Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/1 pp. 22-23
  • An Cece Su Daga Tanderun da ke Cin Wuta!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Cece Su Daga Tanderun da ke Cin Wuta!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Halakar Saduma Da Gwamarata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu Ya Yi Tsayayya da Gwaji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Aka Ɓatar da Aljanna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yesu ya Warkar da Mutane ta Hanyar Mu’ujiza
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/1 pp. 22-23

Don Matasa

An Cece Su Daga Tanderun da ke Cin Wuta!

Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosin, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suka ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.

Shimfiɗar ’yan wasa: Shadrach da Meshach da Abednego da kuma Nebuchadnezzar

Taƙaitawa: An gwada bangaskiyar matasa Ibraniyawa guda uku.

1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA DANIYEL 3:1-30.

Ka kwatanta ƙara dabam-dabam da ka “ji” sa’ad da kake karanta ayoyi 3-7.

․․․․․

Ka kwatanta a zuci yadda wannan tanderu mai ci da wuta yake.

․․․․․

A ganin ka, yaya muryar Nebuchadnezzar take sa’ad da ya ba da umurni cewa a zuga wutar tanderun sau bakwai fiye da yadda aka saba yi? (Sake karanta ayoyi na 19 da kuma 20.)

․․․․․

A zuciyarka, ka kwatanta yadda kamannin mutumi na huɗu da ke cikin tanderun yake. (Sake karanta ayoyi 24 da kuma 25.)

․․․․․

Waɗanne halaye ne ka lura cewa Shadrach da Meshach da kuma Abednego suka nuna sa’ad da suke magana da Nebuchadnezzar a ayoyi 16-18?

․․․․․

2 KA BINCIKA SOSAI.

Ka yi amfani da littattafan bincike da kake da su, ka bincika yadda ake auna kamun, sa’an nan ka lissafa girman gunkin da Nebuchadnezzar ya ƙera. (Sake karanta aya 1.)

․․․․․

Bayan ka karanta ayoyi 19 da 20, da ayoyi 28 da 29, wane irin mutumi ne za ka iya kiran Nebuchadnezzar?

․․․․․

3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .

Girmama shugabanni.

․․․․․

Muhimmancin manne wa abin da ka gaskata.

․․․․․

Taimakon da Jehobah yake ba da wa a lokacin gwaji.

․․․․․

DON ƘARA YIN AMFANI DA ABIN DA KA KOYA.

A waɗanne yanayi ne kake ganin za a iya gwada bangaskiyarka?

․․․․․

Ta yaya ne labarin Shadrach, Meshach da kuma Abednego zai taimaka maka ka riƙe aminci?

․․․․․

4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?

․․․․․

Ka ƙara koya game da Littafi Mai Tsarki, a duniyar gizon www.watchtower.org da www.pr418.com

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba