Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/15 pp. 3-7
  • ‘Ɗan Yana A Shirye ya Bayyana Uban’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ɗan Yana A Shirye ya Bayyana Uban’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YESU YA BAYYANA UBAN A HANYA TA MUSAMMAN
  • YADDA YESU YA BAYYANA UBANSA
  • ƊAN YA YARDA YA BAYYANA UBAN
  • KA YI KOYI DA YESU TA WAJEN TAIMAKA WA MUTANE SU SAN JEHOBAH
  • Waɗanne Irin Halaye Ne Yesu Yake da Su?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Kana Ɗaukan Jehobah a Matsayin Ubanka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehobah Ubanmu Yana Kaunar Mu Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/15 pp. 3-7

‘Ɗan Yana A Shirye ya Bayyana Uban’

“Ba kuwa wanda ya sansance ko wanene Uban, sai Ɗan, da dukan wanda Ɗan ya yi nufi shi bayyana masa.”—LUK 10:22.

MECE CE AMSARKA?

․․․․․

Me ya sa Yesu ne ya fi dacewa ya bayyana halayen Ubansa?

․․․․․

Ta yaya Yesu ya bayyana wa mutane halayen Ubansa?

․․․․․

A waɗanne hanyoyi ne za ka iya yin koyi da Yesu kuma ka bayyana halayen Uban ga mutane?

1, 2. Wace tambaya ce take wa mutane da yawa wuyar amsawa, kuma me ya sa?

‘WANE ne Allah?’ Wannan tambayar tana wa mutane da yawa wuyar amsawa. Alal misali, yawancin mutane da suke da’awa su Kiristoci ne sun gaskata cewa Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ne, sun kuma ce ba zai yiwu a fahimci wannan koyarwar ba. Wani mawallafi wanda limami ne ya ce: “Ba za a iya bayyana wannan koyarwar ba domin akwai wasu abubuwa da ɗan Adam ba zai iya fahimta ba.” Wasu da suka gaskata da ra’ayin bayyanau sun ce babu Allah. Sun ce dukan halittu masu ban al’ajabi sun bayyana ne farat ɗaya. Charles Darwin bai yi musu cewa Allah bai wanzu ba, amma ya ce: “’Yan Adam ba za su iya fahimtar kome game da Allah ba.”

2 Ko da mene ne suka yi imani da shi, yawancin mutane suna da tambayoyi game da Allah. Amma mutane da yawa sun daina yin tambayoyi game da Allah domin ba sa gamsuwa da amsoshin da ake ba su. Shaiɗan ya “makamtar da hankulan marasa-bada gaskiya.” (2 Kor. 4:4) Shi ya sa yawancin mutane sun rikice kuma ba su san gaskiya game da Allah ba, wato, Uba da kuma Mahaliccin sararin samaniya!—Isha. 45:18.

3. (a) Wane ne ya bayyana mana Mahaliccin? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Duk da haka yana da muhimmanci mutane su san gaskiya game da Allah. Me ya sa? Domin sai dukan waɗanda suka “kira bisa sunan Ubangiji” ne za su samu ceto. (Rom. 10:13) Kira bisa sunan Allah yana nufin cewa za mu san ko wanene Allah da sanin irin halaye da yake su. Yesu Kristi ya koya wa almajiransa wannan gaskiya mai muhimmanci. Ya bayyana musu Uban. (Karanta Luka 10:22.) Me ya sa Yesu ya iya bayyana Uban sosai? Ta yaya Yesu ya yi hakan? Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu wajen bayyana wa mutane Uban? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

YESU YA BAYYANA UBAN A HANYA TA MUSAMMAN

4, 5. Me ya sa Yesu ne ya fi cancanta ya bayyana Ubansa?

4 Yesu ne ya fi cancanta ya taimaki mutane su san Ubansa. Me ya sa? Domin ya riga ya halicci ruhu da ya zo duniya a matsayin Yesu. Shi ne “Ɗa haifaffe kaɗai na Allah.” (Yoh. 1:14; 3:18) Yesu kaɗai ne yake tare da Ubansa kafin a soma halittar sauran abubuwa, saboda haka, ya koyi abubuwa da yawa daga wurin Ubansa. Yayin da suke cuɗanya sosai cikin shekara aru-aru, Yesu ya koyi halayen Ubansa. (Yoh. 5:20; 14:31) Yayin da dangantakarsu ta ƙara ƙarfi, hakan ya sa ƙaunar da suke wa juna ta ƙaru sosai. (Yoh. 5:20; 14:31) Babu shakka, Yesu ya koyi abubuwa da yawa game da halayen Ubansa!—Karanta Kolosiyawa 1:15-17.

5 Uban ya zaɓi Ɗan ya zama kakakinsa, a matsayin “Kalmar Allah.” (R. Yoh. 19:13) Saboda haka, Yesu ne kaɗai aka ba aikin bayyana wa mutane Uban. Ya dace da Yohanna, marubucin Linjila ya kwatanta Yesu wanda shi ne “Kalmar” a matsayin “wanda yake wurin Uba.” (Yoh. 1:1, 18, LMT) Da yake Yohanna ya faɗi hakan, mai yiwuwa yana tunanin al’ada da ake bi a zamaninsa a lokacin cin abinci. Za a sa baƙi biyu su zauna tare don su samu zarafin yin hira da juna. Hakanan ma, kasancewa Ɗan a “wurin Uba” ya sa ya samu zarafin tattaunawa da Uban sosai.

6, 7. Ta yaya dangantaka da ke tsakanin Uban da Ɗan ya ci gaba da ƙaruwa?

6 Dangantaka da ke tsakanin Uban da Ɗan ya ci gaba da ƙaruwa har Ɗan ya zama “abin daular [Allah], kullum.” (Karanta Misalai 8:22, 23, 30, 31.) Sun yi aiki tare kuma Yesu ya koyi halayen Ubansa. Sa’ad da Jehobah ya halicci mala’iku da ’yan Adam, Ɗan ya ga yadda yake bi da kowannensu, kuma hakan ya sa ya ƙara ƙaunar Ubansa da kuma daraja shi.

7 Har ma sa’ad da Shaiɗan ya ƙalubalanci yadda Jehobah yake sarauta, Ɗan ya koyi yadda Jehobah zai nuna ƙauna da adalci da hikima da kuma iko sa’ad da ya fuskanci yanayi mai wuya. Wannan ya taimaki Yesu ya koya yadda zai jimre da matsaloli da zai fuskanta a hidimarsa a duniya.—Yoh. 5:19.

8. Ta yaya labaran Linjila suke taimaka mana mu koya halayen Uban?

8 Yesu ya iya bayyana halayen Uban sosai domin yana da dangantaka ta kud da kud da shi. Hanya mafi kyau da za mu koya halayen Uban ita ce ta wajen koyon abin da Ɗansa makaɗaici ya koyar da kuma yi. Alal misali, shin za mu fahimci ainihin ma’anar kalmar nan “ƙauna” idan mun karanta ta a cikin ƙamus kawai? Da kyar. Amma, idan mun yi tunani game da labarai da ke cikin Littafi Mai Tsarki da suka kwatanta hidimar Yesu, hakan zai taimaka mana mu ga yadda ya kula da mutane kuma za mu fahimci ma’anar furucin nan “Allah shi ne ƙauna.” (1 Yoh. 4:8, 16) Hakan yake da sauran halaye na Allah da Yesu ya bayyana wa almajiransa sa’ad da yake duniya.

YADDA YESU YA BAYYANA UBANSA

9. (a) A waɗanne hanyoyi biyu ne Yesu ya bayyana Ubansa ga almajiransa? (b) Ka ba da misalin da ya nuna yadda Yesu ya bayyana Ubansa ta wajen koyarwarsa.

9 Ta yaya Yesu ya bayyana Uban ga almajiransa da kuma waɗanda daga baya suka zama almajiransa? Ya yi hakan ta hanyoyi biyu: ta wurin koyarwarsa da kuma halayensa. Bari mu fara tattauna koyarwar Yesu. Abin da Yesu ya koya wa mabiyansa ya nuna mana yadda Ubansa yake yin abubuwa, da tunaninsa da kuma yadda yake ji. Alal misali, Yesu ya kamanta Ubansa da mutum mai garken tumaki da ya je neman tunkiyarsa da ta ɓata. Yesu ya ce sa’ad da mutumin ya samo tunkiyar “murna da ya yi bisa gareta ta fi ta bisa kan tassain da taran nan waɗanda ba su ɓace ba.” Me ya sa Yesu ya yi amfani da wannan kwatancin? Ya bayyana: “Hakanan kuma ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.” (Mat. 18:12-14) Mene ne za ka iya koya game da Jehobah daga wannan kwatancin? Ko idan a wasu lokatai kana jin ba ka da amfani ko kuma an manta da kai, ka tuna cewa Ubanmu na samaniya yana ƙaunarka kuma yana kula da kai. A gabansa kana cikin “waɗannan ƙanƙanana.”

10. Yaya Yesu ya bayyana Ubansa ta yadda ya bi da mutane?

10 Hanya ta biyu da Yesu ya bayyana Uban ga almajiransa ita ce ta halinsa. Sa’ad da manzo Filibus ya gaya wa Yesu: “Ka nuna mana Uban,” Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yoh. 14:8, 9) Ga wasu misalai da suka nuna yadda Yesu ya bayyana halayen Ubansa. Sa’ad da wani kuturu ya roƙi Yesu ya warkar da shi, Yesu ya taɓa mutumin da ke “cike da kuturta” kuma ya gaya masa: “Na yarda, ka tsarkaka.” Da mutumin ya warke, ya san cewa Jehobah ne ya ba Yesu ikon warkar da shi. (Luk 5:12, 13) Sa’ad da Li’azaru ya mutu, babu shakka cewa almajiran sun ga cewa Uban mai tausayi ne a lokacin da Yesu “ya ji haushi cikin ruhunsa, yana jin zafi a ransa” kuma “Yesu ya yi kuka.” Ko da yake Yesu ya san cewa zai ta da Li’azaru daga matattu, ya ji zafin rasuwar kamar yadda iyalin Li’azaru da abokansa suka ji. (Yoh. 11:32-35, 40-43) Wataƙila kana da labaran Littafi Mai Tsarki game da Yesu da ka fi so da za su taimaka maka ka ga tausayin da Uban ya nuna.

11. (a) Mene ne Yesu ya bayyana game da Ubansa sa’ad da ya tsarkake haikalin? (b) Me ya sa wannan labarin ya ƙarfafa mu?

11 Mene ne ka koya sa’ad da ka karanta labarin yadda Yesu ya tsarkake haikalin? Ka yi tunani abin da ya faru: Yesu ya tukka bulala ta igiya kuma ya kori mutanen da suke sayar da shanu da tumaki a cikin haikali. Ya watsar da kuɗin ’yan canji kuma ya kifar da teburorinsu. (Yoh. 2:13-17) Wannan matakin da ya ɗauka ya sa almajiransa suka tuna da annabcin da Sarki Dauda ya yi: “Himma domin gidanka ya cika zuciyata.” (Zab. 69:9) Matakin da Yesu ya ɗauka ya nuna cewa yana son ya kāre bauta ta gaskiya. Shin kana ganin cewa Yesu ya nuna halin Jehobah sa’ad da ka karanta wannan labarin? Ya tuna mana cewa Allah yana da ikon cire mugunta daga duniya kuma yana matuƙar son yin hakan. Ka yi tunanin yadda Jehobah yake ji yayin da yake ganin mugunta ko’ina a duniya! Yadda Jehobah da Yesu suke ji game da yanayin yana ƙarfafa mu sosai sa’ad da muke fuskantar rashin adalci!

12, 13. Mene ne za ka iya koya game da Jehobah daga yadda Yesu ya bi da almajiransa?

12 Wani misali na yadda Yesu ya bayyana Ubansa shi ne yadda ya bi da almajiransa. Sun ci gaba da gardama a kan wanda ya fi girma. (Mar. 9:33-35; 10:43; Luk 9:46) Domin Yesu ya yi cuɗanya da Ubansa da daɗewa, ya san yadda Jehobah yake ji game da fahariya. (2 Sam. 22:28; Zab. 138:6) Yesu ya gan yadda Shaiɗan Iblis ya nuna fahariya. Shaiɗan mai son kai ne da yake son matsayi da yin suna. Saboda haka, Yesu ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da ya ga almajiransa da ya koyar suka ci gaba da yin fahariya! Manzanni da ya zaɓa su ma suna da wannan halin! Sun nuna wannan halin har rana ta ƙarshe na rayuwar Yesu a duniya. (Luk 22:24-27) Amma, Yesu ya ci gaba da yi musu gyara a hankali, domin ya san cewa wata rana za su zama masu tawali’u kamar shi.—Filib. 2:5-8.

13 Shin ka ga halin Jehobah daga yadda Yesu ya daidaita halin almajiransa cikin haƙuri? Shin ka koya game da Uban daga abin da Yesu ya ce da kuma yi? Ubansa ba ya yatsar da mutanensa ko da yake suna yin kuskure a ko da yaushe. Sanin halayen Allah yana ƙarfafa mu mu tuba kuma mu yi addu’a cewa Jehobah ya gafarta mana kurakuranmu.

ƊAN YA YARDA YA BAYYANA UBAN

14. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana son ya bayyana Ubansa ga mutane?

14 Sarakuna da yawa suna mallakar mutane ta wajen barinsu a cikin jahilci da kuma ƙin koya musu abubuwa da suke bukatar su sani. Yesu bai yi haka ba, yana son ya taimaki mutane su koya game da Ubansa, shi ya sa ya bayyana musu kome da suke bukatar su sani game da Jehobah. (Karanta Matta 11:27.) Ƙari ga hakan, Yesu ya sa almajiransa su ‘fahimta kuma su san wanda yake mai-gaskiya,’ Jehobah Allah. (1 Yoh. 5:20) Mene ne wannan yake nufi? Yesu ya taimaki mabiyansa su fahimci abin da ya koyar game da Uban. Bai bar mutane cikin duhu game da Ubansa ta wajen koya musu batu mai wuyar fahimta kamar koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba.

15. Me ya sa Yesu bai gaya wa almajiransa dukan abubuwa da ya sani game da Ubansa ba?

15 Shin Yesu ya bayyana dukan abin da ya sani game da Ubansa? A’a. Kuma hakan ya nuna cewa shi mai hikima ne. (Karanta Yohanna 16:12.) Me ya sa? Domin a wannan lokacin, almajiransa ba za su ‘iya ɗaukan’ irin wannan bayani game da Ubansa ba. Amma Yesu ya ce za a bayyana musu ƙarin abubuwa sa’ad da za su samu “mai-taimako,” wato, ruhu mai tsarki, wannan zai yi musu ja-gora ‘cikin dukan gaskiya.’ (Yoh. 16:7, 13) Kamar yadda iyaye masu hikima ba za su gaya wa yaransu wasu abubuwa ba sai yaran sun yi girma, shi ya sa Yesu ya jira har sai almajiransa sun manyanta kuma za su iya fahimtar wasu abubuwa game da Ubansa kafin ya ba su ƙarin bayani. Yesu ya nuna basira don ya san cewa almajiransa ba za su iya tuna dukan abubuwa ba.

KA YI KOYI DA YESU TA WAJEN TAIMAKA WA MUTANE SU SAN JEHOBAH

16, 17. Me ya sa za ka iya bayyana wa mutane halayen Uban?

16 Sa’ad da ka san mutum sosai kuma ka ga cewa yana da hali mai kyau, za ka so ka gaya wa mutane game da shi. Sa’ad da Yesu yake duniya ya gaya wa mutane game da Ubansa. (Yoh. 17:25, 26) Shin zai yiwu mu yi koyi da shi wajen bayyana halayen Jehobah ga mutane?

17 Kamar yadda muka tattauna, Yesu ya san Ubansa sosai. Amma, yana son ya koya wa mutane abubuwan da ya sani, kuma ya sa mabiyansu su fahimci abubuwa masu wuya game da halayen Ubansa. Yesu ya taimaka mana mu san Ubanmu a hanyar da yawancin mutane a yau ba su iya ba. Muna godiya sosai cewa Yesu yana son ya bayyana mana Ubansa ta koyarwarsa da kuma halinsa! Muna alfahari cewa mun san Uban. (Irm. 9:24; 1 Kor. 1:31) Da yake mun yi ƙoƙari mu kusaci Jehobah, shi kuma ya kusace mu. (Yaƙ. 4:8) Saboda haka, muna iya koya wa mutane abin da muka sani game da Jehobah. Ta yaya za mu iya yin hakan?

18, 19. A waɗanne hanyoyi ne za ka iya bayyana wa mutane Uban? Ka bayyana.

18 Muna bukatar mu yi koyi da Yesu don bayyana Uban ta furucinmu da halayenmu. Ya kamata mu tuna cewa mutane da muke haɗuwa da su sa’ad da muke wa’azi ba su san halayen Allah ba. Suna iya kasancewa da ra’ayin da ba daidai ba game da Allah domin an koyar musu ƙarya. Kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, muna iya koya musu abin da muka sani game da sunan Allah da nufinsa don ’yan Adam da kuma halayensa. Kuma wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna taimaka mana mu fahimci halayen Allah a hanyar da ba mu yi ba a dā.

19 Ya kamata mu yi koyi da Yesu kuma mu bayyana halayen Uban ta wurin halinmu. Idan mutane suka ga cewa muna ƙaunar Kristi ta ayyukanmu, suna iya so su ƙulla dangantaka da Yesu da kuma Ubansa. (Afis. 5:1, 2) Manzo Bulus ya ƙarfafa mu mu ‘zama masu-koyi da shi, kamar yadda ya yi kuma da Kristi.’ (1 Kor. 11:1) Gata ne mai kyau mu taimaka wa mutane su san Jehobah ta halinmu! Bari dukanmu mu ci gaba da yin koyi da Yesu ta wajen bayyana wa mutane Uban.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba