Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 12/1 pp. 21-26
  • Ka More Nazarinka Na Kalmar Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka More Nazarinka Na Kalmar Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Hali Mai Kyau Yana Kawo Sakamako Mai Kyau
  • Ku Yi Tafiya Wadda ta Cancanta ga Jehovah
  • Abin da Zai Taimake Mu Fahimta
  • Ka Rika Yin Bimbini a Kan Abubuwan da Suka Shafi Ibada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Nazari Mai Albarka Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Nazari Da Kanmu Da Yake Sa Mu Ƙware Wajen Koyarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 12/1 pp. 21-26

Ka More Nazarinka Na Kalmar Allah

“Zan yi ta bimbinin dukan aikinka, in yi maganar zuci a kan aike aikenka.”—ZABURA 77:12.

1, 2. (a) Me ya sa ya kamata mu ba da lokaci domin bimbini? (b) Menene ake nufi da “bimbini” da kuma “waswasi”?

MU ALMAJIRAN Yesu Kristi, ya kamata mu damu sosai game da dangantakarmu da Allah da kuma dalilin da ya sa muke bauta masa. Amma a yau, yawancin mutane sun shagala cikin ayyukan rayuwa da ba su ma da lokaci na yin bimbini. Sun dulmaya cikin ayyukan neman abin duniya, sayan kayayyaki, da kuma nishaɗi marar ma’ana. Ta yaya za mu guji irin waɗannan ayyuka marasa ma’ana? Kamar yadda muka ba da lokaci domin ayyuka masu muhimmanci a rayuwa, kamar su cin abinci da kuma barci, haka ya kamata mu ba da lokaci kowacce rana mu yi bimbini a kan ayyukan Jehovah da kuma sha’aninsa.—Kubawar Shari’a 8:3; Matta 4:4.

2 Ka taɓa ba da lokaci domin ka yi bimbini? Menene ake nufi da a yi bimbini? Wani ƙamus ya fassara kalmar nan da “bin abu a zuci: yin tunani ko kuma waswasi.” Kuma kalmar nan “waswasi” tana nufin “a yi tunanin abu: a bi abu a zuci . . . a yi tunani ko kuma a yi la’akari sosai.” Menene muhimmancin wannan a gare mu?

3. Ga menene ci gaba ta ruhaniya take da nasaba ta kai tsaye?

3 Wani abu shi ne, ya kamata ya tunasar da mu abin da manzo Bulus ya rubuta wa ɗan’uwansa bawa Timothawus: “Ka maida hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa, har na zo. . . . Ka yi [waswasi] cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin ci gabanka ya bayyanu ga kowa.” Hakika, ana tsammanin ci gaba, kuma kalmomin Bulus sun nuna cewa da akwai nasaba ta kai tsaye tsakanin waswasi bisa abubuwa na ruhaniya da ci gaba. Haka yake a yau. Domin mu more gamsuwa ta ci gaba a ruhaniya, dole ne mu yi “waswasi” kuma mu ‘ba da kanmu’ ga abubuwa da suka shafi Kalmar Allah.—1 Timothawus 4:13-15.

4. Waɗanne abubuwa za ka yi amfani da su su taimaka maka wajen waswasi a kan Kalmar Jehovah a kai a kai?

4 Lokaci mafi kyau na yin bimbini ya dangana ne a gare ka da kuma ayyukan yau da kullum na iyalinka. Mutane da yawa suna waswasi a kan ayar Littafi Mai Tsarki da suka karanta daga Nassosin Yini da sassafe. Waɗanda suka ba da kansu su yi hidima a gidajen Bethel a dukan ɓangarorin duniya mutane kusan 20,000 suna fara ayyukansu a rana da bincika ayar Littafi Mai Tsarki na minti 15. Ko da yake mutane kalilan ne suke yin kalami a kan ayar kowacce safiya, sauran suna yin waswasi a kan abin da aka ce da kuma abin da aka karanta. Wasu Shaidu suna waswasi a kan Kalmar Jehovah sa’ad da suke kan hanyarsu zuwa wurin aiki. Suna saurarar kaset na rediyo na Littafi Mai Tsarki da kuma jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! da ake da su a wasu harsuna. Wasu matan aure suna yin haka sa’ad da suke aiki a gida. Babu shakka, suna kwaikwayon Asaf ne, da ya rubuta: “Zan ambata ayyukan Ubangiji; gama zan tuna da al’ajabanka na dā. Zan yi ta bimbinin dukan aikinka, in yi maganar zuci a kan aike aikenka.”—Zabura 77:11, 12.

Hali Mai Kyau Yana Kawo Sakamako Mai Kyau

5. Me ya sa nazari ya kamata ya kasance da muhimmanci a gare mu?

5 A wannan zamaninmu na telibijin, bidiyo, da kuma kwamfuta, karatu ya wahala ƙwarai, idan ma mutane ba su daina ba ke nan. Amma wannan bai kamata ya kasance haka ba a tsakanin Shaidun Jehovah. Karatun Littafi Mai Tsarki hanyar rai ce da take haɗa mu da Jehovah. Shekaru dubbai da suka shige, Joshua ya gāji shugabancin Isra’ila daga Musa. Domin ya samu albarkar Jehovah, dole ne Joshua ya karanta Kalmar Allah. (Joshua 1:8; Zabura 1:1, 2) Wannan har yanzu wajibi ne a yau. Amma domin rashin makaranta, zai yi wa wasu wuya ƙwarai su yi karatu ko kuma su ga aiki ne mai wuya. To, menene zai taimaka mana mu so karatu da kuma nazarin Kalmar Allah? Za a samu amsar wannan tambayar a kalmomin Sarki Sulemanu da suke rubuce a Misalai 2:1-6. Don Allah ka buɗe Littafi Mai Tsarki naka ka karanta waɗannan ayoyin. Bayan haka za mu tattauna su tare.

6. Wane hali ya kamata mu nuna wajen sanin Allah?

6 Da farko mun ga wannan shawara: “Ɗana, idan ka karɓi zantattukana, ka ɓoye dokokina a wurinka: Har da za ka karkata kunnenka ga hikima, ka maida zuciyarka ga fahimi; . . . ” (Misalai 2:1, 2) Menene muka koya daga waɗannan kalmomi? Sun nuna cewa kowannenmu yana da hakkin ya yi nazarin Kalmar Allah. Ka yi la’akari da wannan “idan ka karɓi zantattukana.” Wannan kalmar “idan” tana da girma ƙwarai domin yawancin mutane ba sa saurarar Kalmar Allah. Domin mu samu farin ciki wajen nazarin Kalmar Allah, dole ne mu karɓi zantattukan Jehovah da yardar rai kuma mu riƙe su kamar dukiyar da ba za mu so mu yi hasararta ba. Bai kamata mu ƙyale ayyukanmu na yau da kullum su janye mana hankali mu fara wulakanta Kalmar Allah, ko kuma mu fara yin shakkarta ba.—Romawa 3:3, 4.

7. Duk lokacin da zai yiwu, me ya sa ya kamata mu kasance a taro kuma mu saurari abin da ake faɗa a taro na Kirista?

7 Kana ba da “kunnenka” da gaske ka saurara da kyau sa’ad da ake fassara Kalmar Allah a taro na Kirista? (Afisawa 4:20, 21) Muna ‘mai da zuciyarmu’ domin mu samu fahimi? Wataƙila mai jawabin ba ƙwararre ba ne sosai, amma sa’ad da yake bayyana Kalmar Allah, ya wajaba mu mai da masa hankalinmu. Hakika, domin mu saurari hikima ta Jehovah, dole ne, duk lokacin da ya yiwu mu kasance a taro na Kirista. (Misalai 18:1) Ka yi tunanin yadda wanda ba ya taro a bene a Urushalima a shekara ta 33 K.Z., zai ji! Ko da yake taronmu ba kamar wancan ba ne, Littafi Mai Tsarki, littafinmu mafi girma ake tattaunawa. Saboda haka, kowane taro zai kasance albarka a gare mu idan muka mai da hankali ga abin da ake faɗa kuma muka bi da namu Littafi Mai Tsarki.—Ayukan Manzanni 2:1-4; Ibraniyawa 10:24, 25.

8, 9. (a) Menene nazari yake bukata a gare mu? (b) Ta yaya za ka gwada tamanin zinariya da fahimtar sani na Allah?

