Kana Barin Jehobah Ya Zama Rabonka Kuwa?
“Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.”—MAT. 6:33.
1, 2. (a) Su waye ne “Isra’ila na Allah” da aka ambata a Galatiyawa 6:16? (b) A cikin Matta 19:28 su waye ne “ƙabilan goma sha biyu na Isra’ila” suke wakilta?
MENE NE kake tunawa sa’ad da ka karanta sunan nan Isra’ila a cikin Littafi Mai Tsarki? Shin kana tunanin Yakubu, ɗan Ishaƙu, wanda aka canja sunansa zuwa Isra’ila? Ko kuwa kana tunanin ’ya’yansa, al’ummar Isra’ila ta dā? Littafi Mai Tsarki ya kuma yi magana game da Isra’ila ta ruhaniya, ko kuma “Isra’ila na Allah.” Su mutane 144,000 ne waɗanda aka shafa da ruhu mai tsarki su zama sarakuna da firistoci a sama. (Gal. 6:16; R. Yoh. 7:4; 21:12) Amma ku yi la’akari da ƙabilu 12 na Isra’ila da aka ambata a hanya ta musamman a Matta 19:28.
2 Yesu ya ce: “Cikin sabonta sa’anda Ɗan mutum za ya zauna bisa kursiyin darajarsa, ku kuma za ku zauna bisa kursiyi goma sha biyu, kuna mallakar ƙabilan goma sha biyu na Isra’ila.” A cikin wannan ayar, “ƙabilan goma sha biyu na Isra’ila” sune waɗanda almajiran Yesu shafaffu za su yi wa shari’a kuma su ne za su yi rayuwa har abada cikin Aljanna a duniya. Mutane 144,000 za su yi musu hidima a matsayin alƙalai da firistoci.
3, 4. Wane misali mai kyau ne shafaffu masu amince suka kafa?
3 Kamar firistoci da Lawiyawa na dā, shafaffu a yau suna ɗaukan hidimarsu ga Jehobah da tamani sosai. (Lit. Lis. 18:20) Shafaffu ba sa tsammanin samun wasu yankuna ko wuri a duniya. Maimakon hakan, Ru’ya ta Yohanna 4:10, 11 ya nuna cewa za su ci gaba da hidimarsu ga Jehobah a sama, inda za su zama sarakuna da firistoci tare da Yesu Kristi.—Ezek. 44:28.
4 Sa’ad da suke a duniya, shafaffu suna rayuwa a hanyar da ke nuna cewa Jehobah ne rabonsu. Gatarsu na bauta wa Allah ne ya fi muhimmanci a gare su. Sun ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Kristi kuma sun ci gaba da bin sa, da hakan suna ‘daɗa bada anniya garin su tabbatar da kiransu da zaɓensu.’ (2 Bit. 1:10) Yanayinsu da iyawarsu ya bambanta. Duk da haka, ba sa amfani da kasawarsu a matsayin hujja don yin abu kaɗan kawai a hidimarsu ga Allah. Akasin haka, suna sa hidimar Allah farko a rayuwarsu kuma suna yin iya ƙoƙarinsu. Kuma suna kafa wa waɗanda suke da begen zama a duniya misali mai kyau.
5. Ta yaya Jehobah zai zama rabon dukan Kiristoci, kuma me ya sa yin hakan zai yi wuya?
5 Ko muna da begen zuwa sama ko kuma na zama a duniya, dole ne ‘mu yi musun kanmu, mu ɗauki gungumenmu na azaba, mu bi Kristi.’ (Mat. 16:24) Miliyoyin mutane da suke sauraron yin rayuwa a cikin Aljanna suna bauta wa Allah kuma suna bin Kristi hakan. Ba sa yin kaɗan kawai a cikin hidimar Allah idan sun san cewa za su iya yin fiye da hakan. Mutane da yawa sun sauƙaƙa rayuwarsu kuma sun zama majagaba. Wasu sun yi ƙoƙari su yi hidimar majagaba wasu watanni a kowacce shekara. Duk da haka, waɗanda ba su iya yin hidimar majagaba ba suna ƙwazo sosai a hidima. Irin waɗannan suna kama da Maryamu, wadda ta zuba wa Yesu man ƙanshi a kā. Ya ce: ‘Ta yi mini aikin alheri. . . . Ta yi abin da ta iya.’ (Mar. 14:6-8) Yin iya ƙoƙarinmu ba zai kasance da sauƙi ba, don muna zama a duniya da Shaiɗan ke mallakarta. Duk da haka, muna bukatar mu yi aiki tuƙuru kuma mu dogara ga Jehobah. Ka yi la’akari da yadda za mu yi hakan a hanyoyi huɗu.
Ka Fara Biɗan Mulkin Allah
6. (a) Ta yaya mutane a duniya suke nuna cewa rabonsu a wannan rayuwa ne kawai? (b) Me ya sa ya fi kyau mu yi koyi da Dauda?
6 Yesu ya koya wa mabiyansa su fara biɗan Mulkin da adalcin Allah. Mutanen duniya sukan fara biɗan abubuwa na kansu a matsayin “mutane na duniya waɗanda rabonsu a cikin wannan rai ya ke.” (Karanta Zabura 17:1, 13-15.) Da yake ba sa damuwa game da Jehobah, mutane da yawa suna damuwa game da jin daɗin rayuwa da samun iyali da kuma bar wa yaransu gado. Rabonsu yana cikin wannan rayuwar kawai. A wata sassa kuma, Dauda yana son ya yi “nagarin suna” yadda ɗansa daga baya ya ce kowa ya yi. (M. Wa. 7:1) Kamar Asaph, Dauda ya san cewa zama abokin Jehobah shi ne ya fi muhimmanci a rayuwa. Hakan ya sa Dauda farin ciki. A zamaninmu, Kiristoci da yawa sun nuna cewa hidimarsu ga Jehobah ta fi muhimmanci a gare su fiye da aikinsu na karɓan albashi.
7. Wace albarka ce wani ɗan’uwa ya samu don ya saka Mulkin da farko a rayuwarsa?
7 Ka yi la’akari da Jean-Claude da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Shi dattijo ne mai aure da kuma yara uku. Yana da wuya a samu aiki a wannan ƙasar, kuma yawancin mutane za su yi kome don su ci gaba da yin aikinsu. Wata rana, manajan wurin aikinsu ya gaya wa Jean-Claude cewa ya soma aiki da dare. Za a soma aiki ƙarfe shida da rabi da yamma, kwanaki bakwai a mako. Jean-Claude ya gaya masa cewa ban da bukatun zahiri na iyalinsa, zai biya bukatunsu na ruhaniya. Ya kuma faɗa cewa yana da hakkin taimaka wa ikilisiyar. Manajan ya gaya masa: “Idan ka yi sa’ar samun aiki, dole ne ka manta da kome, har da matarka da yaranka da kuma matsalolinka. Dole ne ka mai da hankali sosai ga aikinka. Ka zaɓi tsakanin addininka ko kuma aikinka.” Da mene ne za ka yi? Jean-Claude ya san cewa idan ya yi hasarar aikinsa, Allah zai kula da shi. Zai ci gaba da samun aiki da yawa da zai yi a hidimar Allah, kuma Jehobah zai taimaka wajen kula da bukatun iyalinsa. Sai ya tafi taron ikilisiya na tsakiyar mako. Bayan hakan ya shirya ya tafi aiki ko da yake bai san ko har ila zai ci gaba da aikinsa ba. Ba da daɗewa ba aka kira sa a waya cewa an kori manajan daga aiki, amma ɗan’uwanmu ya ci gaba da yin aikinsa.
8, 9. A wane azanci ne za mu yi koyi da firistoci da Lawiyawa wajen sa Jehobah ya zama rabonmu?
8 Mai yiwuwa wasu cikinku sun taɓa kasancewa cikin irin wannan yanayin. Wataƙila ka damu game da yadda za ka kula da iyalinka idan ka yi hasarar aikinka. (1 Tim. 5:8) Amma ko idan hakan ya faru maka ko a’a, daga abin da ka shaida a rayuwa ka san cewa Allah ba zai taɓa yasar da waɗanda suka mai da shi rabonsu kuma suka sa hidimarsa farko a rayuwarsu ba. Sa’ad da Yesu ya gaya wa almajiransa su fara biɗan mulkin, ya tabbatar musu cewa Allah zai daɗa musu “waɗannan abubuwa duka” kamar su abinci da abin sha da tufafin da za su saka.—Mat. 6:33.
9 Ka yi tunanin Lawiyawa, waɗanda ba su samu gadon ƙasa ba. Tun da yake bauta mai tsarki ne ainihin abin da ya fi muhimmanci a gare su, za su dogara ga Jehobah don ya biya bukatunsu, hakan ya sa ya gaya musu: ‘Ni ne rabonku.’ (Lit. Lis. 18:20) Ko da yake ba ma hidima a haikali na zahiri kamar yadda firistoci da Lawiyawa suka yi, muna iya yin koyi da halinsu na kasancewa da gaba gaɗi cewa Jehobah zai biya bukatunmu. Yayin da ƙarshe yake kusatowa, ya fi kasancewa da muhimmanci mu dogara ga Allah ya kula da mu.—R. Yoh. 13:17.
Ka Fara Biɗan Adalcin Allah
10, 11. Ta yaya wasu suka dogara ga Jehobah sa’ad da suke zaɓan aiki? Ka ba da misali.
10 Yesu ya gaya wa almajiransa su ‘fara biɗan adalcin Allah.’ (Mat. 6:33) Wannan yana nufin mu sa ra’ayin Jehobah game da abin da ke daidai da abin da ba daidai ba farko, ba na ’yan Adam ba. (Karanta Ishaya 55:8, 9.) A dā, wasu mutane suna nome ko kuma sayar da taba sigari, suna koya wa mutane yaƙi ko kuma su ƙera ko sayar da makaman yaƙin. Amma bayan sun koyi gaskiya, yawancinsu sun canja aikinsu kuma sun cancanci yin baftisma.—Isha. 2:4; 2 Kor. 7:1; Gal. 5:14.
11 Muna da misalin Andrew. Sa’ad da shi da matarsa suka koyi game da Jehobah, sun tsai da shawara su bauta masa. Andrew yana son aikinsa sosai amma ya bar aikin. Me ya sa? Domin ƙungiyar da yake wa aiki tana saka hannu a yaƙi, amma yana son ya yi abin da Jehobah ya ce daidai ne. Sa’ad da Andrew ya bar aikinsa, yana da yara biyu da kuɗin da zai kashe ’yan watanni kawai. A ra’ayin ’yan Adam, kamar dai ba shi da ‘gado.’ Ya nemi aiki yana dogara ga Allah. Yanzu idan suka tuna da wannan lokacin, shi da iyalinsa sun tabbata cewa hannun Ubangiji bai gajarta ba. (Isha. 59:1) Ta wajen yin rayuwa mai sauƙi, Andrew da matarsa suna da gatar shiga hidima ta cikakken lokaci. Ya ce: “Da akwai wasu lokatai da suke damuwa game da kuɗi da gidan da za su zauna da lafiyarsu da kuma cewa sun soma tsufa. Amma, Jehobah yana tare da mu a kowanne lokaci. . . . Muna iya faɗa ba tare da wata shakka ba cewa, bauta wa Jehobah tana kawo albarka da kuma daraja mafi girma da kowane ɗan Adam zai samu.”a—M. Wa. 12:13.
12. Wane hali ne muke bukata don mu fara biɗan adalcin Allah? Ka ba da misalai na yankinku.
12 Yesu ya gaya wa almajiransa: “Idan kuna da bangaskiya kwatancin ƙwayar mustard, sai ku ce ma wannan dutse, ka kawu daganan ka koma can; sai shi kawu; kuma babu abin da ba za shi yiwu gareku ba.” (Mat. 17:20) Za ka iya sa mizanan Allah a farko ko da yin hakan zai jawo maka matsaloli? Idan kana shakka ko za ka iya yin hakan, ka tattauna da wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Babu shakka, labaransu game da yadda Jehobah ya taimaka musu zai sa bangaskiyarka ta daɗa kasancewa da ƙarfi.
Ka Nuna Godiya ga Tanadin Jehobah
13. Idan mun yi ƙwazo a hidimar Jehobah, mene ne za mu tabbata cewa za mu samu?
13 Idan ka daraja gatan da kake da shi na bauta wa Jehobah, za ka iya kasance da tabbaci cewa zai ba ka kome da kake bukata, kamar yadda ya yi wa Lawiyawa. Ka tuna labarin Dauda. Ko da yake yana ɓoye cikin kogon dutse, yana da tabbaci cewa Allah zai taimake shi. Mu ma muna iya dogara ga Jehobah ko a lokacin da kamar babu wanda zai taimake mu. Ka tuna cewa sa’ad da Asaph ya shiga “wuri mai-tsarki na Allah” ya samu fahimi game da abin da yake damunsa. (Zab. 73:17) Haka nan ma, muna bukata mu dogara ga Jehobah don ya ba mu abin da muke bukata don mu ci gaba da abuta da shi. Da hakan, muna nuna godiya ga gatarmu na bauta wa Allah ko yaya yanayinmu. Za mu bar Jehobah ya zama rabonmu.
14, 15. Yaya ya kamata mu aikata sa’ad da aka yi gyara ga yadda muka fahimci wasu Nassosi, kuma me ya sa?
14 Kana dogara ga Jehobah sa’ad da ya taimaka mana mu fahimci “zurfafa na Allah” da suke cikin Littafi Mai Tsarki? (1 Kor. 2:10-13) Manzo Bitrus misali ne mai kyau na wanda ya yi hakan. Yesu ya gaya wa Yahudawa: “In ba ku ci naman Ɗan Mutum ba, ku sha jininsa kuma, ba ku da rai a cikinku ba.” Da yake ba su fahimci ma’anar kalamin ba, almajirai da yawa suka ce: “Wannan batu da wuya yake; wanene ya iya jinsa?” Sai “suka ja da baya.” Amma Bitrus ya ce: “Ubangiji, wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada.”—Yoh. 6:53, 60, 66, 68.
15 Bitrus bai fahimci abin da Yesu ya faɗa game da cin namansa da shan jininsa sosai ba. Amma manzon ya dogara ga Allah don ya fahimci gaskiya. Sa’ad da aka yi gyara a yadda muka fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki a yau, kana yin ƙoƙari ka fahimci dalilan da suka sa aka yi canjin? (Mis. 4:18) Mutanen Biriya na ƙarni na farko sun karɓi maganar “da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowacce rana.” (A. M. 17:11) Yin koyi da su zai sa ka nuna godiya don gatarka na bauta wa Jehobah kuma sa ya zama rabonka.
Yin Aure Cikin Ubangiji Kaɗai
16. Ta yaya Allah zai zama rabonmu game da umurni da ke 1 Korantiyawa 7:39?
16 Wani ɓangare da Kiristoci suke bukatar su riƙa yin biyayya ga Allah shi ne a bin mizanan Littafi Mai Tsarki na yin aure “cikin Ubangiji” kaɗai. (1 Kor. 7:39) Mutane da yawa sun zaɓa su kasance marar aure maimakon su ƙi bin wannan gargaɗin Allah. Allah yana kula da waɗanda suka yi hakan. Mene ne Dauda ya yi sa’ad da ya kaɗaita kamar ba shi da mai taimakonsa? Ya ce: “Ina zuba ƙarata a gabansa [Allah]; Ina nuna masa wahalata. Lokacin da ruhuna ya yi suwu a cikina.” (Zab. 142:1-3) Wataƙila annabi Irmiya wanda ya bauta wa Allah da aminci shekaru da yawa a matsayin marar aure ya ji hakan.
17. Mene ne wata ’yar’uwa marar aure take yi sa’ad da ta kaɗaita?
17 Wata ’yar’uwa a ƙasar Amirka ta ce: “Ban taɓa tsai da shawara cewa ba zan yi aure ba. Zan yi aure sa’ad da na samu wanda ya dace. Mahaifiyata da ba Mashaidiya ba ce tana so na auri kowa da ya ce yana so ya aure ni. Na tambaye ta ko tana son ta ɗauki alhaki idan auren ba na kirki ba ne. Da shigewar lokaci, ta ga cewa ina da aiki mai kyau, ina kula da kaina kuma ina farin ciki. Sai ta daina damu na.”’Yar’uwar takan ji ta kaɗaita a wasu lokatai. Ta ce: “Ina yin ƙoƙari na sa Jehobah ya zama wanda nake dogara ga. Bai taɓa yasar da ni ba.” Mene ne ya taimaka mata ta dogara ga Jehobah? Ta ce: “Addu’a tana taimaka mini na ga cewa Allah yana nan kuma yana tare da ni. Maɗaukaki na sararin samaniya yana saurarawa, me ya sa ba zan ji an ɗaukaka ni kuma na yi farin ciki ba?” Ta yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa “bayarwa ta fi karɓa albarka.” Saboda haka, tana ƙoƙari ta taimaka wa mutane ba tare da yin tsammanin cewa za su biya ta ba. Ta ci gaba: “Sa’ad da nake tunani, ‘Mene ne zan iya yi don na taimaki wannan mutum?’ Hakan na sa ni farin ciki.” (A. M. 20:35) Jehobah ne rabonta, kuma tana farin ciki a hidimarsa.
18. Ta yaya Jehobah zai zama rabonka?
18 Kowanne yanayi ne ka samu kanka a ciki, kana iya barin Allah ya zama rabonka? Idan ka yi hakan, za ka kasance cikin mutane masu farin ciki. (2 Kor. 6:16, 17) Sa’an nan Jehobah zai zama rabonka, kamar yadda wasu bayin Allah suka yi a dā. (Karanta Kubawar Shari’a 32:9, 10.) Kamar yadda Allah ya zama rabon Isra’ila maimakon sauran al’ummai da ke kewaye da su, zai iya zaɓa ya zama rabonka kuma ya kula da kai cikin ƙauna.—Zab. 17:8.
[Hasiya]
a Ka duba Awake! na Nuwamba 2009, shafuffuka na 12-14.
Yaya Za Ka Amsa?
Ta yaya za ka sa Jehobah ya zama rabonka
• ta wajen fara biɗan Mulkin Allah da adalcinsa?
• ta wajen nuna godiya don abinci na ruhaniya?
• ta wajen yin biyayya ga umurnin Allah na yin aure cikin Ubangiji kaɗai?
[Bayanin da ke shafi na 13]
Jehobah yana zama rabonmu sa’ad da muka sa hidimarsa ta fi kasancewa da muhimmanci a gare mu
[Hoto a shafi na 15]
Misalin Irmiya yana da ban ƙarfafa