Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 10/15 pp. 21-25
  • Darussa Daga Addu’a Mai Ma’ana Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Addu’a Mai Ma’ana Sosai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • WATA NA MUSAMMAN
  • RANAR YIN IƘIRARI
  • ƊAUKAKA SUNA MAI GIRMA NA ALLAH
  • ABUBUWA MASU BAN AL’AJABI DA JEHOBAH YA YI
  • SUN BUKACI HORO
  • Jehobah Ne Rabona
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 10/15 pp. 21-25

Darussa Daga Addu’a Mai Ma’ana Sosai

“Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka.”—NEH. 9:5, Littafi Mai Tsarki.

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne abubuwa masu kyau ne Isra’ilawa suka yi sa’ad da Lawiyawa suka kira taro?

  • Mene ne Jehobah ya yi wa mutanensa da ya tabbata mana cewa ya isa a ƙira shi da wannan sunan?

  • Waɗanne darussa ne muka koya daga addu’ar da Lawiyawa suka yi?

1. Wane taron bayin Allah ne za mu tattauna, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu yi tunani a kai?

“KU TASHI tsaye, ku albarkaci Ubangiji Allahnku, tun daga madawwaman zamanai har abada.” Da wannan furuci mai motsawa sosai ne Lawiyawa suka gayyaci bayin Allah su taru don su yi addu’a ga Allah. Wannan ɗaya ce cikin addu’o’i masu tsawo da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki. (Neh. 9:4, 5) Mutanen sun taru a Urushalima a ranar 24 ga watan bakwai na Yahudawa, wato watan Tishri (Satumba ko Oktoba) a shekara ta 455 kafin zamaninmu. Yayin da muke tattauna abin da ya sa aka yi wannan taron, ka yi tunani a kan waɗannan tambayoyin: ‘Mene ne Lawiyawa suka saba yi da ya sa ya yiwu su yi taro a wannan ranar? Mene ne za mu iya koya daga addu’ar da Lawiyawa suka yi?’—Zab. 141:2.

WATA NA MUSAMMAN

2. Wane misali mai kyau ne Isra’ilawa suka kafa mana a yau?

2 Yahudawa sun gama gina ganuwar Urushalima wata ɗaya kafin su yi wannan taron. (Neh. 6:15) Sun kammala aikin cikin kwana 52 ne kawai. Bayan haka, sai suka taru a rana ta farko na watan Tishri don su saurari Shari’ar Allah da Ezra da wasu Lawiyawa za su karanta da kuma bayyana musu. Sai iyalai da “dukan waɗanda su ke da fahimin ji” suka kasance a tsaye suna saurara “tun da sassafe har tsakiyar rana.” Wannan misali ne mai kyau a gare mu da yake muna halartar taro a Majami’un Mulki masu kyau, ko ba haka ba? Amma a wasu lokuta sa’ad da ake taro, wataƙila mu riƙa tunanin wasu abubuwan da ba su da muhimmanci. Idan haka ne yanayinka, ka yi la’akari har ila da misalin Isra’ilawa. Sa’ad da suka saurara da kyau, sai suka yi tunani a kan abin da suka ji, hakan ya sa suka soma kuka don ba su bi Dokar Allah ba.—Neh. 8:1-9.

3. Wane umurni ne Isra’ilawa suka bi?

3 Amma wannan ba lokacin yin iƙirari ba ne. Ranar idi ce, kuma Jehobah ya so mutanensa su yi farin ciki. (Lit. Lis. 29:1) Sai Nehemiya ya gaya wa jama’ar cewa: “Ku yi tafiyarku, ku ci romo, ku sha zaki, ku aike da rabo wurin wanda ba a shirya masa kome ba: gama yau rana ce mai-tsarki ga Ubangiji namu: kada kuwa ku yi ɓacin rai; gama farinciki na Ubangiji shi ne ƙarfinku.” Mutanen sun yi biyayya kuma suka “yi murna ƙwarai.”—Neh. 8:10-12.

4. Mene ne magidantan Isra’ilawa suka yi, kuma mene ne suka gano cewa abu ne mai muhimmanci a Idin Bukkoki?

4 Washegari, dukan magidanta suka haɗu wuri ɗaya don su yi nazari a kan Dokar Allah kuma su tabbata cewa suna bin dukan abin da aka rubuta a ciki. Sa’ad da suke nazarta Dokar, sai suka gano cewa al’ummar tana bukata ta riƙa yin Idin Bukkoki kuma ta kammala idin da taro mai-saduda daga ranar 15 zuwa 22 na watan Tishri. Sai suka soma yin shiri nan da nan don idin. Tun daga zamanin Joshua, ba a taba yin Idin Bukkoki irin wannan ba, kuma an “yi murna ƙwarai” a lokacin. A kowace rana da ake yin wannan idin bukkokin, ana karanta wa jama’a Dokar Allah “rana kan rana, tun daga rana ta fari har rana ta ƙarshe.”—Neh. 8:13-18.

RANAR YIN IƘIRARI

5. Mene ne mutanen Allah suka yi kafin Lawiyawa su yi addu’a a madadin su?

5 Kwana biyu bayan idin, wato ranar 24 ga watan Tishri ne ya fi dacewa bayin Allah su yi iƙirarin zunubansu. Saboda haka, ba su ci da sha a wannan ranar ba. Maimakon haka, mutanen sun yi azumi kuma sun saka tsummokara don su nuna cewa sun yi zunubi. Kuma ana karanta wa mutanen Dokar Allah na sa’o’i uku da safe. Da rana kuma, sai “suka furta laifi, suka yi sujada ga Ubangiji Allahnsu.” A lokacin ne Lawiyawa suka yi addu’a a madadin su. —Neh. 9:1-4.

6. Mene ne ya taimaka wa Lawiyawa su yi addu’a mai ma’ana, kuma wane darasi ne muka koya?

6 Da yake Lawiyawa suna karanta Dokar Allah a kai a kai, hakan ya taimake su su yi addu’a mai ma’ana. Ayoyi goma na farko sun mai da hankali ga ayyukan Allah da kuma halayensa. A sauran ayoyin kuma, Lawiyawan sun ambata wasu zunubai masu yawa da Isra’ilawa suka yi da kuma abin da ya sa ba su cancanci ‘yawan jinƙan’ Allah ba. (Neh. 9:19, 27, 28, 31) Mene ne za mu iya koya daga Lawiyawa? Ya kamata mu riƙa karanta da kuma yi bimbini a kan Kalmar Allah kowace rana. Hakan zai nuna cewa muna barin Allah ya yi mana magana. A sakamako, za mu samu abubuwa masu yawa da za mu yi addu’a a kai kuma addu’o’inmu za su fi kasancewa da ma’ana.—Zab. 1:1, 2.

7. Mene ne Lawiyawa suka roƙi Allah, kuma mene ne muka koya daga misalinsu?

7 A addu’ar da Lawiyawa suka yi, sun roƙi Allah abu ɗaya kawai. Mun ga wannan roƙon a aya ta 32. Sun ce: “Yanzu fa, ya Allahnmu, mai-girma, mai-iko, Allah mai-ban razana, mai-kiyaye alkawari da jinƙai, kada dukan wahalar ta zama kamar ƙanƙanin abu a gabanka, wahala da ta afko mana, da sarakunanmu, da hakimanmu, da firistoci namu, da annabawanmu, da ubanninmu, da dukan jama’arka, tun zamanin sarakunan Assyria har yau.” Hakika, Lawiyawa sun kafa mana misali mai kyau wajen yabon Jehobah da kuma ɗaukaka shi da farko kafin mu roƙe shi wani abu.

ƊAUKAKA SUNA MAI GIRMA NA ALLAH

8, 9. (a) Ta yaya Lawiyawa suka nuna cewa suna da tawali’u a yadda suka soma addu’arsu? (b) Waɗanne rundunai biyu na sama ne Lawiyawa suka ambata?

8 Ko da yake Lawiyawa sun yi addu’a mai ma’ana sosai, sun kasance da tawali’u kuma sun ji kamar abubuwan da suka furta ba su kai su yabi Jehobah ba. Sai suka yi addu’a ga Jehobah, suka ce: “Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, . . . Ko da yake ba yabon da ɗan Adam zai yi har ya isa.”—Neh. 9:5, LMT.

9 An ci gaba da addu’ar: “Kai ne Ubangiji, kai kaɗai; kai ne ka yi sama, da saman sammai, da dukan rundunarsu, ƙasa kuma da abubuwan da ke bisanta, da tekuna, da dukan abin da ke cikinsu, kana kuwa kiyaye su duka; rundunar sama kuma tana yi maka sujada.” (Neh. 9:6) Hakika, Jehobah ne ya halicci sararin sama har da damin taurari. Ƙari ga haka, ya halicci dukan abubuwan da ke wannan duniyar, haɗe da abubuwa masu ban al’ajabi da abubuwa masu rai su riƙa hayayyafa. A addu’ar, an kira mala’ikun Allah “rundunar sama.” (1 Sar. 22:19; Ayu. 38:4, 7) Kuma mala’ikun suna yin nufin Allah ta yin hidima ga ’yan Adam ajizai ‘waɗanda za su gaji ceto.’ (Ibran. 1:14) A yau, bayin Allah suna yin hidima kamar rundunar da aka horar da kyau. Saboda haka, ya kamata mu bi misalin mala’iku ta wajen yi wa Allah hidima da tawali’u.—1 Kor. 14:33, 40.

10. Mene ne muka koya daga abin da Allah ya yi wa Ibrahim?

10 Bayan haka, sai Lawiyawan suka ambata abin da Allah ya yi wa Abram. Jehobah ya canja sunansa zuwa Ibrahim kuma sunan yana nufin ‘uban jama’a,’ ko da yake shi ɗan shekara 99 ne kuma bai da yara. (Far. 17:1-6, 15, 16) Allah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa zuriyarsa za ta gāji ƙasar Kan’ana. Lawiyawan sun kwatanta yadda Jehobah ya cika alkawarinsa, kuma sun ce: “Kai ne Ubangiji Allah wanda ya zaɓi Abram, ya fito da shi daga cikin Ur na Chaldees, ya ba shi suna Ibrahim; ka kuma iske zuciyatasa mai-aminci a gabanka, ka yi alkawari kuma da shi za ka ba shi ƙasar Kan’aniyawa, . . . domin a bayar ga zuriyarsa, har kuma ka cika maganarka; gama kai mai-adalci ne.” (Neh. 9:7, 8) Bari dukanmu mu bi misalin Jehobah ta wajen cika alkawarinmu.—Mat. 5:37.

ABUBUWA MASU BAN AL’AJABI DA JEHOBAH YA YI

11, 12. Mene ne ma’anar sunan nan Jehobah, kuma mene ne ya yi wa bayinsa da ya nuna cewa ya isa a kira shi da sunan?

11 Sunan nan Jehobah yana nufin “Yana Sa Ya Kasance,” kuma wannan yana nuna cewa Allah a ko yaushe yana aiki tuƙuru don ya cika alkawuransa. An ga hakan sa’ad da Allah yake sha’ani da zuriyar Ibrahim a lokacin da suke bauta a ƙasar Masar. A lokacin, kamar ba zai yiwu a ’yantar da al’ummar don su shiga Ƙasar Alkawari ba. Amma, Allah ya ɗauki wasu matakai masu kyau don ya ga cewa ya cika alkawarinsa. Ta yin hakan, ya nuna cewa shi kaɗai ne ya isa a ƙira shi da wannan sunan, wato Jehobah.

12 A addu’ar da Lawiyawan suka yi, sun ambata wasu abubuwan da Jehobah ya yi wa mutanensa. Sun ce: “Ka ga ƙuncin ubanninmu cikin Masar, ka ji kukansu kuma a bakin Jan Teku; ka nuna alamu da al’ajibai bisa Fir’auna, da dukan bayinsa, da dukan mutanen ƙasarsa; gama ka sani suka yi masu aikin alfarma; ka kuwa girmama sunanka, kamar yadda ya ke yau. Ka raba teku a gabansu kuma, har da za su shige a ƙasa ta tsakiyar teku; masu-cin sawunsu kuwa ka yashe su a cikin zurfafa, sai ka ce dutse a cikin manyan ruwaye.” Sai suka sake ambata wasu abubuwa da Allah ya yi wa mutanensa a addu’ar, suna cewa: “Ka kuma sarayyadda mazaunan ƙasan a gabansu, watau su Kan’aniyawa ke nan, . . . Suka ci birane masu-ganuwa, da ƙasa mai-romo, suka amshi mulkin gidaje cike da kayan kirki, rijiyoyi haƙaƙu, gonaki na anab, da gonaki na zaitun, da itatuwa masu-’ya’ya a yalwace: suka ci fa, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, suka yi nishatsi a cikin alherinka mai-girma.”—Neh. 9:9-11, 24, 25.

13. Mene ne Jehobah ya yi wa bayinsa jim kaɗan da suka bar Masar, kuma mene ne suka yi daga baya?

13 Akwai wasu matakai da yawa masu kyau da Allah ya ɗauka don ya cika nufinsa. Alal misali, nan da nan bayan da Isra’ilawa suka bar ƙasar Masar, Jehobah ya tanadar musu da dokoki kuma ya koya musu yadda za su bauta masa. A addu’ar da Lawiyawan suka yi, sun ce: “Ka sauko kuma a bisa dutsen Sinai, ka yi magana da su daga sama, ka ba su hukunci mai-adalci, da shari’u masu-gaskiya, farillai masu-kyau da dokoki.” (Neh. 9:13) Jehobah ya ƙoƙarta ya koya wa mutanensa don su iya yin abin da ake bukata a gare su idan suna so su gāji Ƙasar Alkawari. Duk da haka, Isra’ilawan ba su bi dokarsa ba.—Karanta Nehemiya 9:16-18.

SUN BUKACI HORO

14, 15. (a) Ta yaya Jehobah ya nuna jin ƙai ga Isra’ilawa? (b) Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya yi sha’ani da al’ummar da ya zaɓa?

14 Lawiyawan sun ambata laifuffuka biyu da Isra’ilawa suka yi jim kaɗan bayan da suka yi alkawari a Dutsen Sinai cewa za su bi Dokar Allah. Sun cancanci mutuwa a jeji don waɗannan laifuffukan. Amma addu’ar da suka yi ta yabi Jehobah, sun ce: “Cikin yawan jiyejiyenƙanka ba ka yashe su cikin jeji ba: . . . Shekara ma arba’in ka agaje su . . . ba su rasa komi ba; tufafinsu ba su tsufa ba, ƙafafunsu ba su kumbura ba.” (Neh. 9:19, 21) A yau ma, Jehobah yana tanadar mana da dukan abin da muke bukata don mu bauta masa da aminci. Kada mu taɓa zama kamar dubban Isra’ilawa da suka mutu a jeji don taurin kai da kuma rashin bangaskiya. Hakika, an rubuta waɗannan labaran “domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.”—1 Kor. 10:1-11.

15 Abin baƙin ciki kuma shi ne, Isra’ilawa da suka shiga Ƙasar Alkawari ba su ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah ba. Sun soma bauta wa allolin Kan’aniyawa haɗe da yin lalata da kuma yin hadaya da ’ya’yansu. Saboda haka, Jehobah ya bar wasu al’ummai su wulaƙanta su. Amma sa’ad da suka tuba, Allah ya gafarce su kuma ya cece su daga magabtansu. Hakan ya faru sau da sau. (Karanta Nehemiya 9:26-28, 31.) Lawiyawan sun yi iƙirari suna cewa: “Shekara dayawa kana haƙuri da su, ka yi shaida a kansu kuma da ruhunka ta bakin annabawanka: har wa yau suka ƙi kasa kunne: domin wannan ka bashe su a cikin hannun al’umman ƙasashen.”—Neh. 9:30.

16, 17. (a) Mene ne ya faru sa’ad da Isra’ilawa suka sake soma yin rashin biyayya ga Jehobah? (b) Wane iƙirari ne Isra’ilawan suka yi, kuma wane alkawari ne suka yi?

16 Bayan da suka dawo daga bauta a ƙasar Babila, Isra’ilawan sun sake yi wa Jehobah rashin biyayya. Amma, wane bambanci ne aka samu? Lawiyawan sun bayyana a addu’arsu cewa: “Ga shi, mu bayi ne yau, don zancen ƙasa kuwa wadda ka bayar ga ubanninmu su ci amfaninta da romonta, ga shi, a cikinta mu bayi ne. Ta kuwa bada ni’ima dayawa ga sarakuna waɗanda ka sanya a bisanmu sabili da zunubanmu: kuma . . . mun ƙuntata ƙwarai.”—Neh. 9:36, 37.

17 Shin addu’ar Lawiyawan ta nuna cewa Allah ya yi rashin adalci ne da ya ƙyale mutanensa su sha wahala? A’a. Sun yi iƙirari suna cewa: “Amma ka barata cikin dukan abin da ya same mu; gama kai ka aika da gaskiya, amma mu mun aika da mugunta.” (Neh. 9:33) Sun kammala addu’arsu mai ma’ana da alkawari cewa al’ummar za ta ci gaba da yin biyayya ga Dokar Allah. (Karanta Nehemiya 9:38; 10:29) Sun rubuta wannan alkawarin kuma shugabanni 84 ne suka hatimce shi.—Neh. 10:1-27.

18, 19. (a) Mene ne ya kamata mu yi idan muna so mu tsira zuwa sabuwar duniya? (b) Mene ne za mu ci gaba da yin addu’a a kai, kuma me ya sa?

18 Idan muna son mu tsira zuwa sabuwar duniya, muna bukatar horo daga Jehobah. Manzo Bulus ya yi wannan tambayar: “To, wane ɗa ne ubansa ba ya horonsa?” (Ibran. 12:7, LMT) Muna nuna cewa mun amince da horon Jehobah idan muka ci gaba da bauta masa da aminci da kuma bin ja-gorar ruhu mai tsarki. Idan muka aikata zunubi mai tsanani, muna da tabbaci cewa Jehobah zai gafarta mana idan muka tuba da gaske kuma muka amince da horonsa.

19 Ba da daɗewa ba, Jehobah zai ɗauki wasu matakai don ya yi wa kansa suna fiye da yadda ya yi sa’ad da ya ceci Isra’ilawa a ƙasar Masar. (Ezek. 38:23) A lokacin da Allah zai tsarkake sunansa, duk waɗanda suka kasance da aminci a gare shi za su tsira zuwa sabuwar duniya, kamar yadda Isra’ilawa suka shiga Ƙasar Alkawari. (2 Bit. 3:13) Saboda haka, bari dukanmu mu ci gaba da yin addu’a don a tsarkake sunan Allah mai girma. A talifi na gaba za mu tattauna wata addu’a da za ta taimaka mana mu yi abin da ya dace don mu sami albarkar Allah yanzu da kuma har abada.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba