Yadda Za a Sa Lokacin Nazari Ya Ƙara Yin Daɗi da Kuma Ba da Amfani
Ta yaya za mu ƙara jin daɗin nazarin Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu sa lokacin nazarin ya ƙara ba da amfani? Bari mu tattauna matakai uku masu muhimmanci da za su taimaka mana mu amfana sosai daga nazarinmu na Littafi Mai Tsarki.
1 KA YI ADDU’A: Mataki na farko da za a ɗauka shi ne yin addu’a. (Zab. 42:8) Me ya sa? Ya kamata mu ɗauka nazarin Kalmar Allah a matsayin bautarmu. Saboda haka, muna bukatar mu gaya wa Jehobah ya taimaka mana mu buɗe zuciyarmu don mu amince da abin da muka yi nazarinsa kuma ya ba mu ruhunsa mai tsarki. (Luk 11:13) Barbara wadda ta daɗe tana wa’azi a ƙasar waje ta ce: “A ko da yaushe ina yin addu’a kafin na karanta da kuma yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Bayan hakan, ina jin cewa Jehobah yana tare da ni kuma ya amince da abin da nake yi.” Yin addu’a kafin mu yi nazari yana sa mu buɗe zuciyarmu kuma mu amince da gaskiyar da za mu koya.
2 KA YI BIMBINI: Domin rashin lokaci, wasu suna karanta Kalmar Allah kawai. Amma ba sa samun amfani da ya kamata daga nazarin Littafi Mai Tsarki. Carlos, wanda yake bauta wa Jehobah fiye da shekara 50 yanzu, ya fahimci muhimmancin keɓe lokaci don yin bimbini. Kuma yin hakan zai sa mu amfana daga nazarin da muka yi. Ya ce: “Yanzu ina karanta shafuffuka kaɗan na Littafi Mai Tsarki, aƙalla shafuffuka biyu a kowace rana. Sai in ba da ƙarin lokacin don yin bimbini a kan abin da na karanta don na koyi darussa masu muhimmanci.” (Zab. 77:12) Sa’ad da muka ba da lokaci sosai don yin bimbini, za mu kyautata iliminmu da kuma fahiminmu game da nufin Allah.—Kol. 1:9-11.
3 KA YI AMFANI DA DARASIN: Idan muka ga cewa yin wani abu zai taimake mu, za mu ƙara amfana ta wurin yin sa. Hakan yake da nazarin Littafi Mai Tsarki. “Nazari yana taimaka mini na sha kan matsaloli a rayuwa na yau da kullum, kuma yana sa na kasance a shirye na taimaki wasu,” in ji Gabriel, wani ɗan’uwa matashi wanda yake nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Ya daɗa: “Ina ƙoƙari na yi amfani da kome da nake koya a rayuwa ta.” (K. Sha 11:18; Josh. 1:8) Hakika, za mu iya koya abubuwa da yawa daga Allah kuma mu yi amfani da su.—Mis. 2:1-5.
KA YI BITA: Muna da gatar bincika sani da Jehobah Tushen dukan hikima ke tanadinsa! (Rom. 11:33) Saboda haka, sa’ad da kake son ka yi nazari, ka tabbata cewa ka fara da yin addu’a ga Jehobah kuma ka roƙe shi ya sa ka kasance da ra’ayi mai kyau kuma ya ba ka ruhunsa mai tsarki. A wasu lokatai, ka dakata ka yi bimbini a kan abin da ka karanta. Kuma ka yi amfani da abubuwa da ka koya a rayuwarka na yau da kullum. Idan ka ɗauki waɗannan matakai masu muhimmanci, za ka ga cewa nazarinka na Littafi Mai Tsarki zai yi daɗi sosai kuma zai amfane ka.