Ba da Hadayu da Dukan Zuciyarmu ga Jehobah
“Iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji.”—KOL. 3:23.
1-3. (a) Shin rasuwa da Yesu ya yi a kan gungumen azaba yana nufin cewa Jehobah ba ya bukatar kowane irin hadaya a gare mu? Ka bayyana. (b) Waɗanne tambayoyi ne aka yi game da miƙa hadayu a yau?
A ƘARNI na farko A.Z., Jehobah ya bayyana wa mutanensa cewa hadayar fansa ta Yesu ta kawar da Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa. (Kol. 2:13, 14) Ba a bukatar dukan hadayun da Yahudawa suke yi a cikin ɗarurruwan shekaru domin ba su da amfani kuma. Dokar ta cika aikinta a matsayin “mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi.”—Gal. 3:24.
2 Hakan ba ya nufin cewa Kiristoci ba sa miƙa hadayu kuma. Manzo Bitrus ya yi maganar ‘miƙa hadayu masu-ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kristi.’ (1 Bit. 2:5) Bugu da ƙari, manzo Bulus ya bayyana sarai cewa kowane ɓangaren rayuwa na Kirista yana kamar “hadaya.”—Rom. 12:1.
3 Saboda haka, Kirista zai iya yin hadaya ga Jehobah ta wurin ba da wasu abubuwa ko kuma sadaukar da wasu abubuwa sabili da shi. Game da abubuwan da muka sani game da hadayu da Isra’ilawa suka ba da, yaya za mu tabbata cewa Jehobah yana amincewa da dukan hadayun da muke miƙawa?
A RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM
4. Mene ne ya wajaba mu tuna game da abubuwa da muke yi a yau da kullum?
4 Zai kasance da wuya mu fahimci yadda abubuwan da muke yi a yau da kullum za su iya yin nasaba da ba da hadayu ga Jehobah. Za mu iya gani kamar yin aikace-aikacen gida da makaranta da aikin karɓan albashi da yin cefane da kuma sauransu ba za su iya shafan dangantakarmu da Allah ba. Amma, idan ka riga ka keɓe kai ga Jehobah ko kuma kana begen yin hakan a nan gaba, yana da muhimmanci ka sani cewa ayyukan da kake yi yau da kullum za su iya shafan dangantakarka da Jehobah sosai. Mu Kiristoci ne a kowane lokaci. Ya kamata mu riƙa yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a kowanne fannoni na rayuwarmu. Bulus ya aririce mu: “Iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji, ba ga mutane ba.”—Karanta Kolosiyawa 3:18-24.
5, 6. Mene ne zai taimaka mana mu tsai da shawara game da yadda za mu yi ado da kuma aikata?
5 Ayyuka na yau da kullum da Kirista yake yi ba sashen tsarkakkiyar bautarsa ga Allah ba ne. Duk da haka, tun da yake Bulus ya aririce mu mu “aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji” zai sa mu yi tunani game da halinmu a kowanne lokaci. Saboda haka, mene ne za mu koya daga wannan? Shin adonmu da ayyukanmu suna nuna cewa mu Kiristoci ne? Ko kuma sa’ad da muke yin ayyuka na yau da kullum, muna iya jin kunya ne mu nuna kanmu a matsayin Shaidun Jehobah don yadda muke aikatawa ko kuma yadda muka yi ado? Kada mu taɓa barin hakan ya faru! Mutanen Jehobah ba za su taɓa so yin wasu abubuwa da za su ɓata sunan Allah ba.—Isha. 43:10; 2 Kor. 6:3, 4, 9.
6 Bari mu bincika yadda muradin “aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji” zai shafi yadda muke yin tunani da kuma aikatawa a yanayi dabam dabam. Sa’ad da muke tattauna hakan, ya kamata mu tuna cewa dukan hadayun da Isra’ilawa suka miƙa ga Jehobah ya kasance mafi kyau.—Fit. 23:19.
YADDA YA SHAFI RAYUWARKA
7. Mene ne keɓe kai na Kirista ya ƙunsa?
7 Sa’ad da ka keɓe kanka ga Jehobah, ka yi alkawarin yin amfani da dukan rayuwarka a hidimarsa, ko ba haka ba? Wannan yana nufin cewa a kowanne fannin rayuwarka za ka sa Jehobah ya kasance farko. (Karanta Ibraniyawa 10:7.) Wannan shawara ce mai kyau. Babu shakka, ka shaida cewa sa’ad da ka nemi ra’ayin Jehobah game da wani batu kuma ka yi ƙoƙari ka bi shawarar, za ka yi nasara. (Isha. 48:17, 18) Mutanen Allah suna da tsarki da kuma farin ciki don suna da halin Wanda ya koyar da su.—Lev. 11:44; 1 Tim. 1:11.
8. Me ya sa yake da muhimmanci mu tuna cewa hadayun da Isra’ilawa suka miƙa ga Jehobah suna da tsarki?
8 An ɗauki hadayun da Isra’ilawa suka miƙa ga Jehobah da tsarki. (Lev. 6:25; 7:1) Kalma ta Ibrananci da aka fassara “tsarki” tana da ma’anar kasancewa a ware ko kuma kasance na Allah kaɗai. Don Jehobah ya amince da hadayunmu, dole ne mu guje wa abubuwa marasa tsarki na wannan duniyar. Za mu tsane abubuwan da Jehobah ba ya so. (Karanta 1 Yohanna 2:15-17.) Wannan yana nufin guje wa tarayya ko kuma kowanne abu da zai iya sa mu kasance marasa tsabta a gaban Allah. (Isha. 2:4; R. Yoh. 18:4) Hakan kuma yana nufin cewa ba za mu ci gaba da kallon abubuwa marasa tsarki ba ko lalata ko kuma mu riƙa yin tunani a kan irin waɗannan abubuwan ba.—Kol. 3:5, 6.
9. Ta yaya yadda muke bi da mutane yake da muhimmanci kuma me ya sa?
9 Bulus ya aririce ’yan’uwansa Kiristoci: ‘Kada ku manta da yin alheri da zumuntar tarayya: gama da irin waɗannan hadayu Allah yana jin daɗi.’ (Ibran. 13:16) Saboda haka, idan mun ci gaba da nuna halin kirki ga mutane da kuma taimaka musu, Jehobah zai ga halinmu a matsayin hadayu masu tsarki. Ta yin hakan, muna nuna cewa mu Kiristoci na gaskiya ne.—Yoh. 13:34, 35; Kol. 1:10.
HADAYU A BAUTA
10, 11. Yaya Jehobah yake ɗaukan hidimarmu ta Kirista da kuma bautarmu kuma yaya ya kamata hakan ya shafe mu?
10 Wata fitacciyar hanya da Kiristoci suke nuna halin kirki ga mutane ita ce ta wurin “shaidar begenmu.” Kana amfani da kowanne zarafi don ka ba da shaida? Bulus ya kira wannan muhimmin aiki na Kirista “hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunan [Allah].” (Ibran. 10:23; 13:15; Hos. 14:2) Ya kamata mu riƙa tunanin yawan lokacin da muke yi wajen yin wa’azi da kuma yadda za mu kyautata wa’azinmu, kuma an shirya yawancin sashen Taron Hidima don su taimaka mana mu yi hakan. Amma ya kamata mu tuna cewa yin wa’azi gida gida da sa’ad da muka samu zarafin yin hakan “hadaya ta yabo” ce, kuma sashen bautarmu ne, saboda haka, ya kamata mu ba da hadaya mafi kyau daga zuciyarmu. Ko da yake yanayinmu ya bambanta, amma yawan lokaci da muke yi a wa’azi sau da yawa yana nuna yawan yadda muke godiya don abubuwa na ruhaniya.
11 Muna bauta wa Jehobah a kai a kai ko muna gida ko kuma ikilisiya. Jehobah yana bukatar mu yi hakan. Ko da yake ba a bukatar mu yi biyayya ga dokar Assabaci ko kuma mu tafi Urushalima don idodi, amma har ila muna iya koyan darasi daga waɗannan dokokin. Kullum muna yin abubuwa da yawa, amma Allah yana bukatar mu yi amfani da wasu cikin lokatanmu don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da addu’a da kuma halartar tarurruka. Kuma shugaban iyalai suna da aikin gudanar da bauta ta iyali da waɗanda suke cikin iyalinsu. (1 Tas. 5:17; Ibran. 10:24, 25) Game da ayyukanmu na ruhaniya ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Shin zan iya kyautata bauta ta?’
12. (a) Da mene ne a yau za a iya kamanta turaren wuta da ake miƙa a bauta a zamanin dā? (b) Ta yaya wannan kwatancin zai shafi yadda muke addu’a?
12 Sarki Dauda ya rera waƙa ga Jehobah: “Bari addu’ata ta miƙu a gabanka kamar turaren ƙonawa.” (Zab. 141:2) Yana da kyau mu yi tunani game da yawan yadda muke yin addu’a da kuma abin da muke addu’a game da shi. Littafin Ru’ya ta Yohanna ya kamanta “addu’o’in tsarkaka” da turare, da yake addu’o’in da Jehobah yake amincewa da su suna tashi zuwa wurin Jehobah kamar turare mai ƙanshi. (R. Yoh. 5:8) A Isra’ila ta dā, ana shirya turaren da ake miƙawa a kan bagadin Jehobah a kai a kai da kyau bisa ƙa’ida. Jehobah yana amincewa da turaren idan aka miƙa shi daidai da ƙa’idodin da ya kafa. (Fit. 30:34-37; Lev. 10:1, 2) Haka nan ma, idan muka bi wannan misalin sa’ad da muke addu’a ga Jehobah, za mu kasance da tabbaci cewa zai ji addu’o’inmu.
BAYARWA DA KUMA ƘARBA
13, 14. (a) Wace hidima ce Abafroditus da ikilisiya da ke Filibi suka yi wa Bulus, kuma yaya manzon ya ji? (b) Ta yaya za mu iya bin misalin Abafroditus da kuma Filibiyawa?
13 Gudummawa na kuɗi da muke bayarwa don tallafa wa aikin da ake yi a dukan duniya tana kama da hadaya, ko tana da yawa ko kuma kaɗan ce. (Mar. 12:41-44) A ƙarni na farko A.Z., ikilisiyar da ke Filibi ta tura Abafroditus zuwa Roma don ya kula da bukatun zahiri na Bulus. Ikilisiyar ta aika wa Bulus kyautar kuɗi ta wurinsa. Wannan ba lokaci na farko ba ne da Filibiyawa suka nuna wa Bulus karimci ba. Sun aika wa Bulus wannan kyautar domin ba sa son ya damu game da kuɗi, maimakon haka, suna son ya yi amfani da lokacinsa sosai a hidima. Yaya Bulus ya ɗauki wannan kyautar? Ya kira ta “shesheƙi na ƙanshi mai-daɗi, hadaya ce mai-daɗin karɓa, abin gami Allah.” (Karanta Filibiyawa 4:15-19.) Bulus ya nuna godiya sosai ga alherin da Filibiyawa suka nuna, kuma Jehobah ma ya yi farin ciki.
14 A yau ma, Jehobah yana godiya sosai ga gudummawa da muke ba da ga aikin da ake yi a dukan duniya. Bugu da ƙari, ya yi alkawari cewa idan mun ci gaba da saka al’amura na Mulki farko a rayuwarmu, zai biya dukan bukatunmu na ruhaniya da kuma na zahiri.—Mat. 6:33; Luk 6:38.
KA NUNA GODIYA
15. Don waɗanne abubuwa ne kake godiya ga Jehobah?
15 Muna da dalilai masu yawa na nuna godiya ga Jehobah. A kowace rana ya kamata mu gode masa don kyautar rai. Yana ba mu kome da muke bukata don mu kasance da rai, kamar su abinci da tufafi da wurin kwanciya da kuma iska da muke shaƙa. Bugu da ƙari, bangaskiyarmu da ke bisa cikakken sani tana sa mu kasance da bege. Ya dace mu bauta wa Jehobah kuma mu miƙa masa hadayu na yabo, domin shi ne Mahaliccinmu kuma domin abubuwan da ya yi mana.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 4:11.
16. Ta yaya muke nuna cewa muna godiya don hadayar fansa ta Kristi?
16 Talifin da ya gabata ya ambata cewa hadayar fansa ta Kristi ce kyauta mai tamani da Allah ya ba wa ’yan Adam. Wannan kyautar ta nuna yawan yadda Allah yake ƙaunarmu. (1 Yoh. 4:10) Yaya za mu nuna cewa muna godiya don wannan? Bulus ya ce: “Ƙaunar Kristi tana i mana; gama haka mun gani, ɗaya ya mutu sabili da duka, . . . kuma ya mutu sabili da duka, domin waɗanda ke rayuwa kada su ƙara rayuwa da kansu, amma ga wanda ya mutu ya kuwa tashi sabili da su.” (2 Kor. 5:14, 15) Bulus yana cewa idan muna godiya don abin da Allah ya yi, ya kamata mu yi amfani da ranmu don ɗaukaka Allah da kuma Ɗansa. Muna nuna ƙaunarmu da kuma godiya ga Allah da kuma Kristi ta wurin yin biyayya da kuma son yin wa’azi da kuma samun almajirai.—1 Tim. 2:3, 4; 1 Yoh. 5:3.
17, 18. A waɗanne hanyoyi ne wasu suka ƙara hadayarsu ta yabo ga Jehobah? Ka ba da misali.
17 Shin zai yiwu ka kyautata hadaya ta yabo da kake miƙawa ga Allah? Bayan sun yi tunani game da dukan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi musu, mutane da yawa sun motsa su tsara lokacinsu da ayyukansu don su ƙara saka hannu a aikin wa’azi da kuma wasu ayyuka na ƙungiyar Jehobah. Wasu sun yi hidimar majagaba na ɗan lokaci na wata guda ko fiye da hakan a kowacce shekara, yayin nan kuma wasu sun soma hidimar majagaba na kullum. Wasu sun taimaka da aikin gine-gine da ake amfani da su don hidimar Jehobah. Waɗannan hanyoyi ne masu kyau na nuna godiyarmu. Idan aka yi hakan da muradin da ya dace, wato, don mu nuna masa godiya, Allah zai amince da abin da muke yi masa.
18 Kiristoci da yawa sun nuna godiyarsu ga Jehobah. Morena ma ta yi hakan. An rene ta a Katolika amma tana da tambayoyi da yawa game da Allah da kuma ma’anar rai. Ta nemi amsoshi a Katolika da kuma falsafa na Asiya, amma sai lokacin da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah ne aka amsa tambayoyinta sosai. Morena ta yi godiya sosai ga Jehobah don abin da ta koya a cikin Littafi Mai Tsarki domin hakan ya sa ta farin ciki sosai. Saboda haka, ta soma hidimar majagaba na ɗan lokaci a kai a kai da zarar ta yi baftisma, kuma sa’ad da ta samu dama, sai ta zama majagaba na kullum. Hakan ya faru shekara 30 da suka shige, kuma har ila, Morena tana yin hidima ta cikakken lokaci.
19. Ta yaya zai yiwu ka ƙara hadayunka ga Jehobah?
19 Hakika, da akwai bayin Jehobah da yawa masu aminci da ba su sami damar yin hidimar majagaba ba. Iyakar abin da za mu iya yi a hidimar Jehobah, dukanmu za mu iya yi masa hadaya ta ruhaniya. A halinmu, muna bukatar mu kiyaye ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki kuma mu tuna cewa muna wakiltar Jehobah a dukan lokaci. A batun bangaskiya, muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa. Muna yin nagargarun ayyuka ta wajen yaɗa bishara. Muna nuna cewa muna godiya da gaske ga dukan abin da Jehobah ya yi mana. Saboda haka, bari mu ci gaba da miƙa hadayu da dukan zuciyarmu ga Jehobah.
ZA KA IYA AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN?
․․․․․
Ta yaya za mu iya ɗaukaka Jehobah a ayyukanmu na kullum?
․․․․․
Waɗanne hadayu muke yi a bautarmu ga Allah?
․․․․․
Ta yaya za mu iya miƙa abubuwan mallakarmu ga Jehobah?
[Bayanin da ke shafi na 25]
Shin nagartar Jehobah tana motsa ka ka kyautata hadayarka ta yabo?
[Hoton da ke shafi na 23]
Kana yin amfani da kowane zarafi don ka ba da shaida?