Ka Kusaci Allah
Uba da Babu Kamarsa Matta 3:16, 17
“BABA.” Kalmomi kaɗan ne suka fi ta motsa ran ’yan’ Adam. Uba da yake ƙaunar ’ya’yansa da gaske yana taimakon su su yi nasara. Da kyakkyawan dalili aka kira Jehobah cikin Littafi Mai Tsarki, “Uba.” (Matta 6:9) Wane irin Uba ne Jehobah? Domin mu amsa wannan tambayar, bari mu bincika kalmomin da Jehobah ya furta game da Yesu a lokacin baftismarsa. Ban da haka, yadda uba yake yi wa ’ya’yansa magana zai bayyana iri halinsa.
A watan Oktoba shekara ta 29 A.Z., Yesu ya tafi Kogin Urdun a yi masa baftisma. Littafi Mai Tsarki ya faɗi abin da ya faru: “Yesu kuwa, sa’anda aka yi masa baftisma, ya fita nan da nan daga cikin ruwa: ga kuwa sammai suka buɗe masa, ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya yana zuwa bisansa; ga kuwa murya daga cikin sammai, ta ce, Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.”a (Matta 3:16, 17) Waɗannan kalmomi da Jehobah kansa ya furta, sun nuna mana irin halayen Jehobah. Ka lura da abubuwa uku da Jehobah ya furta game da Ɗansa.
Da farko, ya yi amfani da waɗannan kalmomi “wannan Ɗana ne,” Jehobah yana cewa ne, ‘ina alfahari ni ne Ubanka.’ Uba mai fahimi yana biyan bukatar yaransa kuma yana mai da musu hankali. Yara suna so a tabbatar musu cewa kowannen su yana da tamani cikin iyali. Ka yi tunanin yadda wannan ya shafi Yesu, ko da yake ya girma, amma Ubansa ya nuna masa cewa yana ƙaunarsa!
Na biyu, da ya kira Ɗansa “ƙaunatacena,” Jehobah ya nuna a fili cewa yana ƙaunar Yesu. Wato, Uban yana cewa ne, ‘ina ƙaunarka.’ Uban kirki yana gaya wa yaransa cewa yana ƙaunarsu sosai. Irin waɗannan kalmomi tare da nuna ƙauna da ta dace na taimakon yara su yi girma da kyau. Lallai ya motsa zuciyar Yesu da ya ji muryar Ubansa yana cewa yana ƙaunarsa!
Na uku, Jehobah ya nuna cewa ya amince da Ɗansa sa’ad da ya furta kalmomi nan “raina ya ji daɗi ƙwarai.” Kamar dai Jehobah yana cewa, ‘Ɗana, na yi farin ciki da abin da ka yi.’ Uban kirki yana neman zarafi na nuna wa yaransa cewa yana farin ciki da abubuwa masu kyau da suka ce ko kuma suka yi. Yara suna samun ƙarfafa kuma suna kasancewa da gaba gaɗi sa’ad da iyayensu suka nuna musu ƙauna. Babu shakka, Yesu ya ƙarfafa sa’ad da ya ji cewa Ubansa ya amince da shi!
Hakika, babu Uba kamar Jehobah. Kana son ka samu irin wannan uba? Idan haka ne, ka san cewa za ka iya ƙulla dangantaka da Jehobah. Idan kana da bangaskiya ka koyi game da shi kuma ka yi ƙoƙari ka yi nufinsa, zai taimake ka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yaƙub 4:8) Babu abin da zai sa ka kasance da kwanciyar rai fiye da ƙulla dangantaka na kud da kud da Uba mafi kyau, Jehobah Allah.
[Hasiya]
a A Linjilar Luka, Jehobah ya yi amfani da wakilin sunan nan “kai,” ya ce: “Kai ne Ɗana ƙaunatacce: da kai raina ya ji daɗi ƙwarai.”—Luka 3:22.