Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 9/15 pp. 7-11
  • Jehobah Ne Rabona

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ne Rabona
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ya Kula da Lawiyawa
  • Jehobah Ya Kasance Rabo ga Lawiyawa Ɗai-Ɗai
  • Jehobah Zai Iya Kasance Rabo ga Wasu
  • Kana Barin Jehobah Ya Zama Rabonka Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Ni Ne . . . Gādonka”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Darussa Daga Addu’a Mai Ma’ana Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Hidimar da Lawiyawa Suke Yi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 9/15 pp. 7-11

Jehobah Ne Rabona

“Ni ne rabonka da gadonka a cikin ’ya’yan Isra’ila.” —LIT. LIS. 18:20.

1, 2. (a) Mene ne yanayin Lawiyawa game da samun gadon ƙasa? (b) Wane tabbaci ne Jehobah ya ba Lawiyawa?

BAYAN da Isra’ilawa suka ci wurare da yawa na Ƙasar Alkawari, Joshua ya mai da hankali ga raba ƙasar bisa ga rabonsu. Ya yi aiki tare da Babban Firist Eleazar da kuma shugabannin ƙabilun. (Lit. Lis. 34:13-29) Lawiyawa ba za su samu gādon ƙasa ba kamar yadda sauran ƙabilu suka samu. (Josh. 14:1-5) Me ya sa Lawiyawa ba su da yankin ƙabilarsu ko kuma rabo a Ƙasar Alkawari? Shin an manta da su ne?

2 Mun samu amsar a cikin abin da Jehobah ya gaya wa Lawiyawa. Sa’ad da yake nuna cewa ba a yasar da su ba, Jehobah ya gaya musu: “Ni ne rabonka da gadonka a cikin ’ya’yan Isra’ila.” (Lit. Lis. 18:20) Wannan furuci: “Ni ne rabonka” tabbaci ne mai ƙarfi! Yaya za ka ji idan Jehobah ya gaya maka hakan? Da farko kana iya cewa, ‘Na cancanci samun irin wannan tabbaci daga wurin Maɗaukaki kuwa?’ Kana kuma iya yin tunani, ‘Jehobah zai iya zama rabon wani Kirista ajizi a yau kuwa?’ Waɗannan tambayoyi sun shafe ka da kuma waɗanda kake ƙauna. Saboda haka, bari mu bincika ma’anar wannan kalami da Allah ya yi? Hakan zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah zai iya zama rabon Kiristoci a yau. Yana iya zama rabonka, ko idan kana da begen zama a sama ko kuma a cikin aljanna na duniya.

Jehobah Ya Kula da Lawiyawa

3. Me ya sa Allah ya ɗauki Lawiyawa su riƙa yi masa hidima?

3 Shugabannin iyalan da ke cikinsu suna hidima a matsayin firist kafin Jehobah ya ba Isra’ilawa Dokar. Sa’ad da Allah ya yi tanadin Dokar, ya shirya firistoci na cikakken lokaci da kuma mataimakinsu daga ƙabilar Lawiyawa. Yaya hakan ya faru? Sa’ad da Allah ya halaka ’yan fari na ƙasar Masar, ya tsarkake ’ya’yan fari na Isra’ila, ya ware su kuma a matsayin mutanensa. Sa’annan Allah ya yi wannan gyara na musamman: “Na ɗauki Leviyawa . . . maimakon dukan abin da ya fara buɗe ciki daga cikin ’ya’yan Isra’ila.” An yi fansa don a daidaita su tun da yake ƙidayar da aka yi ta nuna cewa ’ya’yan fari na Isra’ilawa sun fi adadin Lawiyawa. (Lit. Lis. 3:11-13, 41, 46, 47) Ta hakan, Lawiyawa za su iya yin hidimarsu na bauta wa Allah na Isra’ila.

4, 5. (a) Me yake nufi cewa Allah ya zama rabon Lawiyawa? (b) Ta yaya Allah ya kula da Lawiyawa?

4 Wane aiki ne Lawiyawa za su yi? Jehobah ya ce zai zama rabonsu a azanci na cewa maimakon su karɓi gadon ƙasa, an ba su gatar yin hidima mai tamani. Zaman “[Firistoci] na Ubangiji” ne gadonsu. (Josh. 18:7) Abin da Littafin Lissafi 18:20 ya faɗa ya nuna cewa wannan bai sa su talauta ba. (Karanta Littafin Lissafi 18:19, 21, 24.) Za a ba Lawiyawa ‘dukan zakka cikin Isra’ila gado, maimakon hidimarsu da su ke yi.’ Za su karɓi kashi goma na amfanin gonakin Isra’ila da kuma ƙarin dabbobi da ake samu. Haka kuma, Lawiyawa za su ba da kashi goma na abubuwan da suke karɓa, “mafi-kyau daga ciki” don su tallafa wa firistoci.a (Lit. Lis. 18:25-29) Ana ba firistoci “dukan hadayu na cirawa na kaya masu-tsarki” da ’ya’yan Isra’ila suka kawo wa Allah a wurin bautarsa. Saboda haka, waɗanda suke cikin tsarin firistoci suna da dalili mai kyau na gaskata cewa Jehobah zai yi musu tanadin bukatunsu.

5 Kamar dai Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ta yi tanadin ushiri na biyu, da aka keɓe don biyan bukatun iyali da kuma jin daɗi a lokacin tarurruka masu tsarki a kowacce shekara. (K. Sha 14:22-27) Isra’ilawa sun yi amfani da wannan ushiri don su taimaki matalauta da kuma Lawiyawa a ƙarshen kowacce shekara uku da na shida cikin waɗannan shekara bakwai. Me ya sa aka haɗa Lawiyawa a cikin wannan dokar? Domin ba su da “rabo ko gādo” a Isra’ila.—K. Sha 14:28, 29.

6. A ina ne Lawiyawa suke zama ko da yake ba su da rabo a cikin ƙasar?

6 Kana iya yin mamaki, ‘idan Lawiyawa ba su da rabo a ƙasar, a ina suke zama?’ Allah ya kula da su. Ya ba su birane 48 tare da filaye a cikin waɗannan biranen. Waɗannan birane sun haɗa da biranen mafaka guda shida. (Lit. Lis. 35:6-8) Saboda haka, Lawiyawa suna da wurin zama a lokacin da ba sa hidima a wuri mai tsarki na Allah. Jehobah yana kula da bukatun waɗanda suka ba da kansu ga hidimarsa sosai. Ta yaya Lawiyawa za su iya nuna cewa Jehobah ne rabonsu? Ta wajen dogara cewa Jehobah yana da ikon ba su abin da suke bukata kuma yana son ya kula da su.

7. Mene ne ake bukata Lawiyawa su yi don Jehobah ya zama rabonsu?

7 A cikin Dokar, ba a yi wa Ba’isra’ila da bai ba da ushiri horo ba. Amma firistoci da Lawiyawa ne suke shan wahala sa’ad da mutane ba su yi biyayya ga dokar Jehobah game da ushiri ba. Hakan ya faru a zamanin Nehemiya. A sakamako, Lawiyawa za su yi aiki a gonaki kuma ba za su yi aikinsu a matsayin masu hidima ba. (Karanta Nehemiya 13:10.) Lawiyawa za su samu abin biyan bukatunsu idan al’ummar ta yi biyayya ga Dokar Jehobah. Kuma firistoci da Lawiyawa suna bukatar su yi imani ga Jehobah da hanyoyin da yake kula da bukatunsu.

Jehobah Ya Kasance Rabo ga Lawiyawa Ɗai-Ɗai

8. Mene ne ya damu Asaph Balawi?

8 A matsayin ƙabila, Jehobah ne rabon Lawiyawa. Amma wasu Lawiyawa ɗai-ɗai sun yi amfani da kalaman nan “Ubangiji rabona ne” sa’ad da suke magana game da abutarsu da Allah da kuma dogararsu a gare shi. (Mak. 3:24) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar wani mawaƙi da kuma marubuci Balawi wanda ya ce Jehobah ne rabonsa. Za mu kira shi Asaph, ko da yake yana iya zama wani a cikin iyalin Asaph, wanda shi ne ainihin mawaƙi daga cikin Lawiyawa a zamanin Sarki Dauda. (1 Laba. 6:31-43) Zabura ta 73 ta ce wannan Asaph ya soma kishin mugaye kuma bai fahimci dalilin da ya sa suke more rayuwa ba. Ya ma ce: “Gaskiya, banza na tsarkake zuciyata, na wanke hannuwana da rashin laifi.” Kamar dai Asaph ya ɗan manta cewa aikin da Jehobah ya ba shi ya yi na musamman ne. Ya manta cewa Jehobah ne rabonsa. Ya damu sosai har ya “shiga wuri mai-tsarki na Allah.”—Zab. 73:2, 3, 12, 13, 17.

9, 10. Me ya sa Asaph ya ce Allah ne ‘rabonsa har abada’?

9 Sa’ad da Asaph ya shiga wuri mai tsarki, sai ya soma canja ra’ayinsa. Wataƙila irin wannan abin ya taɓa faru maka. Mai yiwuwa kai ma ka manta na ɗan lokaci cewa hidimarka ga Jehobah na musamman ne kuma ka soma tunani game da dukiya da wataƙila za ka iya samu. Amma ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan tarurrukan Kirista, za ka soma tunani yadda Jehobah yake yi. Asaph ya fahimci abin da zai faru da mugaye daga baya. Ya yi tunanin abubuwa masu kyau da yake da su a matsayin bawan Allah. A ƙarshe ya ce Jehobah zai riƙe hannunsa na dama kuma ya yi masa ja-gora. Kuma ya gaya wa Jehobah: “Ba kuwa wani a cikin duniya wanda ni ke muradinsa sai kai.” (Zab. 73:23, 25) Sai ya ce Jehobah ne rabonsa. (Karanta Zabura 73:26.) Ko da yake ‘jiki da zuciyar’ wannan marubucin zabura sun kāsa, amma Allah zai zama ‘rabonsa har abada.’ Marubucin wannan zabura yana da tabbaci cewa Jehobah zai tuna da shi a matsayin abokinsa. Ba zai manta da hidimar da ya yi da aminci ba. (M. Wa. 7:1) Babu shakka, hakan ya ƙarfafa Asaph sosai! Ya rera waƙa: “Amma ya yi mani kyau in kusanci Allah: Na maida Ubangiji Yahweh mafakata.”—Zab. 73:28.

10 Sa’ad da Asaph ya ce Jehobah ne rabonsa, ba ya magana kaɗai game da abin duniya da ya samu a matsayin Balawi. Yana magana musamman game da hidimarsa ga Jehobah da kuma abutarsa da Maɗaukaki. (Yaƙ. 2:21-23) Don ya ci gaba da zama abokin Jehobah, Asaph zai ci gaba da kasancewa da bangaskiya ga Jehobah kuma ya dogara a gare shi. Zai kasance da tabbaci cewa idan ya yi biyayya ga Jehobah zai albarkace shi da gaba mai kyau. Kai ma za ka iya kasance da wannan tabbacin cewa Jehobah zai yi maka hakan.

11. Wace tambaya ce Irmiya ya yi wa Jehobah, kuma ta yaya Jehobah ya amsa tambayar?

11 Wani Balawi da ya ce Jehobah ne rabonsa shi ne annabi Irmiya. Bari mu tattauna dalilin da ya sa ya faɗi hakan. Yana zama a wani Birnin Banyamin kusa da Urushalima da ake kiran Anathoth. (Irm. 1:1) Akwai lokacin da Irmiya ya tambayi Jehobah dalilin da ya sa masu mugunta suke yin rayuwa mai kyau amma masu adalci suke shan wuya. (Irm. 12:1) Sa’ad da ya ga abin da yake faruwa a Urushalima da kuma Yahuda ya kai ƙara wurin Jehobah. Irmiya ya san cewa Jehobah mai adalci ne. Jehobah ya ba Irmiya amsa ta wurin gaya masa ya yi wa’azin saƙon halaka, sa’annan Jehobah ya sa wannan annabcin ya cika. Waɗanda suka yi biyayya ga Jehobah ‘sun tsira,’ amma mugayen da ba su mai da hankali ga kashedin ba suka halaka.—Irm. 21:9.

12, 13. (a) Mene ne ya sa Irmiya ya ce: “Ubangiji ne rabona,” kuma wane ra’ayi ne ya kasance da shi? (b) Me ya sa dukan ƙabilun Isra’ila suke bukatar su jira Jehobah cikin haƙuri kamar yadda Irmiya ya yi?

12 Bayan haka, sa’ad da Irmiya ya dubi ƙasarsu kuma ya ga yadda ta zama kango, ya ji kamar yana tafiya a cikin duhu. Kamar dai Jehobah ya sa ya zama kamar “waɗanda sun daɗe da mutuwa.” (Mak. 1:1, 16; 3:6) Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su dawo wurin Ubansu na samaniya, amma muguntarsa ta yi yawa har da Jehobah zai halaka Urushalima da Yahuda. Hakan ya sa Irmiya baƙin ciki, ko da yake ya yi abin da yake da kyau. Ko a wannan lokaci na baƙin ciki, Irmiya ya ce: “Ba mu halaka ba.” Ya ce, game da jin ƙan Jehobah: “Sabuwa ce kowace safiya.” Kuma a wannan lokacin ne Irmiya ya ce: “Ubangiji rabona ne.” Ya ci gaba da kasancewa da gatar bauta wa Jehobah a matsayin annabi.—Karanta Makoki 3:22-24.

13 Ƙasar Isra’ilawa ta kasance kango na tsawon shekaru 70. (Irm. 25:11) Kalaman Irmiya cewa “Ubangiji rabona ne” sun nuna cewa ya dogara ga Jehobah. Kuma hakan ya ba shi dalilin ‘sa begensa gareshi,’ wato, ya jira cikin haƙuri don Jehobah ya aikata. Dukan ƙabilun Isra’ila sun yi rashin gadonsu, saboda haka suna bukatar su jira yadda Irmiya ya jira. Jehobah ne kaɗai begen da suke da shi. Bayan shekaru 70, sun koma ƙasarsu kuma sun samu zarafin bauta masa a wurin.—2 Laba. 36:20-23.

Jehobah Zai Iya Kasance Rabo ga Wasu

14, 15. Ban da Lawiyawa, wane ne kuma yake da Jehobah a matsayin rabonsa, kuma me ya sa?

14 Asaph da Irmiya sun fito daga ƙabilar Lawi, amma ba Lawiyawa kaɗai ba ne za su samu gatan bauta wa Jehobah. Matashi Dauda, sarkin Isra’ila na gaba, ya kira Allah ‘rabonsa a cikin ƙasar masu-rai.’ (Karanta Zabura 142:1, 5.) Sa’ad da Dauda ya rubuta wannan zabura, ba ya cikin fada ko kuma cikin gida. Ya ɓoye cikin kogon dutse a ƙalla sau biyu don maƙiyansa. A wani lokaci ya ɓoye kusa da garin Adullam kuma ɗaya a cikin jeji na En-gedi. Wataƙila ya rubuta Zabura ta 142 a ɗaya cikin waɗannan kogwanni.

15 Idan haka ne, Sarki Saul ne yake nema ya kashe Dauda. Saboda haka, Dauda ya gudu zuwa cikin kogon dutse da zai yi wuya a same shi. (1 Sam. 22:1, 4) A wannan wurin da yake shi kaɗai, mai yiwuwa Dauda ya ji cewa ba shi da aboki da zai kāre shi. (Zab. 142:4) A wannan lokacin ne Dauda ya nemi taimakon Allah.

16, 17. (a) Me ya sa Dauda ya ji cewa ba shi da mai taimakonsa? (b) A wurin waye ne Dauda zai iya neman taimako?

16 Kafin Dauda ya rubuta Zabura ta 142, wataƙila ya ji abin da ya faru da Babban Firist Ahimelech, wanda ba tare da sanin abin da ya faru ba ya taimaka wa Dauda sa’ad da yake guduwa daga Saul. Sarki Saul don kishi ya sa aka kashe Ahimelech da iyalinsa. (1 Sam. 22:11, 18, 19) Dauda ya ji shi ne sanadiyyar mutuwarsu. Kamar dai ya kashe firist wanda ya taimake shi. Idan kana cikin yanayin Dauda, za ka ji kana da alhaki? Dauda ya daɗa kasancewa cikin matsi domin Saul ya ci gaba da bin sa.

17 Ba da daɗewa ba, annabi Sama’ila wanda ya naɗa Dauda ya zama sarki na gaba, ya rasu. (1 Sam. 25:1) Da hakan zai daɗa sa Dauda ya ji ya kaɗaita, kamar ba shi da mai taimako. Amma Dauda ya san cewa Jehobah zai taimaka masa. Dauda ba shi da gata na musamman da Lawiyawa suke da shi, amma an naɗa shi ya yi wani irin hidima, daga baya zai zama sarkin mutanen Allah. (1 Sam. 16:1, 13) Saboda haka, Dauda ya gaya wa Jehobah dukan abin da ke zuciyarsa kuma ya ci gaba da dogara gare shi. Jehobah zai iya zama rabonka kai ma. Kana iya dogara a gare shi yayin da ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka a hidimarsa.

18. Ta yaya waɗanda muka tattauna game da su a wannan talifin suka nuna cewa Jehobah ne rabonsu?

18 Jehobah ne rabon waɗanda muka tattauna a wannan talifin, kuma hakan yana nufin cewa sun samu aiki a cikin hidimarsa. Sun tabbata cewa Jehobah zai kula da su. Allah ne rabon Lawiyawa da wasu Isra’ilawa kamar Dauda. Ta yaya za ka sa Jehobah ya zama rabonka? Za mu tattauna wannan a talifinmu na gaba.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani a kan yadda Jehobah ya kula da bukatun firistoci ka duba littafin nan Insight on the Scriptures, Littafi na 2, shafi na 684.

Yaya Za Ka Amsa?

• A wane azanci ne Jehobah rabon Lawiyawa?

• Mene ne Asaph da Irmiya da Dauda suka yi da ya nuna cewa Jehobah ne rabonsu?

• Wane hali ne kake bukatar kasancewa da shi don Allah ya zama rabonka?

[Bayanin da ke shafi na 8]

Lawiyawa ba su samu gadon ƙasa ba. Maimakon haka, Jehobah ne rabonsu, don suna da gata mai girma na bauta masa

[Hoto a shafi na 7]

Ta yaya Jehobah ne rabon firistoci da Lawiyawa?

[Hoto a shafi na 9]

Mene ne ya taimaka wa Asaph ya ci gaba da sa Jehobah ya zama rabonsa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba