Zuriyar Firist Basarauci da Za ta Amfane Dukan ’Yan Adam
“Ku zaɓaɓen iri ne, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa.”—1 BIT. 2:9.
1. Me ya sa ake kiran “Jibin Ubangiji” Abin Tuni, kuma mene ne manufarta?
A DAREN 14 ga Nisan na shekara ta 33 A.Z., Yesu Kristi da manzanninsa 12 sun yi Idin Ƙetarewa na Yahudawa a lokaci na ƙarshe. Bayan ya sallami Yahuda Iskariyoti maci amana, Yesu ya gabatar da wani kiyayewa dabam da daga baya aka kira “Jibin Ubangiji.” (1 Kor. 11:20) Yesu ya ce sau biyu: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” An kuma san shi da Abin Tuni, wato, tuna rasuwar Yesu. (1 Kor. 11:24, 25) Ta wajen yin biyayya ga wannan umurnin, Shaidun Jehobah a dukan duniya suna Tuna da Rasuwar Yesu a kowace shekara. Ranar 14 ga Nisan ta shekara ta 2012, za ta soma daga faɗuwar rana, na Alhamis 5 ga Afrilu.
2. Mene ne Yesu ya faɗa game da gurasa da ruwan anab da ya yi amfani da shi?
2 Almajiri Luka ya gaya mana abin da Yesu ya yi da kuma faɗa a wannan lokacin a hanya mai sauƙi: “Ya ɗauki gurasa kuma, sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba su, ya ce, wannan jikina ne wanda an bayar domin ku: ku yi wannan abin tunawa da ni. Hakanan kuma bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.” (Luk 22:19, 20) Yaya manzannin suka fahimci waɗannan kalamin?
3. Yaya manzannin suka fahimci ma’anar gurasa da ruwan anab?
3 A matsayin Yahudawa, manzannin sun san da hadayu na dabbobi da firistoci suke miƙawa ga Allah a haikali na Urushalima. Ana yin irin waɗannan hadayun don a samu tagomashin Jehobah, kuma ya kasance hadaya don gafarar zunubi. (Lev. 1:4; 22:17-29) Saboda haka, manzannin sun fahimci maganar da Yesu ya yi cewa jikinsa da jininsa ‘wanda an bayar dominsu’ yana nufin cewa yana ba sa kamiltaccen ransa a matsayin hadaya. Zai kasance hadayar da ta fi na dabbobi tamani.
4. Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina”?
4 Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce “wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina”? Manzannin sun fahimci annabci game da sabon alkawarin da aka yi maganarsa a littafin Irmiya 31:31-33. (Karanta.) Kalamin Yesu sun nuna cewa yana gabatar da wannan sabon alkawarin, wanda zai ɗauki matsayin Dokar alkawari da aka yi da Isra’ila ta wurin Musa. Waɗannan alkawura biyu suna da nasaba da juna ne?
5. Wane zarafi ne Dokar alkawari ta ba wa Isra’ilawa?
5 Suna da nasaba. Sa’ad da yake gabatar da Dokar alkawari, Jehobah ya gaya wa al’ummar: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gare ni daga cikin dukan al’umman duniya; gama dukan duniya tawa ce. Za ku zama mulki na firistoci a gare ni, al’umma mai-tsarki.” (Fit. 19:5, 6) Yaya Isra’ilawa suka fahimci waɗannan kalmomin?
ALKAWARI NA ZURIYAR FIRIST BASARAUCI
6. Wane alkawari ne Dokar alkawari ta cika?
6 Isra’ilawa sun fahimci kalmar nan “alkawari” domin Jehobah ya yi irin wannan alkawari da kakanninsu Nuhu da kuma Ibrahim. (Far. 6:18; 9:8-17; 15:18; 17:1-9) Bisa ga alkawarinsa da Ibrahim, Jehobah ya ce: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka.” (Far. 22:18) Manufar wannan Dokar alkawarin ita ce don a cika wannan nufin. Bisa ga wannan alkawari ne Isra’ila za ta zama “keɓaɓiyar taska . . . daga cikin dukan al’umman duniya” ga Jehobah. Don me? Don su “zama mulki na firistoci” ga Jehobah.
7. Mene ne furucin nan “mulki na firistoci” yake nufi?
7 Isra’ilawa sun san game da sarakuna da firistoci. Amma akwai mutum ɗaya kaɗai a zamanin dā wanda sarki ne da kuma firist a lokaci ɗaya. Sunan wannan mutum Malkisadik ne. (Far. 14:18) Jehobah ya ba al’ummar zarafin samun “mulki na firistoci.” Kamar yadda daga baya Nassosi suka nuna, hakan ya ba su zarafin samun zuriyar firist basarauci, wato, sarakuna da za su zama firistoci.—1 Bit. 2:9.
8. Waɗanne hidimomi ne firistoci da Allah ya naɗa suke yi?
8 Hakika, sarki yana sarauta. Amma mene ne firist yake yi? Ibraniyawa 5:1 ta bayyana: “Kowane babban firist, da shi ke keɓaɓe ne daga cikin mutane, sabili da mutane a ke sanya shi cikin al’amuran da ke na Allah, domin shi miƙa baye baye da hadayu domin zunubai.” Saboda haka, firist da Jehobah ya naɗa yana wakiltar mutane masu zunubi a gaban Allah ta wajen miƙa hadayu, yana roƙon Jehobah a madadinsu. Kuma firist yana wakiltar Jehobah a gaban mutane ta wajen koya musu dokar Allah. (Lev. 10:8-11; Mal. 2:7) A waɗannan hanyoyin, firist da Allah ya naɗa yana sulhunta mutane ga Allah.
9. (a) Mene ne Isra’ilawa suke bukatar su yi don su samu zarafin zama “mulki na firistoci”? (b) Me ya sa Jehobah ya naɗa firistoci a cikin Isra’ila? (c) Me ya sa Isra’ilawa ba su zama “mulki na firistoci” a ƙarƙashin Dokar alkawari ba?
9 Da hakan, Dokar alkawari ta ba Isra’ila zarafin samun zuriyar firist basarauci a madadin “dukan al’umman duniya.” Amma da akwai wani abu da Isra’ilawa suke bukatar su yi don su samu wannan zarafin mai ban al’ajabi, gama Allah ya ce: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina.” Shin Isra’ilawa za su iya ‘yin biyayya da maganar Jehobah’? E, amma ba gabaki ɗaya ba. (Rom. 3:19, 20) Saboda haka, Jehobah ya naɗa firistoci cikin Isra’ila, ba don su riƙa yin sarauta ba, amma don su riƙa miƙa hadayun dabbobi don zunuban mutane. (Lev. 4:1–6:7) Waɗannan zunuban sun ƙunshi na firistocin da kansu. (Ibran. 5:1-3; 8:3) Ko da Jehobah ya amince da irin waɗannan hadayun, amma ba su iya kawar da zunuban masu miƙa su ba, har ila suna tsufa da kuma mutuwa. Firistoci da aka naɗa a ƙarƙashin Dokar alkawari ba su iya sulhunta Isra’ilawa masu zuciyar kirki gabaki ɗaya ga Allah ba. Kamar yadda manzo Bulus ya ce: “Ba shi yiwuwa jinin bajimai da na awakai shi kawarda zunubai.” (Ibran. 10:1-4) An la’anta Isra’ilawa domin ba su yi biyayya ga dukan abubuwa da ke cikin Dokar ba. (Gal. 3:10) A cikin irin wannan yanayin ba za su iya yi wa duniya hidima a matsayin zuriyar firist basarauci ba.
10. Me ya sa aka kafa Dokar alkawari?
10 Hakan ba ya nufin cewa Isra’ilawa ba za su iya kasance cikin sashen “mulki na firistoci” yadda Jehobah ya yi alkawari ba. Idan suka yi ƙoƙari su yi masa biyayya, za su samu wannan zarafin amma ba a ƙarƙashin Dokar ba. Me ya sa? (Karanta Galatiyawa 3:19-25.) Waɗanda suka yi ƙoƙari su kiyaye Dokar, sun ci gaba da bauta mai tsarki. Dokar ta sa Yahudawa su fahimta cewa su masu zunubi ne kuma suna bukatar hadaya mai girma fiye da wanda babban firist ɗinsu zai miƙa. Dokar mai koyarwa ce da za ta kai su ga Kristi ko kuma Almasihu, laƙabi da suke nufin “Shafaffe.” Amma sa’ad da Almasihu ya iso, zai gabatar da sabon alkawarin da Irmiya ya annabta. Waɗanda suka amince da Kristi sun zama sashen sabon alkawari kuma za su zama “mulki na firistoci.” Bari mu ga yadda hakan ya faru.
WAƊANDA SUKE CIKIN SABON ALKAWARI SUN ZAMA ZURIYAR FIRIST BASARAUCI
11. Ta yaya Yesu ya zama tushen zuriyar firist basarauci?
11 A shekara ta 29 A.Z., Yesu Banazari ya zama Almasihu. Sa’ad da yake ɗan shekara 30, ya ba da kansa don ya yi nufi na musamman na Jehobah a gare shi, kuma ya nuna hakan ta wajen yin baftisma a cikin ruwa. Jehobah ya amince da shi a matsayin “Ɗana ne, ƙaunatacena,” ya shafe shi da ruhu mai tsarki ba da māi ba. (Mat. 3:13-17; A. M. 10:38) Hakan ya sa ya zama Babban Firist ga dukan iyalin ’yan Adam da suka yi imani da shi da kuma Sarkinsu na nan gaba. (Ibran. 1:8, 9; 5:5, 6) Zai sa ya yiwu wasu mutane su zama sashen zuriyar firist basarauci na gaske.
12. Mene ne hadayar Yesu ta sa ya yiwu?
12 A matsayin Babban Firist, wace hadaya ce Yesu zai miƙa da za ta kawar da zunubi na waɗanda suka yi imani gabaki ɗaya da shi? Kamar yadda Yesu ya nuna sa’ad da yake kafa yadda za a Tuna da Rasuwarsa, hadayar ita ce kamiltaccen ransa. (Karanta Ibraniyawa 9:11, 12.) Tun daga lokacin da ya yi baftisma a shekara ta 29 A.Z., Yesu a matsayin Babban Firist ya fuskanci gwaje-gwaje da kuma koyarwa har lokacin rasuwarsa. (Ibran. 4:15; 5:7-10) Bayan da aka ta da shi daga matattu, ya koma sama kuma ya miƙa amfanin hadayarsa ga Jehobah. (Ibran. 9:24) Tun daga lokacin, Yesu yana iya yin roƙo ga Jehobah a madadin waɗanda suka ba da gaskiya ga hadayarsa kuma ya taimaka musu su bauta wa Allah da begen samun rai madawwami. (Ibran. 7:25) Hadayarsa ta sabon alkawari ta cika.—Ibran. 8:6; 9:15.
13. Wane bege ne waɗanda suke cikin sabon alkawari suke da shi?
13 Za a shafa waɗanda suke cikin sabon alkawarin da ruhu mai tsarki. (2 Kor. 1:21) An haɗa da Yahudawa da ’yan Al’ummai masu aminci. (Afis. 3:5, 6) Mene ne zai faru da waɗanda suke cikin sabon alkawarin? Da farko, za a gafarta musu zunubansu gabaki ɗaya. Jehobah ya yi alkawari: “Zan gafarta muguntarsu, ba ni kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba.” (Irm. 31:34) Yanzu da aka gafarta musu zunubansu, za su iya zama “mulki na firistoci.” Bitrus ya gaya wa Kiristoci shafaffu: “Ku zaɓaɓen iri ne, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.” (1 Bit. 2:9) A nan, Bitrus ya yi ƙaulin kalamin Jehobah ga Isra’ila sa’ad da yake gabatar da Dokar da kuma yi amfani da su ga Kiristoci a cikin sabon alkawarin.—Fit. 19:5, 6.
ZURIYAR FIRIST BASARAUCI TA AMFANE DUKAN ’YAN ADAM
14. A ina ne zuriyar firist basarauci za ta yi hidima?
14 A ina ne waɗanda suke cikin sabon alkawari za su yi hidima? Da farko, a duniya inda a matsayin rukuni, za su yi hidimar firistoci, suna wakiltar Jehobah ga mutane ta wajen ‘sanar da mafifitan’ al’amuransa da kuma tanadar da abinci na ruhaniya. (Mat. 24:45; 1 Bit. 2:4, 5) Bayan rasuwarsu da kuma tashiwarsu daga matattu, za su yi aiki a matsayin sarakuna da kuma firistoci da Kristi a sama. (Luk 22:29; 1 Bit. 1:3-5; R. Yoh. 1:6) A cikin wahayi, manzo Yohanna ya ga halittu na ruhohi da yawa a sama kusa da karagar Jehobah. Suna rera “sabuwar waƙa” ga “Ɗan ragon” suna cewa: “Da jininka ka saye wa Allah mutane daga cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, iri-iri, ka maishe su su zama mulki da firistoci ga Allahnmu; suna kuwa mulki bisa duniya.” (R. Yoh. 5:8-10) A wani wahayi, Yohanna ya ce game da waɗannan sarakunan: “Za su zama firistoci na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi shekara dubu.” (R. Yoh. 20:6) Waɗannan sarakuna tare da Kristi sune zuriyar firist basarauci da za su amfani dukan ’yan Adam.
15, 16. Waɗanne albarka ne zuriyar firist basarauci za ta kawo wa ’yan Adam?
15 Wace albarka ce mutane 144,000 za su kawo ga duniya? Ru’ya ta Yohanna sura ta 21 ta kwatanta su a matsayin birni na samaniya, Sabuwar Urushalima, da aka kira “matar Ɗan rago.” (R. Yoh. 21:9) Aya ta 2 zuwa 4 ta ce: “Na ga kuma birni mai-tsarki, sabuwar Urushalima, tana saukowa daga sama daga wurin Allah, shiryayya kamar amarya da ado domin mijinta. Na ji babbar murya kuwa daga cikin kursiyin, ta ce, Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su, ya zama Allahnsu: zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” Wannan albarka ce mai ban al’ajabi! Makoki da baƙin ciki da azaba ko kuma kuka ba za su ƙara kasancewa ba domin babu mutuwa kuma. A lokacin, ’yan Adam za su zama kamiltattu kuma su sulhunta gabaki ɗaya da Allah.
16 Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2, ta ƙara gaya mana game da albarkar da wannan zuriyar firist basarauci za ta kawo, cewa: “Ya nuna mini kogin ruwa na rai, mai-sheƙi kamar kiristal, yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Ɗan rago, a cikin tsakiyar karabkarsa [Sabuwar Urushalima]. A wannan gefen kogi da wancan gefe kuma akwai itace na rai, mai-fid da ’ya’ya so goma sha biyu, kowane wata yana bada ’ya’yansa: ganyayen itacen kuma domin warkarwar al’ummai ne.” Da wannan tanadi na alama, za a warkar da “al’ummai” ko kuma rukuni na iyalai na ’yan Adam gabaki ɗaya daga ajizanci da suka gāda daga Adamu. Hakika, ‘al’amura na fari za su shuɗe.’
ZURIYAR FIRIST BASARAUCI TA KAMMALA AIKINTA
17. Mene ne zuriyar firist basarauci za ta cim ma daga baya?
17 A ƙarshen shekara 1,000 na hidima, zuriyar firist basarauci za ta taimaka wa ’yan Adam su zama kamiltattu. A matsayin Babban Firist da kuma Sarki, Kristi zai miƙa ’yan Adam kamiltattu ga Jehobah. (Karanta 1 Korintiyawa 15:22-26.) A lokacin zuriyar firist basarauci za ta kammala aikinta.
18. Bayan waɗanda suke cikin zuciyar firist basarauci suka kammala aikinsu, ta yaya Jehobah zai yi amfani da su?
18 Bayan hakan, yaya Jehobah zai yi amfani da waɗanda suke cikin zuriyar firist basarauci? Ru’ya ta Yohanna 22:5 ta ce: “Za su yi mulki kuma har zuwa zamanun zamanai.” Su wane ne za su zama talakawansu? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Amma irin rayuwa da za su yi da kuma abin da za su shaida wajen taimakon ’yan Adam ajizai zai shirya su su riƙe matsayinsu na yin sarauta a nufe-nufen Jehobah har abada.
19. Mene ne za a tuna wa waɗanda suka halarci Tuna da Rasuwar Yesu?
19 Za a tuna mana waɗannan koyarwa ta Littafi Mai Tsarki sa’ad da muka taru don mu Tuna da Rasuwar Yesu a ranar Alhamis, 5 ga Afrilu, 2012. Shafaffu Kiristoci da suka rage da har ila suke duniya za su nuna cewa suna cikin sabon alkawari ta wajen cin gurasa marar yisti da kuma shan ruwan inabi. Waɗannan alamu na hadayar Kristi za su tuna musu gata mai ban al’ajabi da kuma aikin da suke da shi a madawwamin nufi na Allah. Bari dukanmu mu halarta da yin godiya sosai don tanadin da Jehobah Allah ya yi na zuriyar firist basarauci don amfanin dukan ’yan Adam.
ZA KA IYA BAYYANAWA?
․․․․․
A wane lokaci ne aka fara yin alkawari na zuriyar firist basarauci?
․․․․․
Ta yaya waɗanda suke cikin sabon alkawari suka zama zuriyar firist basarauci?
․․․․․
Ta yaya zuriyar firist basarauci za ta amfani ’yan Adam?
[Hoton da ke shafi na 29]
Zuriyar firist basarauci za ta amfani ’yan Adam har abada