8 Kalmomin sarki mai hikima na gaba suka ce: “Idan ka nace bin ganewa, ka tada muryarka garin neman fahimi: . . . ” (Misalai 2:3) Wane nufi ne waɗannan kalmomi suke da shi a gare mu? Hakika, muradi na gaske mu fahimci Kalmar Jehovah! Sun nuna yardar rai a yin nazari domin su samu fahimi, su fahimci abin da nufin Jehovah yake. Wannan hakika yana bukatar ƙoƙari, kuma wannan ya kai mu ga kalmomi da kuma kwatanci na gaba na Sulemanu.—Afisawa 5:15-17.

9 Ya ci gaba da cewa: “Idan ka neme ta kamar azurfa, ka biɗe ta kamar da a ke biɗan ɓoyayyun dukiya: . . . ” (Misalai 2:4) Wannan ya sa mu yi tunanin nasarar mutane a cikin ƙarnuka na nema da kuma tono abin da aka kira ƙarafa masu muhimmanci, azurfa da zinariya. Mutane sun yi kisa domin zinariya. Wasu sun ƙarasa rayuwarsu suna ƙoƙarin su neme ta. Amma menene tamanin zinariya da gaske? Idan ka ɓata a hamada kuma kana jin ƙishirwa, wanne za ka fi so: sandan zinariya ko kuma ruwa moɗa guda? Duk da haka, mutane sun nemi zinariya da ƙwazo, da yake tamaninta yana canjawa!a Da wannan irin ƙwazo ya kamata mu nemi hikima, fahimi, da kuma fahimtar Allah da kuma nufinsa! Amma menene amfanin irin wannan biɗan?—Zabura 19:7-10; Misalai 3:13-18.

10. Menene za mu gani idan muka yi nazarin Kalmar Allah?

10 Sulemanu ya ci gaba da tattaunawa: “Sa’annan za ka gane tsoron Ubangiji, ka ruski sanin Allah.” (Misalai 2:5) Abin mamaki ne cewa mu mutane masu zunubi za mu sami “sanin Allah,” Jehovah, Mamallakin dukan halitta! (Zabura 73:28; Ayukan Manzanni 4:24) Masu bin ussan ilimi da waɗanda wai su mutane ne masu hikima na duniya sun yi ƙoƙari ƙarnuka da yawa domin su fahimci gagara fahimta na rayuwa da kuma sararin samaniya. Amma, sun kasa samun “sanin Allah.” Me ya sa? Ko da yake ya kasance na shekaru dubbai a cikin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, ba su yarda da shi ba domin yana da sauƙi saboda haka suka kasa fahimta.—1 Korinthiyawa 1:18-21.

11. Menene za mu amfana daga nazari da kanmu?

11 Wani abin da Sulemanu ya nanata: “Ubangiji yana bada hikima: daga cikin bakinsa ilimi da fahimi su ke fitowa.” (Misalai 2:6) Da yardar rai Jehovah yake ba da hikima, sani, da kuma fahimi ga dukan wanda zai neme su. Babu shakka muna da kyawawan dalilai na yin nazarin Kalmar Allah, ko ma hakan yana bukatar ƙoƙari, kamewa, da kuma sadaukarwa. Aƙalla muna da Littafi Mai Tsarki ba ma bukatar mu rubuta da hannunmu kamar yadda wasu suka yi a lokacin dā!—Kubawar Shari’a 17:18, 19.

Ku Yi Tafiya Wadda ta Cancanta ga Jehovah

12. Menene ya kamata ya zama dalilin da ya sa muke neman sanin Allah?

12 Menene ya kamata ya zama dalilin da ya sa muke yin nazari? Domin mu fi wasu ne? Domin mu nuna ilimi? Domin mu zama masanan Littafi Mai Tsarki? A’a. Burinmu shi ne mu zama Kiristoci masu bi, waɗanda suke a shirye su taimaki wasu, cikin hali mai wartsakarwa irin na Kristi. (Matta 11:28-30) Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Ilimi kuwa ya kan sa kumbura, amma ƙauna ta kan yi gini.” (1 Korinthiyawa 8:1) Saboda haka, ya kamata mu kasance da irin halin tawali’u da Musa ya nuna sa’ad da ya gaya wa Jehovah: “Ka gwada mini tafarkunka, da zan san ka, domin in sami tagomashi a idonka.” (Fitowa 33:13) Ya kamata mu nemi ilimi domin mu faranta wa Allah rai, ba domin mu burge mutane ba. Muna so mu zama waɗanda suka cancanta, bayin Allah masu tawali’u. Ta yaya za mu cika wannan burin?

