Ta Yaya Iyaye Maza Za Su Kusaci ’Ya’yansu Maza?
“BABA, yaya aka yi ka san dukan waɗannan abubuwan?” Ɗanka ya taɓa yi maka irin wannan tambayar ba zata? A lokacin, mai yiwuwa ka yi alfahari cewa kai mahaifi ne. Amma idan ɗanka ya ɗauki matakin da ya wuce hakan, wato, idan ya yi amfani da shawara mai kyau da ka ba shi kuma ya amfana, babu shakka zuciyarka za ta cika da farin ciki.a—Misalai 23:15, 24.
Amma da shigewar shekaru, ƙauna da darajar da ɗanka yake nuna maka suna nan daram? Ko kuma kana ganin cewa yayin da yake girma, darajar da yake ba ka tana ragewa? Ta yaya ne za ka kasance da dangantaka ta kud da kud ɗanka yayin da yake girma daga yaro zuwa mutum? Da farko, bari mu duba wasu kaluɓalen da iyaye maza suke fuskanta.
Sanannun Ƙalubale Guda Uku
1. RASHIN LOKACI: A ƙasashe da yawa, iyaye maza ne suke fita neman yawancin abin da iyalin za ta ci. Sau da yawa, irin aikin da suke yi yana sa su bar gida tun daga safiya har yamma. A wasu wurare, iyaye maza suna amfani da ɗan ƙaramin lokaci ne suna hira da ya’yansu. Alal misali, a wani bincike da aka yi a Faransa a kwanan nan, an gano cewa iyaye maza suna amfani da ƙasa da minti 12 a kowace rana wajen kula da ’ya’yansu.
ABIN DA ZA KA YI TUNANI A KAI: Minti nawa ne kake yi da ɗanka? A cikin mako ɗaya ko biyu masu zuwa, ka rubuta adadin lokacin da ka tattauna da shi a kowace rana. Sakamakon zai iya ba ka mamaki.
2. RASHIN KAFA MISALI MAI KYAU: Wasu mazan ba su shaƙu da mahaifinsu ba. “Ban taɓa samun isashen damar tattaunawa da mahaifina ba,” in ji Jean-Marie, wanda ke zaune a Faransa. Ta yaya hakan ya shafi Jean-Marie? “Hakan ya haddasa matsalolin da ban taɓa zato ba,” in ji shi. “Alal misali, yin tattaunawa mai ma’ana da ’ya’yana maza yana yi mini wuya.” A wasu yanayin, maza sun san mahaifinsu sosai, amma dangantakar da ke tsakanin mahaifi da ɗa ta lalace. Philippe, ɗan shekara 43, ya ce: “Yana yi wa mahaifina wuya ya nuna mini ƙauna. A sakamakon haka, sai da na dage sosai kafin na soma nuna ƙauna ga ɗana.”
ABIN DA ZA KA YI TUNANI A KAI: Kana jin cewa dangantakarka da mahaifinka ce ta shafi yadda kake bi da ɗanka? Ka taɓa ganin cewa kana bin halaye masu kyau ko marasa kyau na mahaifinka. Ta yaya?
3. RASHIN SHAWARA MAI KYAU: A wasu al’adu, ba a ɗaukan nauyin da mahaifi yake da shi na renon yara da muhimmanci. “A inda na girma, mutane suna ganin cewa mata ne suke da nauyin yin renon yara,” in ji Luca wanda ya girma a wata ƙasa a Yammancin Turai. A wasu al’adun kuma, an ƙarfafa iyaye maza su kasance masu horo. Alal misali, George ya girma ne a wata ƙasa a Afirka. Ya ce: “A al’adarmu, iyaye maza ba sa wasa da ’ya’yansu domin suna ganin yin hakan zai rage ikon da mahaifin yake da shi. Saboda haka, yin hira tare da ɗana yana yi mini wuya domin ina ganin hakan zai rage ikon da nake da shi a matsayina na mahaifi.”
ABIN DA ZA KA YI TUNANI A KAI: A yankinku, wane matsayi ne ake son iyaye maza su ɗauka? An koya musu su ɗauki yin renon yara a matsayin aikin mata ne? Ana ƙarfafa iyaye maza su nuna ƙauna ga ’ya’yansu, ko kuma ana ganin cewa yin hakan bai dace ba?
Idan kai mahaifi ne da ke fuskantar ɗaya daga cikin waɗannan kaluɓalen ko kuma fiye da hakan, ta yaya ne za ka yi nasara? Ka yi la’akari da waɗannan shawarwarin da ke gaba.
Ka Soma Tun Ɗanka Yana Ƙarami
’Ya’ya maza suna da halin son yin koyi da mahaifinsu. Saboda haka, tun ɗanka yana ƙarami, ka yi amfani da sha’awar nan da ɗanka yake da ita na yin koyi da kai. Ta yaya za ka iya yin hakan? Kuma a yaushe ne za ka iya samun lokacin kasancewa tare da shi?
A duk lokacin da ya yiwu, ka yi aiki tare da ɗanka a hidimominka na yau da kullum. Alal misali, idan kana aikace-aikacen gida, ka sa ya taimake ka. Idan kana shara, ka ba ɗanka ’yar ƙaramar tsintsiya ya taimake ka kuma idan kana haƙa rami, ka ba shi ƙaramin shebur domin ku yi aikin tare. Babu shakka zai yi farin cikin yin aiki tare da jaruminsa, wato, mahaifinsa! Mai yiwuwa aikin ba zai tafi yadda kake so ba; amma za ka ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninku, kuma za ka koya masa tarbiyya mai kyau game da aiki. Tun da daɗewa, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa iyaye maza su yi aiki tare da ’ya’yansu a kowace rana kuma su yi amfani da waɗannan lokatan su tattaunawa da su kuma su koyar da su. (Kubawar Shari’a 6:6-9) Wannan shawara ce mai kyau a yau.
Ƙari ga yin aiki tare da ɗanka, ka nemi lokacin yin wasa tare da shi. Yin wasa da shi zai ba ka zarafin cim ma abubuwa da dama. Bincike ya nuna cewa sa’ad da iyaye maza suka yi wasa da ’ya’yansu ƙanana, suna ƙarfafa su su zama masu son koyan sababbin abubuwa kuma su kasance masu ƙarfin zuciya.
Yin wasa tsakanin mahaifi da ɗa yana kuma da muhimmanci sosai. “A lokacin wasa ne yaro ya fi tattaunawa da mahaifinsa,” in ji Michel Fize wani mai yin bincike. A lokacin da suke wasa, mahaifi yana iya nuna wa ɗansa ƙauna ta wurin kalami da kuma abubuwan da yake yi. Idan ya yi hakan, yana koya wa ɗansa yadda ake nuna ƙauna. “Sa’ad da ɗana yake ɗan ƙarami, muna yin wasa tare,” in ji André, wani mahaifi da ke zaune a Jamus. “Ina rungumar sa, kuma na koya masa cewa ya kamata ya riƙa nuna mini ƙauna.”
Lokacin barci wani zarafi ne kuma da mahaifi yake da shi na ƙarfafa dangantakarsa da ɗansa. Ka riƙa karanta masa labari a kai a kai, kuma ka saurara sa’ad da yake faɗin abubuwan da suke faranta masa rai da kuma waɗanda ke damun sa a ranar. Idan ka yi hakan, zai riƙa tattaunawa da kai cikin sauƙi yayin da yake girma.
Ka Yi Abubuwan da Kai da Ɗanka Kuke Sha’awa
Wasu matasa maza ba sa jin daɗin tattaunawa da mahaifinsu. Idan ɗanka yana gudun amsa tambayoyinka, kada ka kammala cewa ba ya son tattaunawa da kai ba. Wataƙila zai so ya faɗi abin da ke zuciyarsa idan ka tattauna da shi a hanyar da yake so.
Akwai lokatan da Jacques, wani mahaifin da ke zama a Faransa, ya samu matsala wajen tattaunawa da ɗansa Jérôme. Amma maimakon ya tilasta ma ɗansa ya yi magana, ya canja yadda yake hulɗa da shi, wato, ya soma buga ƙwallo da shi. “Bayan mun gama motsa jiki, muna zama a kan ciyawa kuma mu ɗan huta. A lokacin ne ɗana yake gaya mini abin da ke zuciyarsa. Ina ganin kasancewarmu tare da kuma sanin cewa ni da shi ne kaɗai ke wurin, ya sa muka ƙulla dangantaka ta musamman a tsakanin mu,” in ji Jacques.
Amma idan ɗanka ba ya son wasannin motsa jiki fa? André ya tuna lokacin da shi da ɗansa suke zama tare su kalli taurari. André ya ce: “Muna zama a kan kujeru a waje da dare cikin ɗari. Mu lulluɓe kanmu, riƙe da kofin shayi a hannunmu muna kallon sama. Kuma mu tattauna game da Wanda ya halicci taurari, game da abin da ya shafi kowannenmu, kuma muna tattauna kusan dukan batutuwan da ya kamata.”—Ishaya 40:25, 26.
Amma, idan ba ka son yin wasu abubuwan da ɗanka yake sha’awa fa? A wannan yanayin, mai yiwuwa kana bukatar ka yi waɗannan abubuwan da ba ka so. (Filibiyawa 2:4) “Ina sha’awar wasannin motsa jiki sosai fiye da Vaughan, ɗana. Yana son jiragen sama da kwamfuta. Saboda haka, na fara sha’awar waɗannan abubuwan, ina kai shi wurin da ake wasa da jiragen sama kuma muna wasan jirgin sama da ke cikin kwamfuta. Ina jin cewa Vaughan yana gaya mini abubuwan da ke zuciyarsa ne domin muna yin abubuwan da muke jin daɗin su tare,” in ji Ian wanda ke zaune a Afirka ta Kudu.
Ka Gina Gaba Gaɗinsa
“Baba, duba!” Yaronka ya taɓa gaya maka haka sa’ad da ya ƙware wajen yin wani abu? Idan shi matashi ne yanzu, har ila yana neman amincewarka a fili? Mai yiwuwa ya daina. Amma hakan yana da muhimmanci a gare shi idan kana son ya zama mutum mai hikima.
Ka lura da misalin da Jehobah Allah da kansa ya kafa a yadda ya bi da ɗaya daga cikin ’ya’yansa. Sa’ad da Yesu yake dab da soma wani sashe na musamman na rayuwarsa a duniya, Allah ya bayyana ƙaunar da yake yi masa a fili, ya ce: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.” (Matta 3:17; 5:48) Babu shakka, kai ke da hakkin horar da ɗanka da kuma koyar da shi. (Afisawa 6:4) Amma kana neman zarafin furta farin cikinka game da abubuwan da ya ce da kuma waɗanda ya yi?
Yana yi wa wasu maza wuya su bayyana amincewarsu da kuma ƙaunarsu a fili. Mai yiwuwa sun girma ne a cikin iyalin da iyayensu suka fi mai da hankali ga kurakurai maimakon abin da suke iya yi. Idan haka yanayinka yake, kana bukatar ka ƙoƙarta sosai don ka gina gaba gaɗin ɗanka. Ta yaya za ka yi hakan? Luca, wanda aka yi ƙaulinsa ɗazu, yana yin aikace-aikacen cikin gida tare da ɗansa Manuel ɗan shekara 15. Luca ya ce: “A wasu lokatai, ina gaya wa Manuel ya soma wani aiki da kansa kuma cewa zan taimaka masa idan yana bukatata. Yawancin lokaci, yana gama aikin da kansa. Nasarar da ya yi tana faranta ransa kuma tana ƙara gina gaba gaɗinsa. Sa’ad da ya yi nasara, ina yaba masa. Sa’ad da bai yi abin a yadda yake zato ba, duk da haka, ina yaba masa.”
Kai ma kana iya gina gaba gaɗin ɗanka ta wajen taimaka masa ya cim ma maƙasudansa masu muhimmanci a rayuwa. Amma, idan ɗanka bai cim ma maƙasudansa a lokacin da kake zato ba fa? Ko kuma, idan maƙasudansa masu kyau ne amma sun sha bambam da waɗanda kake so fa? Idan haka ne, wataƙila kana bukatar canja ra’ayinka. Jacques, wanda aka yi ƙaulinsa ɗazu ya ce: “Ina taimaka wa ɗana ya kafa maƙasudan da zai iya cim ma. Kuma, ina ƙoƙarin tabbatar da cewa maƙasudan nasa ne, ba nawa ba. Bayan haka ina tuna wa kaina cewa yana bukatar cim ma maƙasudansa daidai ƙarfinsa.” Idan ka saurari ra’ayoyin ɗanka, ka yaba masa domin abubuwa masu kyau da ya yi, kuma ka ƙarfafa shi ya sha kan kasawarsa, za ka taimaka masa ya cim ma maƙasudansa.
Hakika, za ku fuskanci matsaloli da kaluɓale a dangantakarku. Amma a ƙarshe, ɗanka zai so ya ci gaba da kasancewa kusa da kai. Balle ma, wane ne ba zai so ya kasance kusa da wanda yake taimaka masa ya yi nasara ba?
[Hasiya]
a Ko da yake wannan talifin ya mai da hankali ne ga dangantaka ta musamman da ke tsakanin iyaye maza da ’ya’yansu maza, ƙa’idodin da aka tattauna a wannan talifin sun shafi dangantakar da ke tsakanin iyaye maza da ’ya’yansu mata.