Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/15 pp. 31-32
  • Adana Abubuwa Masu Amfani da Muke da Su a Dā

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Adana Abubuwa Masu Amfani da Muke da Su a Dā
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • “HOTUNAN IYALINMU” DA KUMA “GĀDONMU”
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/15 pp. 31-32

Daga Tarihinmu

Adana Abubuwa Masu Amfani da Muke da Su a Dā

MUTANEN Jehobah suna da tarihi mai kyau na bauta masa da daɗewa. Ban da karanta littattafanmu, muna iya koya game da wannan tarihin ta wajen hotuna da wasiƙu da labarin rayuwa da kayayyaki game da bautarmu da aikinmu na wa’azi da kuma tarihinmu. Amma mene ne amfanin adana irin waɗannan kayayyaki da kuma yin bincike game da tarihinmu na dā? An gaya wa shugabannan iyalai a Isra’ila ta dā cewa su sanar wa ’ya’yansu dokoki da kuma ayyuka masu ban al’ajabi na Jehobah don “su kafa zuciyarsu ga Allah.”—Zab. 78:1-7.

Tun da daɗewa yin bincike game da tarihi ya taimaka wajen cika nufin Jehobah. Alal misali, sa’ad da masu hamayya suka yi ƙoƙari su sa a daina aikin haikali a Urushalima, bincike da aka yi a gidan ajiye littattafai da ke Achmetha a babban birni na Midiya, ya sa aka gano littafi inda Sarki Cyrus ya ba da umurni cewa a yi wannan ginin. (Ezra 6:1-4, 12) Da hakan, aka sake gina haikalin daidai da nufin Allah. Luka marubucin Linjila wanda “tun dafari [ya] bibbiya abu duka daidai” ya kuma yi amfani da kayayyakin tarihi.—Luk 1:1-4.

Hukumar Mulki tana son tarihinmu a tsarin Allah sosai. Da yake magana game da amfanin adana da ajiye da kuma faɗin tarihinmu, wani da yake cikin Hukumar Mulki ya ce, “Sanin tarihinmu zai ba mu ƙarfi da kuma tabbaci na ci gaba.” Saboda haka, an kafa sabon sashe da ake kira Writing Archives, wato, Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā, a hedkwatarmu da ke Brooklyn, New York, kuma yana ƙarƙashin ja-gorar Kwamitin Rubuce-Rubuce.

“HOTUNAN IYALINMU” DA KUMA “GĀDONMU”

Da shigewar lokaci, sai a manta da abin da ya faru a dā, kuma yawancinmu muna yin fata cewa da mun adana kayayyakin tarihi na iyalinmu. A sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā, ana aiki yanzu sosai don a adana da kuma ajiye tarihi mai kyau da ke ƙaruwa. Ana iya ɗaukan hotunan da aka ajiye a Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā a matsayin “hotunan iyalinmu.” Littattafanmu na dā da tarihi masu ban sha’awa na ’yan’uwa da kuma kayayyaki masu tamani suna cikin abubuwa da suke Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā. Irin waɗannan kayayyakin “gādo” ne da ke wayar da mu game da gādonmu na tsarin Allah kuma yana taimaka mana mu saurari nan gaba da tabbaci.

Muna gayyatarku ku sani game da Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā ta wurin sabon talifin nan “Daga Tarihinmu.” Zai riƙa fitowa jifa jifa a cikin Hasumiyar Tsaro ta nazari. Alal misali a fitowa ta gaba, muna shirin wallafa labarin da aka shirya don ya amsa waɗannan tambayoyi: Mene ne Dawn Mobile? Wane ne ya yi amfani da shi? A wane lokaci ne aka yi amfani da shi, kuma da wane manufa?

Kamar hotunan iyali, Kayayyakin Tarihi da aka adana suna sa mu san game da kanmu da kuma kakanninmu na ruhaniya, wato, game da bangaskiya da gaba gaɗin waɗanda suka bauta wa Allah kafin mu da farin ciki da kuma ƙalubalen bauta wa Ubanmu na samaniya mai ƙauna da ja-gorar Allah da kuma yadda yake tallafa wa mutanensa sosai. (K. Sha 33:27) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarce da ake yi na adana tarihin ƙungiyarmu don mu ƙara kasancewa da haɗin kai kuma mu samu ƙarfafa don yin nufinsa.

[Akwati/Hoton da ke shafi na 31]

Yin Bincike Sosai

Marubutanmu da masu zane da masu bincike da kuma wasu suna amfani da abubuwan tarihi da aka adana sa’ad da suke shirya littattafai na Kirista da faifan DVD da kuma wasu abubuwa da ke bisa Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā yana mai da hankali sosai da kuma ɗaukan matakai da suka dace don ya tara da kuma adana kayayyakin tarihi dabam dabam daga ofisoshin reshe da wasu sassa a Bethel da ikilisiyoyi da mutane da kuma ƙungiyoyi. Ka yi la’akari da wasu abubuwa da ake yi a sashen:

Tara Abubuwa da kuma Yin Bincike: A ko da yaushe, ana daɗa tara kayayyaki na musamman a Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā. Iyalan waɗanda suke bauta wa Jehobah da aminci cikin shekaru da yawa ne suke ba da gudummawa ko kuma ba da aron waɗannan kayayyakin. Bincika da kuma gwada irin waɗannan kayayyakin suna taimaka mana mu ƙara sanin tarihinmu da kuma waɗanda suka rayu sa’ad da waɗannan abubuwan suka faru.

Tsari: Abubuwa da ake tara a Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā sun ƙunshi dubban kayayyaki, wasu sun fi ƙarni guda. Da akwai kayayyaki da yawa dabam dabam a Sashen Adana Bayanai game da Ayyukanmu na Dā kuma dole ne a rubuta bayanai game da kowane kaya don ya kasance da sauƙi a same shi kuma a yi amfani da shi don bincike a nan gaba.

Gyarawa da Adanawa: Ana gyara da kuma adana littattafai da kayayyakin fasaha marasa ƙarfi ta wajen yin amfani da kayan gyara masu kyau. Ana saka littattafai da hotuna da labaran da aka yanka daga jaridu da fina-finai da kuma abubuwan da aka ɗauka a tef cikin faifai don a saka a kwamfuta. Da hakan, za a iya bincika su a na’ura don a guji ɓata ainihin littattafai na dā ko kuma wasu kayayyaki da suke da amfani a tarihi.

Wurin Ajiya da Ɗaukowa: Ana ajiye muhimman abubuwa na tarihi bisa tsari don kada su lalace kuma kada haske da danshi su lalace su. Ana amfani da wani fayil don ya taimaka wajen bincike da kuma ɗauko waɗannan abubuwa masu tamani na tarihinmu na dā.

[Hotuna da ke shafi na 32]

1. Hoton “Photo-Drama of Creation.” 2. Sunayen waɗanda suke son a aika musu littattafai. 3. Mota mai lasifika. 4. Bangon Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1912. 5. Takarda da aka rubuta bayanai game da J. F. Rutherford sa’ad da yake kurkuku. 6. Makarufo na WBBR. 7. Garmaho. 8. Akwatin littattafai. 9. ’Yar takarda. 10. Wasiƙar da aka aika wa J. F. Rutherford.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba