Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
Mene Ne Armageddon?
▪ Ga mutane da yawa, kalmar nan “Armageddon” tana sa su yi tunanin kisan ƙare dangi, wato, yin amfani da makaman nukiliya a yaƙi, bala’i a wurare da yawa, ko ma “bala’i na mahalli” da ƙaruwar zafi zai haddasa. Cikin waɗannan bayanai da ke sama, babu wanda ya zo daidai da na Littafi Mai Tsarki. Mene ne Littafi Mai Tsarki yake nufi da Armageddon?
Kalmar nan “Armageddon,” ta bayyana ne a Ru’ya ta Yohanna cikin Littafi Mai Tsarki. Tana nufin wani yaƙi na musamman, “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka,” inda “sarakunan dukan duniya” za su haɗa kai don yin yaƙi na ƙarshe da Allah. An ambata irin wannan yaƙin a nassosi da dama.—Ru’ya ta Yohanna 16:14-16; Ezekiyel 38:22, 23; Joel 3:12-14; Luka 21:34, 35; 2 Bitrus 3:11, 12.
Mene ne wannan yaƙin ya ƙunsa? A alamance, littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce: “Sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru su yaƙi wanda ke kan dokin, da kuma runduna tasa.” Wannan “wanda ke kan doki” shi ne ɗan Allah, Yesu Kristi, wanda Allah ya naɗa domin ya ja-gorance rundunan mayaƙa mala’iku zuwa nasara a kan magabtan Allah. (Ru’ya ta Yohanna 19:11-16, 19-21) Irmiya 25:33 ta bayyana yawan miyagu da za a halaka: “Za a ga kisassun Ubangiji tun daga wannan iyakar duniya zuwa wannan iyaka.”
Me ya sa Armageddon take da muhimmanci? Al’ummai sun ƙi amincewa da ikon mallakar Allah, a maimakon haka, suna ɗaukaka kansu. (Zabura 24:1) An kwatanta kangarewarsu a littafin Zabura 2:2: “Sarakunan duniya sun tashi tsaye, mahukunta kuma suna ƙulla shawara gāba da Ubangiji da Masihansa.”
’Yan tawayen nan suna kama ne da mazauna gidan wani waɗanda suke da’awar cewa su ke da ginin kuma suna lalata gidan. A yau, al’ummai suna ɓata duniya kuma suna gurɓata mahallinta. Kalmar Allah ta annabta wannan mummunar yanayi sa’ad da ta ce: “Al’ummai kuma suka yi fushi, fushin [Allah] kuma ya zo.” Saboda haka, Allah zai “hallaka waɗanda ke hallaka duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 11:18) Allah ya ƙudura cewa zai yi amfani da Armageddon wajen magance wannan batu na wanda yake da izinin yin sarauta bisa ’yan Adam.—Zabura 83:18.
A yaushe ne Armageddon zai auku? Ɗan Allah ya bayyana sarai: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” (Matta 24:36) Ko da yake hakan gaskiya ne, sa’ad da yake magana game da Armageddon, Sarki Jarumi Yesu Kristi ya ƙara wannan gargaɗi: “Duba, kamar ɓarawo ni ke zuwa. Mai-albarka ne shi wanda ya ke tsaro.” (Ru’ya ta Yohanna 16:15) Saboda haka, an danganta wannan yaƙi na dukan duniya da bayyanuwar Kristi wanda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa yana faruwa a yanzu.
Armageddon zai halaka gagararrun miyagu kuma “taro mai-girma” za su tsira. (Ru’ya ta Yohanna 7:9-14) Za su ga cikar waɗannan kalmomin: “Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: Hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:10, 11.
[Bayanin da ke shafi na 32]
“Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama”