“Taro mai girma” daga dukan ƙasashe za su tsira a yaƙin Armageddon
Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Mene ne Armageddon?
Wasu sun yi imani cewa . . .
Lokaci ne da za a halaka duniya da makaman nukiliya ko kuma a gurɓata mahalli. Mene ne ra’ayinka?
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
Armageddon yana nufin “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka,” wato yaƙin da zai yi da masu yin mugunta.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
- Allah zai yi yaƙin Armageddon ne ba don ya halaka duniya ba, amma don ya cece ta daga waɗanda suke son su halaka ta.—Ru’ya ta Yohanna 11:18. 
- Yaƙin Armageddon zai kawo ƙarshen dukan yaƙoƙi.—Zabura 46:8, 9. 
Za mu iya tsira daga yaƙin Armageddon?
Me za ka ce?
- E 
- A’a 
- Wataƙila 
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
“Taro mai girma” daga dukan ƙasashe za su tsira daga “babban tsanani,” wanda zai ƙare a yaƙin Armagedon.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14.
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
- Allah yana son dukan mutane su tsira daga yaƙin Armageddon. Kafin ya halaka mutane, sai ya daɗe yana musu gargaɗi.—Ezekiyel 18:32. 
- Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da za mu yi don mu tsira a Armageddon.—Zafaniya 2:3.