Ka Rika Yin Bimbini a Kan Abubuwan da Suka Shafi Ibada
“Ka yi kwazo [“bimbini,” NW] cikin waɗannan al’amura; ka ba da kanka gare su sosai; domin ci gabanka ya bayanu ga kowa.—1 TIM. 4:15
WAKOKI: 57, 52
1, 2. A waɗanne hanyoyi masu muhimmanci ne ’yan Adam suka bambanta daga dabbobi?
’YAN ADAM suna iya koyan wani yare, kuma hakan zai iya sa su iya karatu ko rubutu ko magana ko su fahimci abin da mutum ya faɗa ko addu’a ko kuma su rera wakar yabo ga Jehobah. Kowanne cikin waɗannan abubuwa suna da ban al’ajabi kuma sun kunshi sassan kwakwalwa da tsarin jijiyoyin da har ila masana kimiyya ba su gama fahimta ba. Muna iya koyon wani yare domin kwakwalwarmu tana da fasaloli na musamman. Wani farfesa ilimin harsuna ya ce: “Yadda yara suke iya koyon yare, wani fasali ne da ya sa ’yan Adam sun bambanta da sauran halittu.”
2 Allah ne ya ba ’yan Adam baiwa ta koyon yare. (Zab. 139:14; R. Yoh. 4:11) Kwakwalwarmu ta bambanta a wani fasali mai muhimmanci kuma. Ba kamar dabbobi ba, Allah ya halicce ’yan Adam “a cikin kamaninsa.”’Yan Adam suna da ’yanci zaɓan yin abin da suke so su yi kuma saboda haka suna iya zaɓan su yi amfani da yare don su girmama Allah.—Far. 1:27.
3. Wace kyauta ce mai tamani Jehobah ya ba mu don mu zama masu hikima?
3 Allah ya ba da kyautar Littafi Mai Tsarki ga dukan waɗanda suke so su bauta masa kuma su yabe shi. A yau muna da Littafi Mai Tsarki ko sashensa a cikin harsuna fiye da 2,800. Idan ka yi bimbini a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, ra’ayinka zai kasance ɗaya da na Allah. (Zab. 40:5; 92:5; 139:17) Hakan zai taimaka maka ka ji daɗin yin bimbini a kan abubuwa da za su sa ka zama mai hikima kuma su sa ka sami “ceto” wato rai na har abada.—Karanta 2 Timotawus 3:14-17.
4. Mene ne yin bimbini yake nufi, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
4 Yin bimbini yana nufin yin tunani mai zurfi a kan wani abu mai kyau ko marar kyau. (Zab. 77:12; Mis. 24:1, 2) Yin bimbini a kan Jehobah Allah da kuma Ɗansa Yesu Kristi shi ne suka fi muhimmanci. (Yoh. 17:3) Shin wace alaka ce ke tsakanin yin karatu da kuma yin bimbini? Wane zarafi ne muke da shi na yin bimbini, kuma mene ne zai taimaka mana mu rika jin daɗin yin bimbini a kai a kai?
KA TABBATA CEWA KANA AMFANA DAGA NAZARIN DA KAKE YI
5, 6. Mene ne zai taimake ka ka fahimci kuma ka tuna abin da ka karanta da kyau?
5 Za ka iya yin abubuwa masu ban al’ajabi ba tare da yin wani tunani ba. Waɗannan abubuwa sun kunshi yin numfashi ko tafiya ko tuka keke da dai sauransu. Hakan ya haɗa da yin karatu. Saboda haka yana da muhimmanci ka mai da hankali don ka san ma’anar abin da kake karantawa. Idan ka kai karshen wani sakin layi ko kuma kafin ka soma karanta wani kan magana a cikin wani littafi, ya kamata ka dakata kuma ka yi bimbini a kan abin da ka karanta don ka tabbata cewa ka fahimci shi da kyau. Hakika, abubuwa da suke raba hankali da kuma tunanin wani abu dabam sa’ad da kake karatu ba za su taimaka maka ka amfana daga abin da kake karantawa ba. Shin mene ne za ka yi?
6 Masana kimiyya sun gano cewa yana da sauki ka tuna wani abu idan kana karantawa da murya. Mahaliccinmu ya san da hakan, shi ya sa ya ba Joshua umurni ya rika ‘bincika’ [“bimbini,” NW] littafinsa na Doka. (Karanta Joshua 1:8.) Za ka ga cewa karanta Littafi Mai Tsarki a hankali ko kuma yin bimbini zai sa ka rika tuna abin da ka karanta. Kari ga haka, zai sa ka rika mai da hankali ga abin da kake karantawa.
7. Wane lokaci ne ya fi dacewa mu rika yin bimbini a kan Kalmar Allah? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)
7 Ko da yake yin karatu yana da sauki, muna bukatar mu mai da hankali sosai sa’ad da muke bimbini. Shi ya sa yake da sauki mu yi abubuwa da ba su da wuya nan da nan. Lokacin da ya fi dacewa ka yi bimbini shi ne sa’ad da ka huta kuma kana inda babu kara ko surutu. Marubucin zabura ya ga cewa lokacin da ya fi dacewa ya yi bimbini shi ne sa’ad da ya farka daddare. (Zab. 63:6) Ko da yake Yesu kamiltacce ne, ya zaɓa ya rika bimbini da kuma addu’a a wurin da babu surutu.—Luk. 6:12.
ABUBUWA MASU KYAU DA ZA KA YI BIMBINI A KAI
8. (a) Ban da Kalmar Allah, mene ne za mu iya yin bimbini a kai? (b) Yaya Jehobah yake ji sa’ad da muke magana game da shi?
8 Ban da abubuwan da ka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki, da akwai wasu abubuwa da za ka iya yin bimbini a kansu. Alal misali, ka dakata kuma ka yi tunani sa’ad da ka ga halittu masu ban al’ajabi. Babu shakka, hakan zai motsa ka ka yabi Jehobah don alherinsa kuma idan kana tare da wasu, za ka so ka gaya musu game da ayyukan Allah. (Zab. 104:24; A. M. 14:17) Shin Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka yi bimbini da addu’a da kuma tattauna game da shi? Kalmarsa ta ba da amsar. Ya yi alkawari game da wannan mugun zamani cewa: ‘Sa’annan su waɗanda suka ji tsoron Ubangiji suka yi zance da junansu; Ubangiji kuma ya kasa kunne, ya ji, aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda suke jin tsoron Ubangiji, masu tunawa da sunansa.’—Mal. 3:16.
Shin kana yin bimbini a kan bukatu da kuma yanayin ɗalibinka? (Ka duba sakin layi na 9)
9. (a) Mene ne Bulus ya gaya wa Timotawus ya yi bimbini a kai? (b) Ta yaya za mu yi amfani da shawarar da Bulus ya ba da sa’ad da muke shirin fita wa’azin bishara?
9 Manzo Bulus ya gaya wa Timotawus ya “yi kwazo” [“bimbini,” NW] a kan yadda furucinsa da halinsa da kuma koyarwarsa suke shafan wasu. (Karanta 1 Timotawus 4:12-16.) Kamar Timotawus, muna da ayyukan ibada da yawa da za mu yi bimbini a kansu. Alal misali, muna bukatar lokaci don mu yi bimbini yayin da muke shirin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu. Ka yi tunani game da ɗalibinka kuma ka yi kokari ka nemi tambaya ko kuma kwatanci da zai taimaka masa ya sami ci gaba a bautarsa. Idan ka shirya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wani ta hakan, za ka karfafa bangaskiyarka kuma zai taimaka maka ka zama mai koyar da Littafi Mai Tsarki da kwazo. Za ka kuma amfana sosai idan ka yi bimbini kafin ka fita wa’azin bishara. (Karanta Ezra 7:10.) Karanta wata sura a cikin littafin Ayyukan Manzanni zai “rura” ko kuma inganta kwazonmu a yin wa’azi. Yin bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki da muke so mu yi amfani da shi da kuma littattafan da muke so mu ba da a wa’azi, za su taimaka mana mu yi hidimarmu sosai. (2 Tim. 1:6) Kari ga haka, ka yi tunanin mutane da ke yankinku da abin da za ka faɗa da zai jawo hankalinsu. Yin wannan shirin zai motsa mu mu yi wa’azi sosai “da shaidar Ruhu da iko” daga Kalmar Allah.—1 Kor. 2:4.
10. Waɗanne karin abubuwa ne za ka iya yin bimbini a kansu?
10 Shin kana rubuta muhimman bayanai sa’ad da ake ba da jawabi ga jama’a ko a manyan taro da kuma taron yanki? Yin bitar waɗannan bayanan zai sa ka sami zarafin yin bimbini a kan abin da ka koya daga Kalmar Allah da kuma kungiyarsa. Kari ga haka, za ka iya yin bimbini a kan bayanai da ke cikin kowace fitowar Hasumiyar Tsaro da Awake! na kowane wata da kuma littattafai da aka fito da su a taron yanki. Sa’ad da kake karanta littafin Yearbook of Jehovah’s Witnesses, ka dakata bayan ka karanta wani labari, hakan zai ba ka lokaci ka yi bimbini a kan abin da ka karanta kuma ya sa labarin ya ratsa zuciyarka. Kana iya jan layi a karkashin muhimman bayanai ko kuma ka rubuta bayanan a gefen littafinka. Hakan zai taimake ka sa’ad da kake shiri don ka ziyarci ɗalibinka ko wani da ka yi masa wa’azi ko wani ɗan’uwa da ke bukatar karfafawa ko kuma sa’ad da kake shirya wani jawabi da za ka bayar. Mafi muhimmanci ma, idan ka dakata ka yi bimbini a kan abin da ka karanta, hakan zai ba ka damar barin bayanin ya ratsa zuciyarka kuma ka samu lokacin yin addu’a don ka gode wa Jehobah don abubuwa masu kyau da kake koya.
KA RIKA YIN BIMBINI A KAN KALMAR ALLAH KULLUM
11. Wane littafi ne ya fi muhimmanci mu yi bimbini a kai, kuma me ya sa? (Ka duba karin bayani.)
11 Hakika, Littafi Mai Tsarki ne ainihin littafi da ya kamata mu yi bimbini a kai sosai. Amma idan ka sami kanka a cikin wani yanayi da babu Littafi Mai Tsarki, babu wanda zai iya hana ka yin bimbini a kan abubuwan da ka haddace, kamar nassosi ko kuma wakokin Mulki da ka fi so.a (A. M. 16:25) Kari ga haka, ruhun Allah zai taimaka maka ka tuna da abubuwan da ka koya.—Yoh. 14:26.
12. Wane tsarin karanta Littafi Mai Tsarki ne zai taimaka maka sosai?
12 Za ka iya keɓe wasu kwanaki a cikin mako don ka karanta da kuma bimbini a kan karatun Littafi Mai Tsarki na mako-mako da ake yi a Makarantar Hidima ta Allah. Za ka iya keɓe sauran kwanakin don yin bimbini a kan abin da Yesu ya faɗa kuma ya yi sa’ad da yake duniya. Kuma littattafan Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna za su taimaka maka ka san labarin rayuwar Yesu da hidimarsa. (Rom. 10:17; Ibran. 12:2; 1 Bit. 2:21) Kari ga haka, an yi wa mutane Allah tanadin wani littafin da ya kwatanta abubuwan da Yesu ya yi da kuma tsarin yadda hakan ya faru. Wannan littafin zai taimaka maka sosai, musamman idan kana karantawa kuma kana yin bimbini a kan ayoyin da aka rubuta a kowane babi.—Yoh. 14:6.
ABIN DA YA SA YIN BIMBINI YAKE DA MUHIMMANCI SOSAI
13, 14. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da yin bimbini a kan abubuwan da za su karfafa dangantakarmu da Jehobah, kuma mene ne hakan zai motsa mu mu yi?
13 Yin bimbini a kan abubuwan da za su karfafa dangantakarmu da Jehobah za su taimaka wa mutum ya zama Kirista da ya manyanta. (Ibran. 5:14; 6:1) Mutumin da ba ya ba da lokaci don yin bimbini game da Jehobah da Yesu ba zai kasance da bangaskiya sosai ba. Zai iya rasa dangantakarsa da Jehobah ko kuma ya daina bauta masa. (Ibran. 2:1; 3:12) Yesu ya ce idan ba ma ji ko kuma amince da Kalmar Allah da “zuciya mai gaskiya mai kyau” ba, ba za mu “rike” ta ba. A maimakon haka, “sha’ani, da wadata, da annashuwa ta wannan rai” za su ɗauke hankalinmu kuma ba za mu “bada wani amfanin kirki ba.”—Luk. 8:14, 15.
14 Saboda haka, bari mu ci gaba da yin bimbini a kan Kalmar Allah. Hakan zai motsa mu mu yi koyi da halayen Jehobah kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki. (2 Kor. 3:18) Kari ga haka, za mu ci gaba da kara koya game da Allah, kuma da yake an ba mu gata mai girma na nuna ɗaukakarsa, za mu ci gaba da yin koyi da shi har abada.—M. Wa. 3:11.
15, 16. (a) Ta yaya za mu amfana idan muka yi bimbini a kan abubuwa da za su karfafa dangantakarmu da Jehobah? (b) Me ya sa wani lokaci yake da wuya mu yi bimbini, amma me ya sa ya kamata mu nace da yin hakan?
15 Idan muka ci gaba da yin bimbini a kan abubuwa da za su karfafa dangantakarmu da Jehobah, za mu kasance da kwazo a ibadarmu. Hakan zai sa mu karfafa ’yan’uwanmu da kuma mutane da muke wa wa’azin bishara. Yin bimbini sosai a kan kyauta mafi tamani da Allah ya ba mu, wato hadayar fansa na Yesu zai taimaka mana mu ɗaukaka gatan da muke da shi na kulla dangantaka ta kud da kud da Ubanmu Jehobah, Mai tsarki. (Rom. 3:24; Yak. 4:8) Wani ɗan’uwa ɗan Afirka ta Kudu mai suna Mark, wanda ya yi shekara uku a kurkuku don imaninsa ya ce: “Ana iya kwatanta yin bimbini da tafiya mai ban sha’awa. Za mu kara koyon sababbin abubuwa game da Allahnmu Jehobah, yayin da muke kara yin bimbini a kan abubuwa da za su karfafa dangantakarmu da shi. Nakan ɗauki Littafi Mai Tsarki kuma in yi bimbini a kan wata aya a lokacin da na yi sanyin gwiwa ko kuma na damu game da abin da zai faru a nan gaba. Ina ganin hakan yana sa hankalina ya kwanta.”
16 Hakika, akwai abubuwa da suke raba hankali sosai a wannan duniya, saboda haka yin bimbini a kan abubuwan da za su karfafa dangantakarmu da Jehobah bai da sauki. Wani ɗan’uwa a Afrika mai aminci, mai suna Patrick, ya ce: “Zuciyata tana kama da akwatin gidan waya da ke cike da sako iri-iri, wanda muke so da wanda ba ma so, kuma ana bukata a rika bincika su a kowace rana. Yayin da nake bincika abin da ke cikin zuciyata, nakan sami tunanin banza kuma in yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini in tattara hankalina wuri ɗaya don yin bimbini da kyau. Ko da yake yin hakan yakan ɗauki lokaci kafin na soma yin bimbini a kan abubuwa da suka shafi dangantakata da Jehobah, ina ganin hakan ya sa na kusaci Jehobah sosai. Kari ga haka, na kara fahimtar koyarwa Littafi Mai Tsarki da kyau.” (Zab. 94:19) Hakika, waɗanda suke bincika “littattafai kowacce rana” da kuma yin bimbini a kan abin da suka koya za su amfana sosai.—A. M. 17:11.
A WANE LOKACI NE KAKE YIN BIMBINI?
17. Ta yaya kake samun lokacin don yin bimbini?
17 Wasu suna tashi da sassafe don su yi karatu da bimbini da kuma addu’a. Wasu suna hakan a lokacin cin abincinsu na rana. Kana iya yin hakan da yamma ko kuma kafin ka yi barci da daddare. Wasu suna jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki da safe da kuma sa’ad da suke son su kwanta daddare. Ta yin hakan suna karanta shi “dare da rana,” ko kuma a kai a kai. (Josh. 1:8) Abin da yake da muhimmanci shi ne mu daina wasu abubuwa da ba su da muhimmanci sosai don yin bimbini a kan Kalmar Allah.—Afis. 5:15, 16.
18. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da waɗanda suke yi bimbini a kan Kalmar Allah a kowace rana kuma suna kokari su yi abin da suka koya?
18 Allah ya yi alkawari a cikin Littafi Mai Tsarki cewa waɗanda suke yin bimbini da kuma bin abin da suke koya za su sami albarka. (Karanta Zabura. 1:1-3.) Yesu ya ce: “Gwamma dai waɗannan da suke jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma.” (Luk. 11:28) Mafi muhimmanci, yin bimbini a kan abubuwan da za su karfafa dangantakarmu da Jehobah a kowace rana zai taimaka mana mu ɗaukaka Mahaliccinmu. Kari ga haka, zai sa mu yi farin ciki yanzu, mu sami rai na har abada a sabuwar duniya.—Yak. 1:25; R. Yoh. 1:3.
a Ka duba talifin nan “Our Fight to Stay Spiritually Strong” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 2006 a Turanci.