Ba “Dalilin Tuntuɓe” Ga Masu Ƙaunar Jehobah
“Salama mai-yawa tana ga waɗanda suke ƙaunar shari’arka; ba kuwa wani dalilin tuntuɓe garesu.”—ZAB. 119:165.
1. Ta yaya wata mai tsere ta nuna cewa ba ta yi sanyin gwiwa ba?
MARY DECKER matashiya ce sa’ad da ta fara gasar tsere. A shekara ta 1984, ta ƙware sosai a yin tsere, kuma mutane da yawa suna tsammanin za ta ci zinariya a wasan Olamfik. Amma, sa’ad da take tsere na mita 3,000, ta yi tuntuɓe kuma ta faɗi. Saboda haka, ba ta ƙarasa wannan gasar ba, amma ba ta daina yin tsere ba. Kuma bayan ’yan watanni, ta kammala tsere na mil ɗaya da sauri fiye da kowace mace.
2. Wane irin tsere ne Kiristoci suke yi, kuma yaya ya kamata mu yi shi?
2 A matsayinmu na Kiristoci, muna tsere don mu samu rai madawwami. Wajibi ne mu ci gaba da yin wannan tseren, don ba na ɗan lokaci ba ne da wanda ya fi gudu zai ci tseren. Kuma ba gudu ba ne da ake yi a hankali da mutum yakan tsaya a wasu lokatai, amma gudu ne na dogon zango. Ya kamata mai tsere na dogon zango ya jimre don ya yi gudun har zuwa ƙarshe. Manzo Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci da ke Korinti cewa: “Ba ku sani ba, masu-tsere cikin fage duka su kan yi gudu, amma ɗaya ne ya kan karɓi rawani? Haka nan kuma ku yi tsere, domin ku samu.”—1 Kor. 9:24.
3. Su waye ne suke samun lada a tseren rai madawwami?
3 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu yi irin wannan tseren. (Karanta 1 Korintiyawa 9:25-27.) Mece ce ladar wannan tseren? Rai madawwami ne. Shafaffu Kiristoci za su samu ladar zuwa sama, amma sauran ’yan Adam masu aminci za su kasance a nan duniya. A yawancin gasar tseren da ake yi a yau, waɗanda suka fi gudu ne suke samun lada. Amma a tseren da muke yi, dukan waɗanda suka jimre har ƙarshe za su samu lada. (Mat. 24:13) Masu yin gasar ba za su samu lada ba, idan ba su bi ƙa’idojin wasan ba ko kuma ba su gama tseren ba. Ƙari ga haka, a wannan tseren ne kaɗai ake samun ladar rai madawwami.
4. Me ya sa tseren rai madawwami ba cin tuwo ba ne?
4 Yin tseren rai madawwami ba cin tuwo ba ne. Yesu Kristi ne kaɗai ya yi wannan tsere ba tare da yin tuntuɓe ba. Amma, babu kowannenmu da zai iya yin haka. Almajiri Yaƙub ya ce, “a cikin abu dayawa dukanmu mu kan yi tuntuɓe.” (Yaƙ. 3:2) Ajizancinmu ko kuma na wasu zai iya sa mu yi sanyin gwiwa ko kuma mu ɗan daina tseren. Idan hakan ya faru, muna iya bukatar taimako don mu soma yin tseren kuma. Saboda haka, a wasu lokatai za mu iya yin tuntuɓe ko kuma mu faɗi.—1 Sar. 8:46.
KADA KA DAINA TSEREN DON KA YI TUNTUƁE
5, 6. (a) Me ya sa Kirista ba shi da “dalilin tuntuɓe,” kuma me zai taimaka masa ya “tashi” sa’ad da ya faɗi? (b) Me ya sa wasu ba sa tashiwa sa’ad da suka yi tuntuɓe?
5 Matakan da muka ɗauka sa’ad da muka yi tuntuɓe ko kuma muka faɗi suna nuna halinmu. Wasu mutane da suka yi tuntuɓe ko faɗi sun tuba kuma sun ci gaba da bauta wa Allah. Wasu kuma sun ƙi tuba. Littafin Misalai 24:16 ya ce: “Mai-adalci ya kan fāɗi so bakwai, ya sake tashi kuma: Amma masifa ta kan kāda mugu.”
6 Jehobah ba zai ƙyale waɗanda suke dogara gare shi su yi tuntuɓe, ko kuma su faɗi har ba za su iya tashi kuma su bauta masa ba. Muna da tabbaci cewa zai taimaka mana mu “tashi” don mu ci gaba da bauta masa. Jehobah ya san muna ƙaunarsa, amma ya san cewa miyagu ba sa son su tashi. Waɗannan mutanen ba sa neman taimakon mutanen Allah da na ruhu mai tsarki, ko kuma suna ƙin taimakon. Littafi Mai Tsarki ya ce waɗanda suke ƙaunar dokar Jehobah ba su da “dalilin tuntuɓe.” Hakan yana nufin cewa muna iya sake soma yin tseren rai madawwami.—Karanta Zabura 119:165.
7, 8. Ta yaya mutum zai samu tagomashin Allah ko idan ya “faɗi”?
7 A wasu lokatai, mutum yakan yi zunubi domin kasawarsa, kuma yana iya yin hakan a kai a kai. Amma, shi mai adalci ne a gaban Jehobah idan ya ci gaba da ‘tashiwa’ sa’ad da ya yi tuntuɓe, wato, ya tuba da gaske kuma ya yi ƙoƙari ya yi abin da ya dace. Muddin Isra’ilawa na dā sun tuba daga zunubansu, Allah yana ɗaukansu a matsayin masu adalci. (Isha. 41:9, 10) Littafin Misalai 24:16 bai nanata kurakuran da muke yi ba, amma ya nuna cewa Jehobah zai taimaka mana mu “tashi.” (Karanta Ishaya 55:7.) Jehobah Allah da Yesu Kristi sun tabbata cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu, kuma suna ƙarfafa mu mu “tashi.”—Zab. 86:5; Yoh. 5:19.
8 Idan maguji ya yi tuntuɓe ko kuma ya faɗi a gudun dogon zango, yana iya tashi da sauri kuma ya ci gaba da tseren. Ba mu san ‘ranar da sa’ar’ da za mu gama tseren rai madawwami da muke yi ba. (Mat. 24:36) Amma, idan muka yi ƙoƙari don kada mu yi tuntuɓe, zai yi mana sauƙi mu ci gaba da tseren kuma mu gama shi. Ta yaya za mu guji yin tuntuɓe?
ABUBUWAN DA ZA SU IYA SA MU TUNTUƁE
9. Waɗanne abubuwa biyar ne za mu tattauna?
9 Za mu tattauna abubuwa guda biyar da za su iya sa mu tuntuɓe. Abubuwan su ne kasawarmu da sha’awoyinmu da rashin adalci daga ’yan’uwa da ƙunci ko tsanani da kuma ajizancin wasu mutane. Idan ka yi tuntuɓe, ka tuna cewa Jehobah mai haƙuri ne sosai kuma ba zai yasar da kai nan da nan ba.
10, 11. Wace kasawa ce Dauda ya yi fama da ita?
10 Kasawarmu tana kama da duwatsu da ke kan hanya. Za mu iya koyon darasi daga kasawar Sarki Dauda da kuma manzo Bitrus. Kasawar Dauda ita ce rashin kame kansa, kuma ta manzo Bitrus ita ce jin tsoron mutane.
11 Rashin kame kansa ya sa Sarki Dauda ya yi zina da Bath-sheba. Daga baya, ya kusan kai wa Nabal wanda ya zage shi hari. Ko da yake a wasu lokatai ya yi abubuwa ba tare da yin la’akari sosai ba, amma, bai daina yin ƙoƙari ya faranta wa Jehobah rai ba. Mutane sun taimaka masa ya “tashi” bayan ya yi kuskure.—1 Sam. 25:5-13, 32, 33; 2 Sam. 12:1-13.
12. Ta yaya Bitrus ya ci gaba da yin tsere duk da cewa ya yi tuntuɓe?
12 Bitrus ya ji tsoron mutane, duk da haka ya kasance da aminci ga Yesu da kuma Jehobah. Alal misali, ya yi musun sanin Yesu har sau uku. (Luk 22:54-62) A wani lokaci kuma, ya nuna cewa Kiristoci Yahudawa sun fi ’yan Al’ummai marasa kaciya daraja. Bulus ya yi wa Bitrus gargaɗi sosai don abin da ya yi bai dace ba, kuma wasu a cikin ikilisiya suna iya yin koyi da shi. (Gal. 2:11-14) Shin Bitrus ya yi fushi don an yi masa gargaɗi kuma ya daina tseren rai? A’a. Ya yi tunani sosai a kan abin da Bulus ya gaya masa, ya yi gyara kuma ya ci gaba da yin tseren.
13. Ta yaya kasawa zai sa mutum tuntuɓe?
13 Rashin lafiya yana iya jawo mana matsala a rayuwa. Hakan ya sa wasu sun daina yin tseren rai. Alal misali, bayan shekara 17 da wata ’yar’uwa a ƙasar Japan ta yi baftisma sai ta soma rashin lafiya mai tsanani. Ta mai da hankali ainun ga rashin lafiyarta, kuma hakan ya sa ta daina ƙwazo a ibadarta ga Jehobah. Sai dattawa biyu suka ziyarce ta kuma suka ƙarfafa ta. Hakan ya sa ta sake soma halartar taro. Ta ce, “Na zub da hawaye domin ’yan’uwa sun gai da ni sosai.” ’Yar’uwarmu ta sake soma tseren rai.
14, 15. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da muke fama da mugun sha’awoyi? Ka ba da misali.
14 Mutane da yawa sun yi tuntuɓe saboda sha’awoyinsu. Idan mun fuskanci gwaji don sha’awoyinmu, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da yin tunani da kuma aikata daidai da ƙa’idojin Allah. Yesu ya ce idan idonmu ko kuma hannunmu yana sa mu tuntuɓe, mu ‘cire shi mu yar.’ Ya kamata mu kawar da tunani ko kuma ayyuka na lalata da za su iya sa mu daina yin tseren rai.—Karanta Matta 5:29, 30.
15 Wani ɗan’uwa ya ce ya daɗe yana fama da sha’awar daudanci. Ko da yake iyayensa Shaidun Jehobah ne kuma sun koya masa gaskiya, ya ce: “A koyaushe ina jin na yi dabam da sauran mutane, kuma ba na sake jiki idan ina tare da su.” Sa’ad da yake ɗan shekara 20, shi majagaba na kullum ne da kuma bawa mai hidima. Sai ya yi kuskure mai tsanani, aka yi masa horo, kuma dattawa sun taimaka masa. Ya yi addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya yi ƙoƙari ya taimaka wa mutane. Dukan waɗannan abubuwa sun taimaka masa ya ci gaba da yin tseren rai. Bayan shekaru da yawa, sai ya ce: “A wasu lokatai ina yin waɗannan sha’awoyi, amma ba na barin su su shawo kaina. Na koya cewa Jehobah ba zai ƙyale a gwada ka da abin da ya fi ƙarfinka ba. Saboda haka, na gaskata cewa Allah yana ganin zan iya tsayayya wa gwajin.” Wannan ɗan’uwa ya kammala da cewa: “A cikin sabuwar duniya, zan samu lada don famar da nake yi da sha’awoyina. Zan ci gaba da yin hakan har sai lokacin. Ya ƙudura niyya ya ci gaba da yin tseren rai.
16, 17. (a) Mene ne ya taimaki wani ɗan’uwa da yake ganin an yi masa rashin adalci? (b) Mene ne ya kamata mu tuna don kada mu yi tuntuɓe?
16 Muna iya yin tuntuɓe don rashin adalci da wasu ’yan’uwa suka yi mana. Wani ɗan’uwa da dattijo ne a dā a ƙasar Faransa yana ganin an yi masa rashin adalci, kuma hakan ya sa shi baƙin ciki. Sai ya daina halartar taro da yin wa’azi. Dattawa biyu suka ziyarce shi, kuma suka saurare shi yayin da yake bayyana musu abin da yake ganin ya faru. Suka ƙarfafa shi ya dogara ga Jehobah, kuma suka tuna masa cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne mutum ya faranta wa Allah rai. Ya bi gargaɗinsu kuma ba da daɗewa ba, ya sake soma yin tseren rai.
17 Ya kamata dukanmu mu tuna cewa Yesu Kristi ne Allah ya naɗa Shugaban ikilisiya, kuma bai kamata mu ƙyale abin da ’yan Adam ajizai suke yi ya dame mu ba. Idanun Yesu suna kama da “harshen wuta.” Ya san dukan abin da ke faruwa a cikin ikilisiya fiye da mu. (R. Yoh. 1:13-16) Alal misali, wataƙila abin da muke ganin cewa rashin adalci ne a cikin ikilisiya ba hakan ba ne. Mai yiwuwa, ba mu fahimci abin da ya faru ba ko kuma ba mu san dalilin da ya sa hakan ya faru ba. Yesu yana magance matsalolin ikilisiya a hanya da kuma lokacin da ya dace. Saboda haka, bai kamata mu ƙyale abin da wani Kirista ya yi ya sa mu daina yin tseren rai ba.
18. Ta yaya za mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar ƙunci ko tsanantawa?
18 Abubuwa biyu kuma da ke sa mutane tuntuɓe su ne, ƙunci ko tsanantawa da kuma ajizancin wasu a cikin ikilisiya. A cikin labarinsa na mutum wanda ya shuka iri, Yesu ya ce wasu mutane za su yi tuntuɓe don sun fuskanci “ƙunci ko tsanani.” Iyalinmu da maƙwabtanmu ko kuma gwamnati za su iya sa mu fuskanci ƙunci ko kuma su tsananta mana don imaninmu. Mutum yakan yi tuntuɓe musamman idan “ba shi da asali a cikinsa,” wato, idan bangaskiyarsa ta raunana. (Mat. 13:21) Amma, idan mun ƙudura niyya mu ci gaba da kusantar Jehobah, saƙo na Mulki zai taimaka mana mu kasance da bangaskiya sosai. Sa’ad da kake fuskantar matsaloli, ka yi bimbini a kan abubuwan da suka cancanci yabo. (Karanta Filibiyawa 4:6-9.) Jehobah zai ƙarfafa mu mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar gwaji, don kada mu yi tuntuɓe kuma mu daina tseren rai.
19. Mene ne zai taimaka mana don kada laifin da wani ya yi mana ya sa mu tuntuɓe?
19 Wasu sun daina bauta wa Jehobah don ajizancin wasu mutane. Ko kuma sun yi tuntuɓe domin wasu sun yi abubuwan da suka dame su a zuciya. (1 Kor. 8:12, 13) Idan wani ya ɓata mana rai, shin za mu yi fushi har mu daina bauta wa Allah? Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi Kiristoci su daina shar’anta mutane, amma su riƙa gafartawa kuma kada su nace wa ra’ayinsu. (Luk 6:37) Idan kana ganin wani ya ɓata maka rai, ka tambayi kanka: ‘Shin ina shar’anta mutane bisa yadda na fi son a yi abubuwa? Zan daina bauta wa Jehobah domin ajizancin ’yan’uwana? Ƙaunarmu ga Jehobah za ta iya taimaka mana mu ci gaba da yin tseren rai har ƙarshe.
KA GUJI YIN TUNTUƁE KUMA KA YI TSERE DA JIMIRI
20, 21. Mene ne ka duƙufa za ka yi, yayin da muke tseren rai?
20 Shin ka duƙufa cewa za ka gama tseren? (2 Tim. 4:7, 8) Idan amsarka E ce, wajibi ne ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Ya kamata kuma ka riƙa yin bincike da bimbini domin ka san irin abubuwan da za su iya sa ka tuntuɓe. Ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhunsa mai tsarki don ka samu ƙarfi. Kada ka manta cewa idan muka yi tuntuɓe, za mu iya sake tashiwa kuma mu ci gaba da yin tseren har ƙarshe. Za mu iya koyon darasi daga kurakuranmu domin mu yi tseren rai da kyau.
21 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna bukatar mu yi tseren har ƙarshe idan muna son mu samu ladar, wato rai madawwami. Yayin da muke tseren, Jehobah zai ba mu “salama mai-yawa.” (Zab. 119:165) Zai ci gaba da taimaka mana yanzu, kuma zai ba mu lada madawwamiya idan muka ƙarasa tseren.—Yaƙ. 1:12.