Abin Da Ke Ciki
15 Ga Janairu, 2012
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI
27 GA FABRAIRU, 2012–4 GA MARIS, 2012
Kiristoci na Gaskiya Suna Daraja Kalmar Allah
SHAFI NA 4 • WAƘOƘI: 113, 116
5-11 GA MARIS, 2012
Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu
SHAFI NA 9 • WAƘOƘI: 125, 43
12-18 GA MARIS, 2012
SHAFI NA 16 • WAƘOƘI: 107, 13
19-25 GA MARIS, 2012
Ba da Hadayu da Dukan Zuciyarmu ga Jehobah
SHAFI NA 21 • WAƘOƘI: 66, 56
26 GA MARIS, 2012–1 GA AFRILU, 2012
Zuriyar Firist Basarauci da Za ta Amfane Dukan ’Yan Adam
SHAFI NA 26 • WAƘOƘI: 60, 102
MANUFAR TALIFOFIN NAZARI
TALIFIN NAZARI NA 1 SHAFUFFUKA NA 4-8
Wannan talifin zai nuna yadda Kiristoci na gaskiya a cikin shekaru da yawa suke bin ja-gorar Kalmar Allah. Tattaunawar ta nanata jigonmu na shekara ta 2012.
TALIFIN NAZARI NA 2 SHAFUFFUKA NA 9-13
Wannan talifin ya tattauna darussa guda uku da za mu iya koya daga manzannin da wasu Kiristoci na ƙarni na farko game da yin tsaro. Nazarin wannan talifin zai ƙarfafa mu mu shaida bisharar Mulkin Allah sosai.
TALIFOFIN NAZARI NA 3, 4 SHAFUFFUKA NA 16-25
Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ta bukaci Isra’ilawa na zamanin dā su ba da hadaya sau da yawa. Kiristoci ba sa bin wannan Dokar. Amma, ƙa’idodin da ke ciki suna ɗauke da darassi game da halin godiya da Jehobah yake son bayinsa a yau su nuna, kamar yadda wannan talifin zai bayyana.
TALIFIN NAZARI NA 5 SHAFUFFUKA NA 26-30
Abu mafi muhimmanci da ’yan Adam suke bukata shi ne su sulhuntu da Allah. Wannan talifin ya bincika yadda zuriyar firist basarauce za ta cim ma wannan, kuma ya bayyana yadda za mu amfana.
A FITOWAR NAN
3 Sabon Fasali na Talifi na Nazari
14 ‘Yaya Zan Iya Yin Wa’azi Duk da Yanayina?’
15 Yadda Za a Sa Lokacin Nazari Ya Ƙara Yin Daɗi da Kuma Ba da Amfani
BANGO: Kasuwar da ke kan titi a birnin San Cristóbal de las Casas, a ƙasar Mezico. Wannan majagaba ma’aurata sun koyi yaren Tzotzil kuma suna wa’azi da yaren
MEZICO
YAWAN JAMA’A
108,782,804
MASU SHELA
710,454
AIKIN FASSARA
Harsuna 30