Ka Koya Daga Kalmar Allah
Ta Yaya Iyalinka Za ta Kasance Mai Farin Ciki?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Me ya sa aure yake da muhimmanci ga farin cikin iyali?
Jehobah, Allah mai farin ciki, shi ne ya kafa aure. Aure yana da muhimmanci ga farin cikin iyali domin hakan yana sa dangantakar ta kasance na kud da kud kuma a samu yanayi mai kyau na rainon yara. Mene ne ra’ayin Allah game da aure? Allah yana son a ɗaura aure tsakanin mace da namiji kuma auren ya kasance na dindindin. (Luka 2:1-5) Allah yana son mata da miji su kasance da aminci ga juna. (Ibraniyawa 13:4) Jehobah ya yarda Kiristoci su kashe aure kuma su sake yin wani idan ɗaya daga cikin ma’auratan ya yi zina.—Karanta Matta 19:3-6, 9.
2. Yaya ya kamata mata da miji su bi da juna?
Jehobah ya halicci maza da mata domin su taimaka ma juna a aure. (Farawa 2:18) A matsayin shugaban iyali, maigida ne ya kamata ya kasance kan gaba wajen biyan bukatun iyalinsa kuma ya koya musu game da Allah. Ya kamata ya nuna ƙauna irin ta sadaukarwa ga matarsa. Ya kamata mata da miji su nuna ƙauna da daraja ga juna. Tun da dukan maza da mata ajizai ne, gafarta wa juna yana da muhimmanci sosai domin yana kawo farin ciki a aure.—Karanta Afisawa 4:31, 32; 5:22-25, 33; 1 Bitrus 3:7.
3. Ya kamata ka rabu da matarka ne idan ba ka jin daɗin aurenka?
Idan kai da matarka kuna samun matsaloli, ku yi ƙoƙarin bi da juna cikin ƙauna. (1 Korintiyawa 13:4, 5) Kalmar Allah ba ta ce rabuwa ce za ta magance matsalolin da ake samu a aure ba. Amma a matsanancin yanayi, Kirista zai ko za ta iya yanke shawarar rabuwa ko a’a.—Karanta 1 Korintiyawa 7:10-13.
4. Yara, mene ne nufin Allah a gare ku?
Jehobah yana so ku kasance masu farin ciki. Yana ba ku shawara mafi kyau a kan yadda za ku more ƙuruciyarku. Yana son ku amfana daga hikima da ƙwarewar iyayenku. (Kolosiyawa 3:20) Jehobah yana jin daɗin duk wani abin da kuka yi don ku yaba masa.—Karanta Mai-Wa’azi 11:9–12:1; Matta 19:13-15; 21:15, 16.
5. Iyaye, mene ne yaranku suke bukata don su kasance masu farin ciki a rayuwa?
Ya kamata ku yi aiki tuƙuru don ku yi tanadin abinci da wurin kwana da kuma sutura ga yaranku. (1 Timotawus 5:8) Amma don yaranku su kasance masu farin ciki, kuna bukatar ku koya musu su ƙaunaci Allah kuma su koya daga wurinsa. (Afisawa 6:4) Misalin da kuka kafa wajen nuna ƙauna ga Allah zai iya yin tasiri sosai a zuciyar yaranku. Idan umurnin da kuka ba da ya fito ne daga Kalmar Allah, hakan zai iya daidaita tunanin ’ya’yanku sosai.—Karanta Kubawar Shari’a 6:4-7; Misalai 22:6.
Yara za su amfana idan suna samun ƙarfafawa da yabo daga wurin ku iyaye. Suna kuma bukatar gyara da horo. Irin tarbiyyar nan tana kāre su daga halin da zai iya jawo musu baƙin ciki. (Misalai 22:15) Duk da haka, kada horo ya kasance mai tsanani ko kuma da azaba.—Karanta Kolosiyawa 3:21.
Shaidun Jehobah suna wallafa littattafai da dama da aka rubuta musamman don taimaka wa iyaye da kuma yara. An ɗauko batutuwan da ke cikin waɗannan littattafan ne daga Littafi Mai Tsarki.—Karanta Zabura 19:7, 11.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 14 na wannan littafin, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.