masu gaskiya, mu ma za mu sami albarka a hidimar Jehobah.
7, 8. Me ya sa za mu iya cewa Dauda da Jonathan abokai ne na gaskiya?
7 Allah yana son mu abokansa mu kasance masu gaskiya. (Mis. 17:17) Jonathan ɗan sarki Saul ya zama abokin Dauda. Sa’ad da Jonathan ya ji cewa Dauda ya kashe Goliyat, “Ran Jonathan ya saje da ran Dauda, Jonathan kuma ya ƙaunace shi kamar ransa.” (1 Sam. 18:1, 3) Jonathan ya gargaɗi Dauda sa’ad da Saul yake son ya kashe shi. Bayan da Dauda ya gudu, Jonathan ya je ya same shi kuma suka yi wa juna alkawari. Sai da Saul ya so ya kashe Jonathan saboda ya yi masa magana game da Dauda, amma waɗannan abokan biyu sun sake haɗuwa kuma suka sabonta abotarsu. (1 Sam. 20:24-41) A haɗuwarsu ta ƙarshe, Jonathan ya ƙarfafa Dauda cewa zai sami “kiyayewar Allah.”—1 Sam. 23:16-18, Littafi Mai Tsarki.
8 Jonathan ya mutu sa’ad da suke yaƙi da Filistiyawa. (1 Sam. 31:6) A waƙar baƙin cikin da ya yi, Dauda ya rera: “Raina ya ƙuntata sabili da kai, ɗan’uwana Jonathan, Mai-daɗi ka ke a gareni ƙwarai: Ƙaunarka a gareni abin al’ajibi ne, Ta fi ƙarfin ƙaunar mata.” (2 Sam. 1:26) Dauda da Jonathan abokai ne na gaske kuma suna ƙaunar juna sosai.
Ka Kasance Mai “Tawali’u” a Koyaushe
9. Ta yaya aka nuna muhimmancin tawali’u a littafin Alƙalawa sura 9?
9 Idan muna son mu zama abokan Allah, dole ne mu zama “masu-tawali’u.” (1 Bit. 3:8; Zab. 138:6) An nuna muhimmancin kasancewa da tawali’u a littafin Alƙalawa sura 9. Jotham, ɗan Gidiyon ya ce: “Wata rana itatuwa suka tafi domin su naɗa ma kansu sarki.” Ya ambata icen zaitun, ɓaure, da kuringar anab. Sune suka wakilci mutane masu tawali’u da ba sa son su sarauci ’yan’uwansu Isra’ilawa. Amma ƙaya, wadda ake ƙona abubuwa da ita, ita ce take wakiltar sarautar Abimelech mai fahariya kuma mai kisan kai wanda yake son ya shugabanci wasu. Ko da yake ya ci gaba da ‘yin sarauta a Isra’ila har tsawon shekaru uku,’ ya mutu tun bai tsufa ba. (Alƙa. 9:8-15, 22, 50-54) Hakan ya nuna cewa yana da kyau sosai mu kasance “masu tawali’u”!
10. Menene ka koya daga ƙin “bada girma ga Allah” da Hirudus ya yi?
10 A ƙarni na farko na zamanin mu, an sami matsala a tsakanin Sarki Hirudus Agaribas na Yahudiya mai fahariya da kuma mutanen ƙasar Sur da Sida, waɗanda suka nemi su zauna lafiya da shi. Sa’ad da Hirudus yake ba da jawabi ga mutane, sai suka soma cewa da babbar murya: “Muryar wani allah ke nan, ba ta mutum ba ce.” Domin Hirudus bai ƙi wannan ɗaukakar ba, mala’ikan Jehobah ya buge shi har ya mutu domin “ba ya bada girma ga Allah ba.” (A. M. 12:20-23) Idan mu ƙwararru ne wajen ba da jawabi ko kuwa wajen koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki fa? Muna bukatar mu yi godiya ga Allah domin abubuwan da ya sa mu yi.—1 Kor. 4:6, 7; Yaƙ. 4:6.
Ka Kasance Mai Gaba Gaɗi da Kuma Ƙarfi
11, 12. Ta yaya ne labarin Anuhu ya nuna cewa Jehobah yana sa bayinsa su kasance da gaba gaɗi da kuma ƙarfi?
11 Idan muka bi hanyoyin Jehobah cikin tawali’u zai ba mu gaba gaɗi da ƙarfi. (K. Sha 31:6-8, 23) Anuhu, wanda shi ne mutum na bakwai a salsalar Adamu, ya bi Allah da gaba gaɗi ta wajen biɗar tafarki mai kyau a cikin mugayen tsaransa. (Far. 5:21-24) Jehobah ya ƙarfafa Anuhu don ya faɗi saƙo mai iko ga mutanen domin kalamai da halayensu na banza. (Ka karanta Yahuza 14, 15.) Kana da gaba gaɗin da ake bukata don ka sanar da hukuncin da Allah zai yi?
12 Jehobah ya hukunta mugaye a Rigyawar da aka yi a zamanin Nuhu. Duk da haka, annabcin da Anuhu ya yi yana da ban ƙarfafa, domin nan ba da daɗewa ba, Allah zai sa mala’ikunsa su halaka mutanen da ba sa tsoronsa a zamaninmu. (R. Yoh. 16:14-16; 19:11-16) Ta wajen amsa addu’o’inmu, Jehobah yana ƙarfafa mu mu sanar da saƙonsa na hukuncin da zai yi da kuma albarkar da za a samu a ƙarƙashin sarautar Mulkinsa.
13. Me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Allah zai ba mu gaba gaɗi da ƙarfin da muke bukata don mu jimre matsaloli?
13 Muna bukatar gaba gaɗi da kuma ƙarfi daga Allah don mu jimre matsaloli. Sa’ad da Isuwa ya auri mata Hittiyawa guda biyu, matan sun “zama abin ɓāta rai ga [iyayensa] Ishaƙu da Rifkatu.” Rifkatu ta ce: “Na gaji da raina saboda ’yan mata na Heth: idan fa [ɗanmu] Yaƙubu ya yi aure cikin ’yan mata na Heth, irin waɗannan, ’yan mata na wannan ƙasa, me raina ya daɗa mini?” (Far. 26:34, 35; 27:46) Ishaƙu ya ɗauki mataki kuma ya tura Yaƙubu ya nemo matar da zai aura a cikin masu bauta wa Jehobah. Ko da yake Ishaƙu da Rifkatu sun kasa canja abin da Isuwa ya yi, Allah ya ba su hikima, gaba gaɗi, da kuma ƙarfi don su kasance da aminci. Idan muka yi addu’a don samun taimako, Jehobah zai taimaka mana.—Zab. 118:5.
14. Ta yaya ne ’yar ƙaramar yarinya ’yar Isra’ila ta nuna gaba gaɗi?
14 Ƙarnuka bayan haka, wata ’yar ƙaramar yarinya ’yar Isra’ila wadda sojoji suka kama, ta zama baiwa a gidan Na’aman shugaban sojojin Suriya, wanda kuturu ne. Sa’ad da ta ji game da mu’ujizan da Allah ya yi ta hanyar annabi Iliya, da gaba gaɗi yarinyar ta gaya wa matar Na’aman cewa: ‘Da ubangijina zai je Isra’ila, da annabin Jehobah ya warkar da kuturtarsa.’ Na’aman ya je Isra’ila, kuma an warkar da shi ta hanyar mu’ujiza. (2 Sar. 5:1-3) Wannan yarinyar misali ce mai kyau ga yara waɗanda suka dogara ga Jehobah don samun gaba gaɗin yin wa’azi ga malamansu, abokan makarantarsu, da kuma sauran mutane.
15. Wane mataki ne Obadiah mai kula da gidan Ahab ya ɗauka da gaba gaɗi?
15 Gaba gaɗin da Allah yake bayarwa yana taimaka mana mu jimre tsanantawa. Yi la’akari da Obadiah wanda ya rayu a zamanin annabi Iliya kuma shi ne ke kula da gidan Sarki Ahab. Sa’ad da Jezebel ta ba da umurni cewa a yanka annabawan Allah, Obadiah ya ɓoye annabawa ɗari “a cikin kogon dutse, [su] hamsin hamsin.” (1 Sar. 18:13; 19:18) Za ka iya taimaka wa ’yan’uwa Kiristoci da ake tsanantawa da gaba gaɗi kamar yadda Obadiah ya taimaka wa annabawan Jehobah?
16, 17. Menene Aristarkus da Gayus suka yi sa’ad da aka tsananta musu?
16 Idan aka tsananta mana, ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana. (Rom. 8:35-39) A filin wasan da ke Afisa, abokan aikin Bulus, wato, Aristarkus da Gayus sun fuskanci mugun taron mutane dubbai. Dimitriyus maƙerin azurfa ne ya ta da hargitsin. Shi da sauran maƙera ne suka gina gidan azurfa inda ake zuwa a bauta wa alla Artemis, kuma kasuwar da ke kawo masu riba tana son ta rushe domin wa’azin da Bulus ya yi ya sa yawancin mazauna birnin sun daina bauta wa gunki. Wannan muguwar taron ta ja Aristarkus da Gayus zuwa wannan gidan kallon kuma suka ci gaba da ɗaga murya suna cewa: “Artemis ta Afisawa mai-girma ce.” Aristarkus da Gayus wataƙila suna tsammanin cewa za su mutu, amma marubucin garin ya kwantar da hankalin taron.—A. M. 19:23-41.
17 Idan kai ne ka fuskanci irin wannan matsalar, da za ka so ka nemi rayuwa mai sauƙi? Babu abin da ya nuna cewa Aristarkus da Gayus sun yi sanyin gwiwa. Domin shi ɗan Tassalunika ne, Aristarkus ya san cewa yin bishara za ta iya jawo tsanantawa. Kafin wannan lokacin, an yi tashin hankali sa’ad da Bulus ya yi wa’azi a Tassalunika. (A. M. 17:5; 20:4) Domin Aristarkus da Gayus sun bi hanyoyin Jehobah, Allah ya ba su ƙarfi da gaba gaɗi don su jimre tsanantawa.
Ka Mai da Hankali ga Bukatun Wasu
18. Ta yaya ne Biriska da Akila suka “lura da” bukatun wasu?
18 Ko da ana tsananta mana a yanzu ko a’a, muna bukatar mu mai da hankali ga bukatun ’yan’uwanmu Kiristoci. Biriska da Akila sun “lura da” bukatun wasu. (Ka karanta Filibiyawa 2:4.) Waɗannan ma’auratan masu kirki wataƙila sun ba Bulus wurin kwana a Afisa, inda Dimitriyus mai ƙera azurfa ya ta da hargitsi. Wataƙila wannan abin ne ya motsa Akila da Biriska su “miƙa wuyansu” domin Bulus. (Rom. 16:3, 4; 2 Kor. 1:8) A yau, nuna damuwa domin ’yan’uwanmu da ake tsananta wa yana sa mu “zama masu-azanci fa kamar macizai.” (Mat. 10:16-18) Muna ci gaba da yin aikinmu da hankali kuma ba ma cin amanar ’yan’uwanmu ta wajen ba da sunansu ko kuma mu ba da wasu bayanai ga masu tsanantawa.
19. Waɗanne abubuwa masu kyau ne Dokas ta yi wa mutane?
19 Mai da hankali ga bukatun wasu yana da fasaloli dabam dabam. Wasu Kiristoci suna da bukatu, kuma wataƙila muna iya biyan waɗannan bukatun. (Afis. 4:28; Yaƙ. 2:14-17) A ikilisiyar da ke birnin Yafa a ƙarni na farko, akwai wata mata mai kirki mai suna Dokas. (Ka karanta Ayukan Manzanni 9:36-42.) Dokas tana cike “da ayyukan nagarta da bayebayen” da suka haɗa da yi wa gwauraye mabukata tufafi. Sa’ad da ta mutu a shekara ta 36 A.Z., hakan ya sa gwaurayen baƙin ciki ƙwarai da gaske. Allah ya yi amfani da manzo Bitrus ya ta da Dokas daga matattu, kuma wataƙila ta ci gaba da yin wa’azi da kuma yin nagarta ga mutane har sa’ad da ta sake mutuwa. Muna farin ciki cewa muna da irin waɗannan mata marar son kai a cikinmu a yau!
20, 21. (a) Ta yaya ƙarfafa yake da nasaba da mai da hankali ga bukatun wasu? (b) Menene za ka iya yi don ka zama mai ƙarfafawa?
20 Muna damuwa da bukatun wasu ta wajen ƙarfafa su. (Rom. 1:11, 12) Sila wanda abokin aikin Bulus ne ya ƙarfafa shi sosai. Bayan an yanke shawara game da batun kaciya a kusan shekara ta 49 A.Z., hukumar mulki da ke Urushalima ta aika wakilai su kai wasiƙu ga masu bi da ke wurare dabam dabam. Sila, Yahuda, Barnaba, da Bulus ne suka kai wasiƙar zuwa Antakiya. A nan ne Sila da Yahuda “suka yi ma yan-uwa galgaɗi da zantattuka dayawa, suka ƙarfafa su.”—A. M. 15:32.
21 Bayan haka, an jefa Bulus da Sila a cikin kurkuku a Filibbi amma sun sami tsira domin girgizar ƙasar da aka yi. Babu shakka sun yi farin cikin ganin cewa mai tsaron kurkuku da iyalinsa da suka yi wa wa’azi sun zama masu bi! Kafin su bar wannan birnin, Sila da Bulus sun ƙarfafa ’yan’uwan. (A. M. 16:12, 40) Kamar Bulus da Sila ka yi ƙoƙari ka ƙarfafa mutane ta kalaminka, jawabanka, da kuma yin himma a wa’azin fage. Kuma sa’ad da kuke da “maganar gargaɗi” kada ku fasa ‘faɗansa.’—A. M. 13:15.
Ka Ci Gaba da Bin Tafarkun Jehobah
22, 23. Ta yaya ainihi za ma amfana daga labaran Littafi Mai Tsarki?
22 Ya kamata mu yi godiya don labaran rayuwa na gaske da aka rubuta a Kalmar Jehobah, “Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Kor. 1:3) Idan muna son mu amfana daga waɗannan labaran, dole ne mu yi amfani da darussan Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu kuma mu bar ruhu mai tsarki na Allah ya yi mana ja-gora.—Gal. 5:22-25.
23 Yin bimbini a kan labaran Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu nuna halaye na ibada. Zai ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, wanda ke ba mu “hikima, da ilimi, da farinciki.” (M. Wa. 2:26) Mu kuma za mu faranta wa Allah rai. (Mis. 27:11) Bari mu ƙuduri aniyar yin hakan ta wajen ci gaba da bin tafarkun Jehobah.
Mecece Amsarka?
• Ta yaya za ka nuna kai mai gaskiya ne?
• Me ya sa ya kamata mu kasance “masu tawali’u?
• Ta yaya ne labaran Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu kasance masu gaba gaɗi?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu mai da hankali ga bukatun wasu?
[Hoto a shafi na 8]
Jephthat da ’yarsa masu yin gaskiya sun cika alkawarinsu, ko da yake yin hakan yana da wuya
[Hoto a shafi na 10]
Matasa, me kuka koya daga yarinya ’yar Isra’ila?
[Hoto a shafi na 11]
Ta yaya Dokas ta biya bukatun Kiristoci masu bi?