13. Menene ake bukata domin mutum ya zama bawan Allah wanda ya cancanta?

13 Bulus ya yi wa Timothawus kashedi game da yadda zai faranta wa Allah rai, yana cewa: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.” (2 Timothawus 2:15) Furcin nan “rarrabe . . . sosai” daga kalmar aikatau ne na Helenanci mai goyo da ainihi take nufin “yanka a miƙe,” ko kuma ‘a yanka babu karkata.’ (Kingdom Interlinear) In ji wasu manazarta, wannan yana nuna yadda tela yake yanka yadi yadda ya kamata, ko kuma yadda manomi yake yin kunya a gona, da dai sauransu. Ko yaya dai, sakamakonsa dole ne ya kasance gaskiya, ko kuma a miƙe. Darasin shi ne domin ya kasance bawan Allah da ya cancanta, wanda Allah ya amince da shi, dole ne Timothawus ya yi ‘iyakan ƙoƙarinsa’ ya tabbatar da cewa koyarwarsa da kuma halinsa sun jitu da kalmar gaskiya.—1 Timothawus 4:16.

14. Ta yaya nazarinmu ya kamata ya shafi abin da muke yi da kuma yadda muke magana?

14 Bulus ya ba da irin wannan kashedi sa’ad da ya aririci Kiristoci a Kolosi su “yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji, [s]una gamshe shi sarai” ta wurin, “bada ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki, [s]una ƙaruwa kuma cikin sanin Allah.” (Kolossiyawa 1:10) A nan Bulus ya faɗi dangantaka tsakanin cancanta ga Jehovah da “bada ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki” da “ƙaruwa kuma cikin sanin Allah.” Abin da yake da muhimmanci ga Jehovah ba yadda muke ɗaukan ilimi da tamani ba kawai amma yadda muke bin Kalmar Allah a abin da muke yi da kuma yadda muke magana. (Romawa 2:21, 22) Wannan yana nufin cewa nazarinmu dole ne ya shafi tunaninmu da kuma halinmu idan muna so mu faranta wa Allah rai.

15. Ta yaya za mu kāre kuma mu ja-goranci zuciyarmu da kuma tunaninmu?

15 A yau, Shaiɗan ya rantse sai ya halaka ruhaniyarmu ta wurin tunanin zuciyarmu. (Romawa 7:14-25) Saboda haka, dole ne mu kāre kuma mu ja-goranci zuciyarmu da tunaninmu domin mu kasance mun cancanta ga Allah, Jehovah. Makamin da muke da shi “sanin Allah” ne, wanda yake da ikon ya “komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kristi.” Wannan ya daɗa ba da dalilin da ya kamata mu mai da hankali ga nazarin Littafi Mai Tsarki kullum, domin mu kawar da tunani na son kai daga zuciyarmu.—2 Korinthiyawa 10:5.

Abin da Zai Taimake Mu Fahimta

16. Ta yaya za mu amfani kanmu sa’ad da Jehovah yake koyar da mu?

16 Koyarwa ta Jehovah tana kawo amfani na ruhaniya da na zahiri. Ba marar kyau ba ne marar muhimmanci. Saboda haka, mu karanta: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi.” (Ishaya 48:17) Ta yaya Jehovah yake sa mu yi tafiya a hanyar da za ta amfane mu? Na farko, muna da Kalmarsa da ya hure, Littafi Mai Tsarki. Wannan shi ne ainihin littafinmu da muke bincikawa kullum. Abin da ya sa ke nan yana da kyau mu bi abin da ake faɗa a taron Kirista da Littafi Mai Tsarki namu a buɗe. Sakamako mai amfani na yin haka za mu gani a tarihin Bahabashe bābā da yake rubuce cikin Ayukan Manzanni sura 8.

17. Menene ya faru a batun Bahabashe bābā, kuma menene wannan ya nuna?

17 Bahabashe bābān ya amince da addinin Yahudawa. Mai bin Allah ne da gaske, kuma ya yi nazarin Nassosi. Yana tafiya a kan karusarsa, yana karatun ayoyin Ishaya sa’ad da Filibbus ya sadu da shi kuma ya tambaye shi: “Ka fahimci abin da kake karantawa?” Menene amsar bābān? “Yaya zan iya, sai ko wani ya bishe ni? Ya roƙi Filibbus shi hau, shi zauna tare da shi.” Sai ruhu mai tsarki ya ja-goranci Filibbus ya taimaki bābān ya fahimci annabcin Ishaya. (Ayukan Manzanni 8:27-35) Menene wannan ya nuna? Cewa karatunmu na Littafi Mai Tsarki kawai bai isa ba. Jehovah, ta wurin ruhunsa, yana amfani da bawan nan mai aminci mai hikima ya taimake mu mu fahimci Kalmarsa a lokacin da ya dace. Ta yaya ake wannan?—Matta 24:45-47; Luka 12:42.

18. Ta yaya bawan nan mai aminci mai hikima ya taimake mu?

18 Ko da yake an kwatanta ajin bawan da “mai-aminci mai-hikima,” Yesu bai ce wannan ba zai yi kuskure ba. Wannan rukunin ’yan’uwansa shafaffu mai aminci ya ƙunshi Kiristoci ajizai. Ko da suna da buri mai kyau, za su iya yin kuskure, kamar yadda na ƙarni na farko suka yi. (Ayukan Manzanni 10:9-15; Galatiyawa 2:8, 11-14) Duk da haka, burinsu mai tsarki ne, kuma Jehovah yana amfani da su ya ba mu abubuwa da za su taimake mu wajen nazarin Littafi Mai Tsarki ya gina bangaskiyarmu ga Kalmar Allah da kuma alkawuransa. Tanadin da bawan ya yi mana domin nazari shi ne New World Translation of the Holy Scriptures. Yanzu ana iya samu gaba ɗayansa ko kuma rabinsa cikin harsuna 42, kuma an buga guda miliyan 114 a harsuna da yawa. Ta yaya za mu yi amfani da shi da kyau a nazarinmu?—2 Timothawus 3:14-17.

19. Waɗanne abubuwa ne New World Translation—With References yake da su da za su iya taimaka mana wajen nazari?

19 Alal misali, New World Translation of the Holy Scriptures—With References. Yana da hasiya, da wuraren bincike da aka jera bisa abajadi, da kuma ƙarin bayani da ya ƙunshi batutuwa 43, haɗe da taswira. Da kuma “Gabatarwa,” da ta ƙunshi wasu tushe da yawa domin wannan fassarar Littafi Mai Tsarki da ta kasance farda. Idan ana samu cikin harshen da za ka iya fahimta, ka yi ƙoƙari ka sarƙu da waɗannan fannoni ka yi amfani da su. Ko yaya dai, Littafi Mai Tsarki shi ne wurin da za mu fara nazarinmu, kuma a cikin New World Translation, muna da juyin da ya nanata sunan Allah da kyau kuma ya nanata Mulkin Allah.—Zabura 149:1-9; Daniel 2:44; Matta 6:9, 10.

20. Waɗanne tambayoyi ne game da nazari suke bukatar amsa?

20 Yanzu za mu iya tambaya: ‘Wane ƙarin taimako muke bukata domin mu fahimci Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu sami lokaci domin mu yi nazari? Ta yaya za mu inganta nazarinmu? Ta yaya nazarinmu zai shafi wasu?” Talifi na gaba zai bincika waɗannan ɓangare na ci gaban Kirista.

[Hasiya]

a Tun daga shekara ta 1879 kuɗin zinariya ya faɗi daga dalla 850 ga oza ɗaya a shekara ta 1980 zuwa dalla 252.80 ga oza ɗaya a shekara ta 1999.

Ka Tuna?

• Menene ake nufi a yi “bimbini” da kuma a yi “waswasi”?

• Wane hali ya kamata mu kasance da shi game da nazarin Kalmar Allah?

• Wane buri ya kamata mu kasance da shi a yin nazarinmu?

• Waɗanne abin taimako muke da su domin fahimtar Littafi Mai Tsarki?

[Hoto a shafi na 23]

Iyalin Bethel sun ga yana ƙarfafawa a ruhaniya a fara ayyuka a rana da bincikan ayar Littafi Mai Tsarki

[Hotuna a shafi na 23]

Za mu iya amfani da lokaci wajen sauraron kaset na Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke tafiya a mota

[Hoto a shafi na 24]

Mutane sun yi aiki tuƙuru domin su samu zinariya. Wane ƙoƙari kake yi domin ka yi nazarin Kalmar Allah?

[Inda aka Dauko]

Courtesy of California State Parks, 2002

[Hotuna a shafi na 25]

Littafi Mai Tsarki dukiya ce da za ta iya kai wa ga rai na har abada

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba