Ka Kusaci Allah
“Mai-Tsarki, Mai-Tsarki, Mai-Tsarki Ne, Ubangiji”
IDAN za ka yi amfani da kalma guda ka kwatanta Jehobah Allah, wace kalma ce za ka zaɓa? A ƙarni na takwas K.Z., an nuna wa Ishaya wani wahayi wanda a ciki, ya ji mala’iku suna amfani da kalmar da ke kwatanta Jehobah a yabon da suke yi, wato, tsarki. Abin da Ishaya ya gani da kuma wanda ya ji ya kamata ya sa mu nuna daraja da mamaki kuma ya jawo mu kusa ga Jehobah. Yayin da muke tattauna kalmomin Ishaya 6:1-3, ka ga kanka kamar kana wurin.
Mene ne Ishaya ya gani? “Na ga Ubangiji a zaune bisa kursiyi, mai-tsayi, maɗaukaki,” in ji Ishaya. (Aya 1) Ba wai Ishaya ya ga Ubangiji Jehobah Mai Ikon Mallaka da idanuwansa biyu ba ne. Idanu na zahiri ba za su iya ganin halittu na ruhu ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa: “Ba wanda ya taɓa ganin Allah ba daɗai.” (Yohanna 1:18) Wahayi ne Ishaya ya gani.a Ya ga wahayin dalla-dalla, abin da Ishaya ya gani ya shafe shi sosai, har ya ga kamar Jehobah ne da kansa yake gani.
Bayan haka, Ishaya ya ga wani abin da babu wani ɗan Adam ɗin da ya taɓa gani a wahayi. Ya rubuta: “A birbishinsa [Jehobah] ga seraphim a tsaye; kowane yana da fukafukai guda shidda: da guda biyu ya ke rufe da fuskatasa, da biyu ya ke rufe da sawunsa, da biyu kuma ya ke tashi.” (Aya 2) Seraphim mala’iku ne masu matsayi mai girma sosai. Ishaya ne kaɗai marubucin Littafi Mai Tsarki da ya ambace su. Waɗannan Seraphim ɗin suna tsaye kuma a shirye su cika duk wani umurnin da Jehobah ya ba su. Suna rufe fuskarsu da kuma sawayensu, hakan alama ce da ke nuna girmamawa da daraja ga Wanda suke da gatan bauta wa.
Abin da Ishaya ya gani da kuma wanda ya ji ya ba shi tsoro. Seraphim sun ta da muryoyinsu suna rera waƙa, a matsayin mawaƙa na samaniya. Ishaya ya rubuta: “Ɗayan kuma ya kira ma ɗayan, ya ce, Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji mai-runduna.” (Aya 3) Kalmar Ibrananci da aka fassara “tsarki” tana nufin abu mai tsabta, marar aibi. Kalmar tana kuma nufin “kasancewa a ware gaba ɗaya daga zunubi.” A waƙar da suka ci gaba da rera wa, seraphim sun ambata kalmar nan “mai-tsarki” sau uku, kuma hakan ya nanata cewa Jehobah mai tsarki ne wanda babu kamar sa. (Ru’ya ta Yohanna 4:8) Saboda haka, tsarki, halinsa ne na musamman. Gaba da baya, Jehobah marar aibi ne, yana da tsarki kuma kamili ne.
Sanin cewa Jehobah mai tsarki ne ya kamata ya motsa mu mu kusace shi. Me ya sa? Akasin sarakuna ’yan Adam da suke iya zama masu karɓan rashawa kuma su zama mazalunta, Jehobah bai da zunubi ko kaɗan. Tsarkin da yake da shi tabbaci ne cewa a kowane lokaci shi Uba ne mafi kyau, Sarki mai adalci, da kuma Mai Shari’ar gaskiya. Muna da kyakkyawan dalili na kasancewa da gaba gaɗi cewa Jehobah wanda komi game da shi yana da tsarki ba zai taɓa sa mu baƙin ciki ba.
[Hasiya]
a Littafin nan Insight on the Scriptures ya bayyana: “Sa’ad da mutum ya sami wahayi daga Allah a lokacin da yake farke, kamar dai an saka abin da ya gani ne a cikin zuciyarsa. Daga baya wanda ya samu wahayin zai iya tuna abin da ya gani kuma ya kwatanta ko kuma ya rubuta wahayin a nasa kalmomin.”—Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Bayanin da ke shafi na 32]
Sanin cewa Jehobah mai tsarki ne ya kamata ya motsa mu mu kusace shi