Ka Kusaci Allah
Za Ka Iya Samun “Sanin Allah”
JEHOBAH ALLAH ya ba mu damar neman wata dukiya mai tamanin gaske, kuma yana son mu sami wannan dukiyar. Wannan dukiyar ba ta kawo arziki na kuɗi, amma tana ba da abin da dukan kuɗin da ke duniya ba zai iya saye ba, wato, kwanciyar hankali, wadar zuci da kuma rayuwa mai gamsarwa. Mece ce wannan dukiyar? Kalmomin Sarki Sulemanu mai hikima da aka rubuta a Misalai 2:1-6 sun bayyana ko mece ce ce.
Sulemanu ya nuna cewa wannan dukiyar ita ce “sanin Allah,” wato, sanin gaskiya game da Allah da kuma manufofinsa kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana. (Aya ta 5) Wannan dukiyar tana da fannoni da dama.
Koyarwa ta gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyi kamar su: Mene ne sunan Allah? (Zabura 83:18) Mene ne yake faruwa sa’ad da mutum ya mutu? (Zabura 146:3, 4) Me ya sa muke wanzuwa? (Farawa 1:26-28; Zabura 115:16) Hakika, amsoshin waɗannan tambayoyin suna da muhimmanci sosai, ko ba haka ba?
Shawara mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana hanya mafi kyau na yin rayuwa. Ta yaya za ka sa aurenka ya dawwama? (Afisawa 5:28, 29, 33) Ta yaya za ka yi renon yara don su kasance masu halaye mai kyau? (Kubawar Shari’a 6:5-7; Afisawa 6:4) Ta yaya za ka iya samun farin ciki a rayuwa? (Matta 5:3; Luka 11:28) Samun shawara mai amfani a kan waɗannan batutuwa yana da muhimmanci sosai, ko ba haka ba?
Sanin Allah da kuma halinsa. Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai iya ba da cikakken bayani na ainihi game da Allah. Mene ne kamanninsa? (Yohanna 1:18; 4:24) Ya damu da mu kuwa? (1 Bitrus 5:6, 7) Mene ne halayensa na musamman? (Fitowa 34:6, 7; 1 Yohanna 4:8) Akwai abin da za a iya kwatantawa da tabbataccen bayanin da muke da shi game da Mahaliccinmu?
Hakika, “sanin Allah” dukiya ce mai tamani sosai. Ta yaya za ka iya samun ta? Mun samu ƙarin haske a Misalai sura 2 aya ta 4, inda Sulemanu ya kwatanta wannan sanin da “ɓoyayyun dukiya.” Ka yi tunanin wannan: Dukiyar da ke ɓoye ba za ta iya faɗawa hannun ragwaye ba. Muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu same ta. Hakan yake da sanin Allah. A alamance, wannan dukiyar tana ɓoye a cikin Littafi Mai Tsarki. Muna bukatar mu yi aiki tuƙuru idan muna son mu same ta.
Sulemanu ya bayyana abin da muke bukatar mu yi don mu samu “sanin Allah.” Kalmomin nan, “karɓi zantattukana” da “maida zuciyarka” sun nuna cewa muna bukatar mu kasance da zuciya mai biyayya. (Ayoyi 1, 2) Kalmomin nan, “tada murya,” “neme” da kuma “biɗe” sun nuna cewa muna bukatar mu yi aiki tuƙuru, domin mu nuna ƙwazo da basira. (Ayoyi 3, 4) Don mu samu wannan dukiyar, muna bukatar mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, kuma mu yi hakan da sahihiyar zuciya.—Luka 8:15.
Idan muka ɗauki irin waɗannan matakan, Jehobah zai taimaka mana mu samu dukiyar. “Ubangiji yana bada hikima,” in ji aya ta 6. Da taimakon Allah ne kaɗai za mu fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki sosai. (Yohanna 6:44; Ayyukan Manzanni 16:14) Ka kasance da tabbacin nan: Idan ka bincika Kalmar Allah da sahihiyar zuciya, za ka samu “sanin Allah,” wato, dukiyar da za ta kyautata rayuwarka fiye da yadda kake zato.—Misalai 2:10-21.a
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah a dukan duniya suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki kyauta da waɗanda suke son su fahimci Littafi Mai Tsarki. Me zai hana ka tuntuɓe su a yankinka ko kuwa ka rubuta zuwa ga adireshin da ya dace a shafi na 4?