Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 10/1 pp. 21-25
  • Nazari Mai Albarka Kuma Mai Daɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Nazari Mai Albarka Kuma Mai Daɗi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mai da Nazari Abu Mai Daɗi
  • Ƙara Ƙaunar Kalmar Allah Sosai
  • Nazari Bauta Ce
  • Bincika Kalmar Allah Sosai
  • Ana Bukatar Ƙoƙari da Kuma Kayan Aiki Masu Kyau
  • Ka ƙaru wajen Samun Cikakken Sani Da “Yardar Rai Sarai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka More Nazarinka Na Kalmar Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Karatun Littafi Mai Tsarki—Mai Amfani Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 10/1 pp. 21-25

Nazari Mai Albarka Kuma Mai Daɗi

“Ka nema . . . Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah.”—KARIN MAGANA 2:4, 5.

1. Ta yaya za mu ji daɗin karatun shaƙatawa ƙwarai?

MUTANE da yawa suna karatu don jin daɗi ne kawai. Idan abin da ake karantawa mai kyau ne, karatu zai kasance tushe ne mai kyau na shaƙatawa. Ban da tsarin karatunsu na Littafi Mai Tsarki na kullum, waɗansu Kiristoci suna jin daɗin karatun Zabura, Karin Magana, Lingila, da wasu ɓangarorin Littafi Mai Tsarki. Kyan lafazi da kuma tunani yana sa su farin ciki. Wasu sun zaɓi karatun Yearbook of Jehovah’s Witnesses, jaridar Awake! domin shaƙatawarsu, domin labaran rayuwa da ake bugawa a ciki, ko kuma wasu al’amuran tarihi, yanayin ƙasa, da kuma nazarin yanayin rai.

2, 3. (a) A wace hanya za a iya kwatanta sani mai zurfi na ruhaniya da abinci mai tauri? (b) Menene nazari ya ƙunsa?

2 Ko da yake karatu haka zai iya zama hanyar shaƙatawa, nazari yana bukatar wasa ƙwaƙwalwa. Francis Bacon ɗan falsafan Ingilishi ya rubuta: “Wasu littattafai za a ɗanɗana su ne, wasu kuma za a haɗiye, kalilan daga cikinsu kuma za a tauna a kuma narkar da su.” Littafi Mai Tsarki ya faɗa a kashi na ƙarshe. Manzo Bulus ya rubuta: “Muna da abu da yawa da za mu faɗa game da shi kuwa [Kristi, wanda Malkisadik ya alamta], amma zai yi wuyar bayani, da ya ke basirarku ta dushe . . . Abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:11, 14) Abinci mai tauri dole ne a tauna kafin a haɗiye kuma ya narke. Sani mai zurfi na ruhaniya yana bukatar bimbini kafin a fahimci kuma a riƙe.

3 Wani ƙamus ya ba da ma’anar “nazari” cewa “lokacin mai da hankali ne don a sami ilimi ko fahimi, ta wajen karatu, bincike, da sauransu.” Wannan ya nuna ya ƙunshi fiye da yin karatu kawai, wataƙila muna zana ƙarƙashin kalmomi yayin da muke ci gaba. Nazari yana nufin aiki, wasa ƙwaƙwalwa, da kuma amfani da hankalinmu. Ko da yake nazari yana bukatar ƙoƙari, ba ya nufin cewa ba za a iya jin daɗinsa ba.

Mai da Nazari Abu Mai Daɗi

4. In ji mai zabura, ta yaya nazarin Kalmar Allah zai iya zama da wartsakarwa kuma na ban albarka?

4 Karatu da kuma yin nazarin Kalmar Allah yakan iya wartsakarwa kuma ya ba da ƙarfi. Mai zabura ya ce: “Dokar Ubangiji cikakkiya ce, tana wartsakar da rai. Umarnan Ubangiji abin dogara ne, sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita. Ka’idodin Ubangiji daidai suke, waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi. Umarnan Ubangiji daidai suke, sukan ba da fahimi ga zuciya.” (Zabura 19:7, 8) Dokoki da kuma umarnan Jehovah suna wartsakar da ranmu, suna gyara ruhaniyarmu, suna kawo mana kwanciyar rai, suna ba mu fahimi cikin nufe-nufen Jehovah na ban mamaki. Abin farin ciki kuwa!

5. A waɗanne hanyoyi ne nazari zai iya sa mu ji daɗi ƙwarai?

5 Idan muka ga aikinmu da riba, sai mu ji daɗin yin sa. Saboda haka, don mu mai da nazari ya zama da daɗi, ya kamata mu riƙa hanzarin amfani da sababbin abubuwan da muka koya. Yakubu ya rubuta: “Mai duba cikakkiyar ka’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to, wannan shi za a yi wa albarka cikin abin da yake aikatawa.” (Yakubu 1:25) Hanzartawa wajen amfani da darrusa da muka koya zai sa mu gamsu sosai. Yin bincike domin mu amsa wata tambaya da aka yi mana lokacin da muke aikinmu na wa’azi ko koyarwa zai sa mu yi farin ciki ƙwarai.

Ƙara Ƙaunar Kalmar Allah Sosai

6. Ta yaya marubucin Zabura 119 ya furta ƙaunarsa ga kalmar Jehovah?

6 Marubucin Zabura 119, wataƙila Hezekiya, lokacin da yake ɗan ƙaramin yarima, ya furta zurfin ƙaunarsa ga kalmar Jehovah. A cikin waƙa ya ce: “Ina murna da dokokinka, ba zan manta da umarnanka ba. Umarnanka suna faranta mini rai. . . . Ina murna in yi biyayya da umarnanka, saboda ina ƙaunarsu. Ka yi mini jinƙai, zan rayu, saboda ina murna da dokarka. Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarka.”—Zabura 119:16, 24, 47, 77, 174.

7, 8. (a) In ji wani aikin bincike, menene yake nufi a yi “murna” da Kalmar Allah? (b) Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Kalmar Allah? (c) Ta yaya Ezra ya shirya kansa kafin karatun Dokar Jehovah?

7 Da yake bayani a kan kalmar da aka fassara “murna” a Zabura 119, wani ƙamus na Nassosin Ibrananci ya ce: “Yadda aka yi amfani da shi a aya ta 16 ya yi daidai da [aikatau] na yin murna . . . da kuma na bimbini . . . Jerin shi ne: yi murna, yi bimbini, yi farin ciki da . . . Wannan gamin wataƙila, na nufin cewa yin waswasi mai ma’ana hanya ce ta yin ƙaunar kalmar Yahweh. . . . Ma’anar ta haɗa da yadda muke ji.”a

8 Hakika, ƙaunarmu ga Jehovah ya kamata ya fito daga zuciyarmu, aba da take motsa mu. Ya kamata mu ji daɗin dakatawa mu bincika wasu ayoyi da muka karanta ɗazu. Ya kamata mu kawo tunani mai zurfi daga zukatanmu don mu yi bimbini a kansu. Wannan yana bukatar bimbini da kuma addu’a. Kamar Ezra, muna bukatar mu shirya zukatanmu don karatu da kuma nazarin Kalmar Allah. Game da shi an rubuta: “Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra’ilawa dokokin da farillan Allah.” (Ezra 7:10) Ka lura da dalilai uku da ya sa Ezra ya ba da kansa: don ya yi nazari, don ya kiyaye abin da ya koya, kuma don ya koyar. Ya kamata mu bi misalin da ya bari.

Nazari Bauta Ce

9, 10. (a) Ta waɗanne hanyoyi ne mai zabura ya yi bimbini a kan Kalmar Jehovah? (b) Menene aikatau na Ibrananci da aka fassara ‘[ka] yi tunani’ yake nufi? (c) Me ya sa yake da muhimmanci mu ɗauki nazarin Littafi Mai Tsarki ɓangare ne na “bautarmu”?

9 Mai zabura ya ce ya yi bimbini a kan dokokin Jehovah, umarnansa, da kuma koyarwansa. Ya rera: “Nakan yi nazarin umarnanka, nakan kuma yi bimbinin koyarwarka. Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu, zan yi ta tunani a kan koyarwarka. Ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina ta tunani a kanta dukan yini. Ganewata ta fi ta dukan malamaina, saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.” (Zabura 119:15, 48, 97, 99) Me ake nufi da ‘yin tunanin’ ko kuma tunanin Kalmar Jehovah?

10 Kalmar aikatau ta Ibrananci da aka fassara ‘yin tunani’ tana nufin “bin abu a zuciya.” “Yin waswasi a kan ayyukan Allah . . . da kuma kalmar Allah.” (Theological Wordbook of the Old Testament) Suna irin ta kalmar “tunani” yana nuni ga “bimbinin mai zabura,” “ƙaunarsa a yin nazarin” dokar Allah, cewa “bauta ce.” Yin la’akari da cewa nazarin Kalmar Allah ɓangaren bautarmu ce, yana ƙara masa muhimmanci. Saboda haka, ya kamata mu yi shi da kyau da kuma darajar addu’a. Nazari ɓangaren bautarmu ce kuma muna yin sa saboda mu inganta bautarmu ne.

Bincika Kalmar Allah Sosai

11. Ta yaya Jehovah ya bayyana tunani na ruhaniya mai zurfi ga mutanensa?

11 Mai zabura cikin yabawa ya ce: “Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji! Tunaninka da zurfi suke!” (Zabura 92:5) Manzo Bulus ya kuma yi magana game da “zurfafan al’amuran Allah,” tunani masu zurfi da Jehovah ya bayyana wa mutanensa “ta Ruhu” da yake aiki cikin ajin amintaccen bawan nan mai hikima. (1 Korantiyawa 2:10; Matiyu 24:45) Ajin bawan suna ba da abinci na ruhaniya da ƙwazo ga dukan mutane—“nono” ga sababbi amma “abinci mai tauri” ga “manya ne.”—Ibraniyawa 5:11-14.

12. Ka ba da misalin “zurfafan al’amuran Allah” da ajin bawa ya ba da bayanin.

12 Don a fahimci waɗannan “zurfafan al’amuran Allah,” dole ne a yi nazari da addu’a kuma a yi waswasi bisa Kalmarsa. Alal misali, an buga abubuwa masu kyau waɗanda suka nuna yadda Jehovah zai iya yin gaskiya da kuma jinƙai a lokaci ɗaya. Yin jinƙansa ba rage yin gaskiyarsa ba ne; maimako, jinƙan Allah nuna yin gaskiya da kuma ƙaunarsa ce. Idan yana yi wa mai zunubi shari’a, Jehovah zai duba ya ga ko zai yiwu ya yi jinƙai domin fansar hadaya da Ɗansa ya bayar. Idan mai zunubi ya ƙi tuba ko kuma ya yi tawaye, Allah sai ya ƙyale yin gaskiya ta cika aikinta ba tare da tabbacin jinƙai ba. A ta kowace hanya dai, yana manne wa mizanansa masu girma.b (Romawa 3:21-26) “Zurfin hikimar Allah!”—Romawa 11:33.

13. Ta yaya ya kamata mu nuna godiya ga gaskiya ta ruhaniya da “ba su da iyaka” da aka bayyana zuwa yanzu?

13 Kamar mai zabura, muna farin ciki cewa Jehovah yana gaya mana abubuwa da yawa daga tunaninsa. Dauda ya rubuta: “Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni, ba su da iyaka! In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi.” (Zabura 139:17, 18) Ko da yake ilimin da muke da shi a yau kaɗan ne kawai daga cikin tunanin Jehovah mara iyaka wanda zai bayyana cikin dawwama, muna godiya ƙwarai ga gaskiya ta ruhaniya mai tamani da “ba su da iyaka” wadda aka riga aka bayyana zuwa yanzu, za mu ci gaba da tone abubuwan, Kalmar Allah.—Zabura 119:160, hasiya na NW.

Ana Bukatar Ƙoƙari da Kuma Kayan Aiki Masu Kyau

14. Ta yaya Karin Magana 2:1-6 ya nuna bukatar ƙoƙari wajen nazarin Kalmar Allah?

14 Nazari mai zurfi yana bukatar ƙoƙari. Wannan gaskiyar tana bayyane daga karanta Karin Magana 2:1-6 a hankali. Ka yi la’akari da aikatau da Sarki Sulemanu ya yi amfani da su don ya bayyana ƙoƙari da ake bukata don a sami sanin Allah, hikima, da kuma fahimi. Ya rubuta: “Ɗana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na faɗa maka ka yi. Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi. I, ka roƙi ilimi da tsinkaya. Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya. Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah. Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Hakika, nazari mai albarka yana bukatar nema, tonawa, kamar ana neman ɓoyayyiyar dukiya.

15. Wane misali ne na Littafi Mai Tsarki ke nuna bukatar tsarin nazari mai kyau?

15 Nazari mai amfani a ruhaniya har ila yana bukatar tsarin nazari mai kyau. Sulemanu ya rubuta: “Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa.” (Mai Hadishi 10:10) Idan ma’aikaci ya yi amfani da kayan aiki da ba shi da kaifi ko kuma bai yi amfani da shi da hikima ba, zai lalatar da ƙarfinsa kuma aikinsa ba zai yi kyau ba. Hakanan, fa’ida da za mu samu a ba da lokaci a yin nazari zai bambanta ƙwarai, ta dangana bisa tsarin nazarinmu. Shawara mai kyau na yadda za mu inganta nazarinmu za a same shi a cikin Nazari na 7 na littafin nan Theocratic Ministry School Guidebook.c

16. Wace shawara aka bayar da za ta taimaka mana mu yi nazari mai zurfi?

16 Lokacin da masassaƙi zai yi aiki, zai ajiye kayayyakin aiki da yake bukata. Hakanan, lokacin da muka fara nazari, ya kamata mu zaɓi littattafai daga laburarenmu da za mu yi amfani da su. Ka tuna cewa nazari aiki ne da yake bukatar wasa ƙwaƙwalwa, yana da kyau mu zauna da kyau. Idan muna so mu mai da hankali, zama a kan kujera da tebur za ta fi kwanciya ko kuma zama a kan kujerar shaƙatawa kyau. Bayan ka mai da hankali na ɗan lokaci, za ka ga yana da amfani ka warware jikinka ko kuma ka fita waje ka ɗan sha iska.

17, 18. Ka ba da misalin yadda za ka yi amfani da kayayyakin aiki masu kyau da ka ke da su.

17 Muna da kayayyakin aiki da babu na biyunsu. Mafi muhimmanci a cikin su shi ne Littafi Mai Tsarki na New World Translation, yanzu ana samun gaba ɗayansa ko kuma ɓarinsa a cikin harsuna 37. New World Translation cikakke yana ɗauke da hasiya da kuma “Table of the Books of the Bible” (Jerin Littattafai na Littafi Mai Tsarki) da ya ba da sunan marubucin, wajen da ya yi rubutu, da kuma lokacin da ya ci a rubutun. Har ila yana da fihirisa na kalmomin Littafi Mai Tsarki, ƙarin bayani, da kuma taswirori. A wasu harsuna, wannan Littafi Mai Tsarki yana da wanda aka buga da manyan rubutu, da ka sani da Reference Bible. Yana ɗauke da dukan waɗannan abubuwa da kuma fiye da haka, ya haɗa da hasiya, waɗanda su ma fihirisa ne. Kana amfani da abin da ka ke da shi a yarenka domin ka tone da zurfi cikin Kalmar Allah?

18 Wani kayan aiki da muke da shi, kundin sani na ɗaya da na biyu na Littafi Mai Tsarki ne Insight on the Scriptures. Idan kana da wannan a yaren da ka fahimta, ya kamata ya zama abokin hiranka dukan lokacin da ka ke nazari. Zai sanar da kai tushen yawancin batutuwan Littafi Mai Tsarki. Wani littafi mai taimakawa kuma kamar wannan shi ne “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial.” Lokacin da ka fara karatun sabon littafi cikin Littafi Mai Tsarki, yana da kyau ka bincika nazarin da ya yi daidai da shi a littafin “All Scripture” domin ka fahimci yadda yanayin ƙasar take da kuma tarihinta, da kuma taƙaicaccen abin da yake cikin littafin da kuma amfaninsu a gare mu. Wani sabon kayan aiki da aka buga shi ne Watchtower Library wanda yake cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa, ana samunsa a harsuna tara yanzu.

19. (a) Me ya sa Jehovah ya yi mana tanadin kayayyakin aiki masu kyau don nazarin Littafi Mai Tsarki? (b) Menene ake bukata don karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau?

19 Jehovah ya yi tanadin dukan waɗannan kayayyakin aiki ta wurin “amintaccen bawan nan mai hikima” domin bayinsa a duniya su ‘nemi kuma su sami sanin Allah.’ (Karin Magana 2:4, 5) Tsarin nazari mai kyau yana taimakonmu mu sami sanin Jehovah da kyau kuma mu more dangantaka ta kurkusa da shi. (Zabura 63:1-8) Hakika, nazari yana nufin aiki, amma aiki ne mai daɗi kuma mai albarka. Yana ɗaukan lokaci, wataƙila kana tunani cewa, ‘A ina zan sami lokacin da zan yi karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazarina?’ Wannan fanni za a bincika a talifi na ƙarshe na wannan jerin.

[Hasiya]

a New International Dictionary of Old Testament Theology & Exegesis, Littafi na 4, shafuffuka na 205-207.

b Duba Hasumiyar Tsaro 1 ga Agusta, 1998, shafi na 26, izifi na 7. Don nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya maimaita dukan talifai biyun a cikin wannan fitar da kuma talifai su “Justice” (Yin Gaskiya), “Mercy” (Jinƙai), da kuma “Righteousness” (Adalci) a kundin sani na Littafi Mai Tsarki, Insight on the Scriptures, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga.

c Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga. Idan babu wannan littafin a yarenku, za ku sami shawara a tsarin nazari a cikin waɗannan Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 1994, shafuffuka 19-22; 1 ga Agusta, 1987, shafuffuka 28-29.

Tambayoyin Maimaitawa

• Ta yaya za mu mayar da nazarinmu ya zama mai wartsakarwa kuma mai albarka?

• Kamar mai zabura, ta yaya za mu nuna “ƙauna” kuma mu yi “tunani” a kan Kalmar Jehovah?

• Ta yaya Karin Magana 2:1-6 ya nuna ana bukatar ƙoƙari a nazarin Kalmar Allah?

• Waɗanne kayayyakin aiki masu kyau ne Jehovah ya yi tanadinsu?

[Hoto a shafi na 22]

Waswasi da addu’a suna taimakonmu wajen gina ƙauna ga Kalmar Allah

[Hotuna a shafi na 25]

Kana amfani mai kyau da kayayyakin nazari domin ka tone da zurfi cikin Kalmar Allah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba