Ka Yi Tseren Da Jimiri
“Mu kuma yi tseren nan da ke gabanmu tare da jimiri.”—IBRAN. 12:1, Littafi Mai Tsarki.
1, 2. Da mene ne manzo Bulus ya gwada tafarkin rayuwa ta Kirista?
ANA tsere a wurare da yawa, a kowacce shekara. Wasu da suke yin wannan tseren ƙwararru ne sosai, kuma suna son su ci ladar. Amma yawancinsu sun san cewa ba za su iya cin tseren ba. Abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne su gama tseren.
2 A cikin Littafi Mai Tsarki, an gwada tafarkin rayuwa na Kirista da tsere. Manzo Bulus ya rubuta game da wannan tseren a cikin wasiƙarsa ta farko zuwa ga Kiristoci da ke Korinti na dā. Ya rubuta: “Ba ku sani ba, masu-tsere cikin fage duka su kan yi gudu, amma ɗaya ne ya kan karɓi rawani? Haka nan kuma ku yi tsere, domin ku samu.”—1 Kor. 9:24.
3. Me ya sa Bulus ya ce mutum ɗaya ne kawai zai samu ladar?
3 Shin Bulus yana nufin cewa mutum ɗaya ne kawai cikin waɗannan Kiristoci za su samu ladar rai kuma dukan sauran za su yi tseren a banza? A’a! Masu tsere suna horar da kansu sosai kuma su yi tsere a hanya mafi kyau domin su ci tseren. Bulus yana son ’yan’uwansa su sa ƙwazo sosai hakan a tserensu na rai madawwami. Dukan Kiristoci da suka yi hakan za su iya samun ladar rai madawwami.
4. Mene ne muke bukatar mu sani game da tseren da Kiristoci suke yi?
4 Waɗannan kalaman suna da ban ƙarfafa a gare mu, suna kuma sa mu yi tunani sosai game da yadda muke yin rayuwa a yau. Idan muka yi rayuwa da ke faranta wa Jehobah rai, muna da begen yin rayuwa har abada a sama ko kuma a cikin Aljanna a duniya. Amma rayuwa ta Kirista tana kama da yin dogon tsere a hanyar da ke da haɗarurruka masu yawa. Da akwai abubuwa masu yawa da za su iya sa mu rage hidimarmu ga Jehobah, ko kuma su sa mu daina bauta wa Jehobah. (Mat. 7:13, 14) Hakan ya riga ya faru ga wasu bayin Jehobah. Waɗanne tarkuna da haɗarurruka ne za a fuskanta a yin tsere na rai? Ta yaya za ka guje musu? Mene ne za ka iya yi don ka gama kuma ka ci tseren?
Muna Bukatar Haƙuri Don Mu Yi Nasara
5. Mene ne Bulus ya bayyana a Ibraniyawa 12:1?
5 A wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa da ke Urushalima da Yahudiya, Bulus ya kuma yi magana game da masu tsere. (Karanta Ibraniyawa 12:1.) Ya bayyana dalilin da ya sa Kiristoci za su ci gaba da tserensu da kuma abin da dole ne su yi don su gama tseren. Za mu fara yin magana a kan dalilin da ya sa Bulus ya rubuta wannan wasiƙar zuwa ga Ibraniyawa da kuma abin da yake son su yi. Kuma za mu yi magana game da abin da za mu iya koya daga abin da ya rubuta musu.
6. Mene ne shugabannin addinai suka yi ƙoƙari su yi wa Kiristoci?
6 Kiristoci na ƙarni na farko, musamman waɗanda suke zama a Urushalima da Yahudiya sun fuskanci gwaje-gwaje da matsaloli masu yawa. Shugabannin addinai na Yahudawa sun yi ƙoƙari su tilasta musu su yi musu biyayya. Kusan shekara talatin kafin wannan lokacin, sun ma sa mutane su gaskata cewa Yesu Kristi yana gaba da gwamnati kuma shi mai aikata laifi ne da ya cancanci ya mutu. Waɗannan shugabannin addinai sun kashe Yesu Kristi, kuma yanzu suna son waɗanda suke wa’azi game da shi su daina. A cikin littafin Ayyukan Manzanni, muna iya karanta abin da ya faru bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Waɗannan shugabannai sun kai wa Kiristoci farmaki sau da yawa don su hana su wa’azi. Rayuwa ta yi wa Kiristoci masu aminci wuya sosai.—A. M. 4:1-3; 5:17, 18; 6:8-12; 7:59; 8:1, 3.
7. Me ya sa lokacin da waɗannan Kiristocin suke zama yake da wuya sosai?
7 Wani dalili kuma da ya sa waɗannan Kiristoci suka yi rayuwa a lokaci mai wuya shi ne cewa an kusan halaka Urushalima. Yesu ya yi musu gargaɗi cewa Allah zai halaka Urushalima. Ya gaya musu abin da zai faru kafin wannan halakar, kuma ya gaya musu ainihin abin da ya kamata su yi don su tsira. (Karanta Luka 21:20-22.) Yesu ya yi musu gargaɗi: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko.”—Luk 21:34.
8. Mene ne mai yiwuwa ya sa wasu Kiristoci suka rage hidimarsu ga Jehobah ko suka daina bauta masa?
8 Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa kusan shekaru 30 bayan Yesu ya faɗa waɗannan kalaman. Ta yaya shigewar lokaci ya shafi waɗannan Kiristoci? Wasu sun faɗa wa matsi da abubuwa masu raba hankali na yau da kullum kuma sun kasa samun ci gaba na ruhaniya da zai ƙarfafa su. (Ibran. 5:11-14) Wataƙila wasu Kiristoci suna ganin cewa zai fi sauƙi su yi rayuwa kamar sauran Yahudawa. Mai yiwuwa sun yi tunani cewa hakan ba laifi ba ne domin har ila Yahudawa sun gaskata da Allah kuma suna bin yawancin Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa. Kuma akwai wasu mutane a cikin ikilisiyoyi da suke ƙoƙari su tilasta wa wasu su yi biyayya ga Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa da al’adun Yahuduwa. Mene ne Bulus ya faɗa don ya ƙarfafa ’yan’uwansa Kiristoci su ci gaba da rayuwa kamar Kiristoci kuma su kasance da aminci ga Jehobah?
9, 10. (a) Wane ƙarfafawa ne Bulus ya ba da a kusan ƙarshen Ibraniyawa sura 10? (b) Me ya sa Bulus ya rubuta game da ayyukan bangaskiya na shaidu na dā?
9 Jehobah ya hure Bulus ya rubuta wannan wasiƙa mai ban ƙarfafa ga Kiristoci Ibraniyawa. A sura ta 10, ya bayyana cewa Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa “inuwar kyawawan matsaloli masu-zuwa” ne, kuma sai ta wurin hadayar Yesu ne kaɗai za a iya gafarta musu zunubansu. A ƙarshen wannan surar, Bulus ya ƙarfafa masu karatu: “Kuna da bukatar haƙuri, domin, bayan da kun aika nufin Allah, ku karɓi alkawarin. Gama da sauran jimawa kaɗan, wanda ke zuwa za shi zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.”—Ibran. 10:1, 36, 37.
10 A Ibraniyawa sura ta 11, Bulus ya bayyana abin da yake nufi a kasance da bangaskiya na gaske ga Allah ta wajen rubuta abubuwa da mutane masu bangaskiya suka yi. Me ya sa ya yi magana game da bangaskiya kafin ya sake magana game da jimiri? Domin yana son waɗannan Kiristoci su san cewa don a kasance da bangaskiya ga Jehobah, suna bukatar jimiri da ƙarfin zuciya. Ya ambata maza da mata masu yawa da a dā sun kasance da aminci ga Jehobah ko a yanayi mai wuya sosai. Misalinsu zai taimaka wa Kiristoci Ibraniyawa su jimre a yanayi mai wuya. Bayan ya ambata ayyukan bangaskiya na dukan waɗannan bayin Jehobah, Bulus ya gaya wa Kiristoci Ibraniyawa: “Da ya ke taron shaidu mai-girma haka yana kewaye da mu, bari mu tuɓe kowane abin nauwaitawa, da zunubin da ke manne mamu, tare da haƙuri [“jimiri,” LMT] kuma mu yi tseren da an sa gabanmu.”—Ibran. 12:1.
“Taron Shaidu”
11. Yaya yin tunani game da “taron shaidu mai-girma” zai shafe mu?
11 Bulus ya faɗa cewa bayin Jehobah da suke raye kafin zamanin Kiristoci ‘taron shaidu mai-girma ne da ke kewaye da mu.’ Sun kasance da aminci ga Jehobah har ƙarshen rayuwarsu, kuma misalinsu ya nuna cewa zai yiwu Kiristoci su kasance da aminci ga Jehobah har a cikin yanayi mai wuya. “Taron shaidu” ko kuma bayin Jehobah na dā suna kama da masu tsere da suka yi tseren sosai kuma suka gama. Yin tunani a kan misalinsu ya ƙarfafa waɗannan Kiristoci Ibraniyawa su ci gaba da tseren kuma su yi iya ƙoƙari don su gama tseren. Misalinsu zai ba su ƙarfin zuciya kuma ya tuna musu cewa zai yiwu su yi tseren ‘da jimiri’ kuma su gama tserensu. Zai yiwu mu ma mu yi hakan.
12. Mene ne za mu iya koya daga bangaskiyar mutanen da Bulus ya yi maganarsu?
12 Mutane da yawa masu aminci da Bulus ya ambata sun kasance cikin irin yanayin da muke ciki. Alal misali, Nuhu ya rayu kafin Jehobah ya halaka duniya na wannan zamanin da Rigyawa. Kuma muna rayuwa a kusan ƙarshen wannan zamanin. Jehobah ya gaya wa Ibrahim da Saratu su bar ƙasarsu don su biɗi bauta ta gaskiya kuma su jira cikar alkawarin Jehobah. Jehobah ya gaya mana mu daina rayuwa don kanmu kuma mu samu amincewarsa da albarka da zai ba mu. Musa ya yi doguwar tafiya a cikin jeji mai haɗari don ya kai Ƙasar Alkawari. Muna zama a muguwar duniya kuma muna jiran sabuwar duniya da Jehobah ya yi mana alkawarinta. Yana da muhimmanci mu yi tunani game da rayuwar waɗannan mutane masu aminci. Muna iya yin koyi da abubuwa da suka yi don su faranta wa Jehobah rai kuma mu koya darasi daga abubuwa da ba su faranta masa rai ba.—Rom. 15:4; 1 Kor. 10:11.
Ta Yaya Suka Yi Nasara?
13. Wane ƙalubale ne Nuhu ya fuskanta, kuma mene ne ya taimaka masa ya sha kansu?
13 Mene ne ya taimaka wa waɗannan bayin Jehobah su jimre kuma su gama tseren? Ka lura da abin da Bulus ya rubuta game da Nuhu. (Karanta Ibraniyawa 11:7.) Nuhu bai taɓa ganin “ruwan tufana a bisa duniya, domin a halaka dukan mai-rai” ba. (Far. 6:17) Hakan bai taɓa faruwa ba. Amma Nuhu bai yi tunani ba cewa ba zai yiwu a yi rigyawa ba. Me ya sa? Domin yana da bangaskiya cewa a koyaushe, Jehobah yana cika alkawarinsa. Saboda haka, Nuhu ba ya ganin cewa yana da wuya ainun ya yi biyayya ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Haka ya yi.” (Far. 6:22) Nuhu yana da abubuwa da yawa da zai yi. Zai gina jirgi da tattara dabbobi da tara abincin da iyalinsa da dabbobin za su ci, zai gargaɗi mutane game da Rigyawar kuma ya taimaka wa iyalinsa su kasance da bangaskiya sosai ga Jehobah. Bai yi wa Nuhu sauƙi ya yi dukan abubuwan da Jehobah ya umurce shi ba. Amma yana da bangaskiya ga Jehobah, saboda haka ya jimre a aikin da zai yi. Kuma Jehobah ya cece shi da iyalinsa kuma ya yi musu albarka mai yawa.
14. Waɗanne gwaje-gwaje ne Ibrahim da Saratu suka jimre, kuma wane darasi ne wannan ya koya mana?
14 Bulus ya ambata Ibrahim da Saratu cikin ‘taron shaidu mai girma da suka kewaye mu.’ Rayuwarsu ta canja sa’ad da Allah ya gaya musu su bar gidansu a birnin Ur. Suna da bangaskiya mai ƙarfi ga Jehobah kuma sun yi masa biyayya ko a yanayi mai wuya. Littafi Mai Tsarki ya kira Ibrahim “uban masu-bada gaskiya duka” domin ya yi sadaukarwa da yawa ga Jehobah. (Rom. 4:11) Kiristoci Ibraniyawa sun riga sun san game da rayuwar Ibrahim da iyalinsa, saboda haka, Bulus ya ambata wasu cikin ayyukansu na bangaskiya kawai. Amma hakan ya isa don a nuna yadda suke da bangaskiya sosai. Bulus ya ce game da su: “Dukan waɗannan [har da Ibrahim da iyalinsa] suka mutu cikin bangaskiya, ba su rigaya sun amshi alkawarai ba, amma daga nesa suka tsinkaye su, suka yi masu maraba, suka shaida haka nan su baƙi ne, alhazai ne cikin duniya.” (Ibran. 11:13) Bangaskiyarsu ga Allah da kuma abutarsu da shi sun taimaka musu su jimre a tseren.
15. Me ya motsa Musa ya yi irin rayuwar da ya yi?
15 Musa yana cikin bayin Jehobah da abin koyi ne da yake cikin “taron shaidu.” Musa ya bar gidansa da ɗaukaka da arziki na fadar sarki kuma ya zaɓa a “wulakance shi tare da mutanen Allah.” Mene ne ya motsa shi ya yi hakan? Bulus ya ba da amsa: “Yana sauraron sakamakon. . . . Ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” (Karanta Ibraniyawa 11:24-27.) “Zunubi domin ’yan kwanaki” bai raba hankalin Musa ba. Allah ya kasance da gaske a gare shi, kuma ya san cewa dukan alkawuran Allah za su cika. Hakan ya taimaka masa ya aikata da gaba gaɗi kuma ya jimre a yanayi mai wuya. Kuma hakan ya taimake shi ya yi aiki tuƙuru don ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar kuma ya kai su Ƙasar Alkawari.
16. Me ya sa Musa bai yi sanyin gwiwa ba domin bai iya shiga Ƙasar Alkawari ba?
16 Ibrahim da Musa sun mutu kafin alkawarin da Allah ya yi musu ya cika. Jim kaɗan kafin Isra’ilawa su shiga Ƙasar Alkawari, Allah ya gaya wa Musa: “Za ka ga ƙasan a gabanka; amma kai ba za ka shiga cikin ƙasa wadda ni ke ba ’ya’yan Isra’ila ba.” Domin shi da Haruna sun yi fushi don tawayen mutanen sun yi kuskure ga Allah “a tsakar ’ya’yan Isra’ila a wurin ruwaye na Meribah na Kadesh.” (K. Sha 32:51, 52) Musa bai yi sanyin gwiwa ba domin ba zai iya shiga Ƙasar Alkawari ba. Ya furta albarka ga mutanen kuma ya kammala da waɗannan kalaman: “Mai-farin zuciya ne kai, ya Isra’ila: Wanene yana kama da kai, al’umma mai-samun ceto ga Ubangiji, garkuwar taimakonka, shi wanda ya ke takobi na fifikon darajarka!”—K. Sha 33:29.
Darussa Dominmu
17, 18. (a) Mene ne za mu iya koya daga “taron shaidu”? (b) Mene ne za mu nazarta a talifi na gaba?
17 Mun koyi darussa daga rayuwar waɗanda suke cikin ‘taron shaidu mai-girma da ke kewaye da mu’ cewa don mu kammala tseren, dole ne mu kasance da bangaskiya ga Allah sosai da kuma alkawuransa. (Ibran. 11:6) Wannan bangaskiya zai shafi yadda muke yin rayuwa a yanzu. Mun san cewa Allah ya yi mana alkawari cewa za mu yi farin ciki a nan gaba. Muna iya “ganin wanda ba shi ganuwa” kuma mu yi tseren da jimrewa.—2 Kor. 5:7.
18 Tseren da Kiristoci suke yi ba shi da sauƙi. Amma za mu iya kammala tseren. A talifi na gaba, za mu tattauna wasu abubuwa da za su taimaka mana mu iya kammala tseren.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Me ya sa Bulus ya yi magana game da shaidu masu aminci na dā?
• Ta yaya misalin ‘taron shaidu mai girma da ke kewaye da mu’ suka taimaka mana mu jimre a tseren?
• Mene ne ka koya daga misalin Nuhu da Ibrahim da Saratu da kuma Musa?
[Hoto a shafi na 19]
Ibrahim da Saratu suna a shirye su bar jin daɗin birnin Ur