Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 9/15 pp. 12-15
  • Ka ƙaru wajen Samun Cikakken Sani Da “Yardar Rai Sarai”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka ƙaru wajen Samun Cikakken Sani Da “Yardar Rai Sarai”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Zai sa Mu Kasance da Bangaskiya
  • “Ga Yadda Nake Ƙaunar Dokarka!”
  • Ka Yi Nazari da Nufin Aikatawa
  • Yaya Zan Iya Samun Lokaci?
  • Ƙara Samun Cikakken Sani Yana da Amfani!
  • Nazari Mai Albarka Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 9/15 pp. 12-15

Ka ƙaru wajen Samun Cikakken Sani Da “Yardar Rai Sarai”

DUKAN bayin Jehobah suna son su sami amincewarsa. Da yake muna son hakan, muna son mu kyautata bangaskiyarmu kuma mu bauta masa da himma. Amma, manzo Bulus ya jawo hankalinmu ga wani haɗari, wani da ya shafi wasu Yahudawa a zamaninsa: “Suna da himma domin Allah, amma ba bisa ga sani ba.” (Rom. 10:2) Hakika, bangaskiyarmu da bautarmu ga Jehobah bai kamata su kasance bisa motsin rai ba. Muna bukatar mu san Mahaliccinmu da kuma nufinsa sosai.

Sa’ad da yake rubutu a wani waje, Bulus ya haɗa halin da Allah ya amince da shi da kuma yadda muke ɗokin samun cikakken sani. Ya yi addu’a mabiyan Kristi su “cika da sanin” nufin Allah yayin da suka ci gaba da ‘bada ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki, suna ƙaruwa kuma cikin sanin Allah.’ (Kol. 1:9, 10) Me ya sa muke bukatar cikakken “sani” sosai? Me ya sa ya kamata mu ƙaru a wannan sanin?

Abin da Zai sa Mu Kasance da Bangaskiya

Cikakken sanin Allah da kuma nufinsa yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki ne tushen bangaskiyarmu. Idan ba mu da irin wannan tabbataccen sani, bangaskiyarmu ga Jehobah za ta zama kamar gidan kara da zai rushe idan aka yi ɗan iska. Bulus ya ƙarfafa mu mu bauta wa Allah da “hankalinmu” kuma ‘mu sabonta azancinmu.’ (Rom. 12:1, 2; NW) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai zai taimake mu mu yi hakan.

Ewa, majagaba ta kullum a Poland ta ce: “Da a ce ba na nazarin Kalmar Allah, da na daina ci gaba wajen samun cikakken sani na Jehobah. Halina na Kirista zai soma lalacewa da sauri kuma bangaskiyata ga Allah za ta raunana kuma hakan zai ɓata dangantakata da Allah.” Kada mu bari hakan ya same mu! Ga misalin wani mutum da ya ƙara samun cikakken sanin Jehobah kuma ya more amincewarsa.

“Ga Yadda Nake Ƙaunar Dokarka!”

Waƙar da aka tsara a Zabura ta 119 a cikin Littafi Mai Tsarki ta nuna ra’ayin mai zabura game da dokoki, tunasarwa, farillai, umurni, da ƙa’idodi masu adalci na Jehobah. Mai zabura ya rubuta: “Ina murna da dokokinka . . . Umarnanka suna faranta mini rai.” Ya kuma rubuta: “Ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina ta tunani a kanta dukan yini.”—Zab. 119:16, 24, 47, 48, 77, 97; LMT.

Furcin nan “murna” da “tunani” suna nufin yin bimbini a kan Kalmar Allah, wato, yin farin ciki da irin wannan bimbini. Wannan furci ya nuna yadda mai zabura yake ƙaunar yin nazarin dokar Allah. Wannan ƙaunar ba motsin rai na mai zabura ba ce kawai. Amma, yana son ya ‘yi ta tunanin’ dokar don ya samu fahimin kalmomin Jehobah. Daga halinsa mun ga cewa yana son ya san Allah da kuma nufinsa sosai.

A bayyane yake cewa mai zabura yana ƙaunar Kalmar Allah da dukan zuciyarsa. Muna iya tambayar kanmu: ‘Ina ƙaunar Kalmar Allah kamar mai zabura? Ina farin cikin karanta da kuma bincika Nassosi kowace rana? Ina iyakar ƙoƙarina na karanta Kalmar Allah kuma na yi addu’a ga Jehobah kafin na yi hakan?’ Idan amsarmu ga waɗannan tambayoyin E ne, muna “ƙaruwa kuma cikin sanin Allah” ke nan.

Ewa ta ce: “Koyaushe ina ƙoƙari na kyautata nazari na. Tun lokacin da na samu mujallar nan See the Good Land’ ina amfani da shi kusan kowane lokacin da nake nazari. Ina ƙara ƙoƙari na bincika abubuwa cikin littafin nan Insight on the Scriptures da kuma wasu kayan bincike idan ina bukatarsu.”

Ka yi la’akari da misalin Wojciech da Małgorzata, ma’aurata da suke da hakkin iyali da yawa. Menene suka yi don su haɗa nazarin Littafi Mai Tsarki cikin tsarinsu? “Mun keɓe lokaci don kowannenmu ya yi nazarin Kalmar Allah da kansa. Sa’annan a lokacin nazarinmu na iyali da kuma sa’ad da muke tattaunawa, muna maganar darussa da muka ga suna da ban ƙarfafa da kuma daɗi.” Yin nazari sosai na sa su farin ciki sosai kuma yana taimakonsu su ‘ƙaru cikin cikakken sanin Allah.’

Ka Yi Nazari da Nufin Aikatawa

A matsayinmu na Kiristoci, mun gaskata cewa nufin Allah ne “dukan [ire-iren] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) Wannan ya nuna muhimmancin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin ƙoƙari mu “fahimta.” (Mat. 15:10) Wani abin da zai taimake mu yin hakan shi ne yin nazari da niyar aikata abin da muka karanta. Mutanen Biriya ta dā sun yi hakan sa’ad da Bulus ya yi musu wa’azi: “Suka karɓi magana da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowace rana, su gani ko waɗannan al’amura haka su ke.”—A. M. 17:11.

Kana bin misalin mutanen Biriya na kasancewa da yardar rai kuma ka kawar da dukan abubuwan da suke janye hankali sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki? Kirista zai iya yin ƙoƙari ya yi koyi da mutanen Biriya, ko da a dā ba ya jin daɗin nazari. Bugu da ƙari, wasu mutane ba sa yawan karatu da nazari sa’ad da suka fara tsufa, amma bai kamata ya kasance hakan da Kirista ba. Ko da menene shekarar mutum, yana yiwuwa ya guji abubuwa masu janye hankali. Idan kana karatu, za ka samu abin da za ka iya gaya wa wasu. Alal misali, kana iya sa ya zama halinka ka gaya wa abokin aurenka ko kuma wani abokinka Kirista abubuwan da ka karanta ko ka koya a lokacin da kake nazari. Yin haka zai sa ka riƙa tuna waɗannan abubuwa kuma ka kasance da tasiri mai kyau ga wasu.

Idan kana son ka yi nazari, ka bi misalin Ezra, bawan Allah na dā, wanda yake “kafa zuciyatasa ga biɗar shari’ar Ubangiji.” (Ezra 7:10) Ta yaya za ka yi hakan? Za ka iya neman wuri da zai dace don nazari. Sai ka zauna ka yi addu’a ga Jehobah don ja-gorarsa da kuma hikima. (Yaƙ. 1:5) Ka tambayi kanka, ‘Menene nake son na koya a wannan nazarin?’ Sa’ad da kake karatu, ka nemi muhimman darussan. Za ka so ka rubuta ko kuma ka ja layi a kan abubuwan da kake son ka tuna. Ka yi tunanin yadda za ka yi amfani da wannan bayani sa’ad da kake wa’azi, sa’ad da kake tsai da shawara, ko kuma sa’ad da kake ƙarfafa ’yan’uwa masu bi. Idan ka kai ƙarshen nazarin, ka ɗan taƙaita abin da ka karanta. Wannan zai taimake ka ka tuna abin da ka koya.

Ewa ta faɗi abin da take yi: “Sa’ad da nake karanta Littafi Mai Tsarki, ina amfani da kayan bincike, Watch Tower Publications Index, da kuma Watchtower Library a faifan CD-ROM. Ina rubuta abubuwa don na yi amfani da su a hidimata.”

Shekaru da yawa wasu sun mori yin nazari sosai, kuma suna koyon abubuwa na ruhaniya. (Mis. 2:1-5) Duk da haka, suna da hakki masu yawa kuma yana yi musu wuya su yi nazari na kai. Idan haka gaskiya ne, wane gyara ne ya kamata ka yi?

Yaya Zan Iya Samun Lokaci?

Za ka yarda cewa yana da sauƙi ka keɓe lokacin yin abubuwan da kake so. Mutane da yawa sun ga cewa abin da zai sa su yi nazari na kai shi ne su kafa makasudi da zai yiwu, kamar karanta duka Littafi Mai Tsarki. Hakika, zai iya kasance da wuya a karanta labarin zuriya da ke da tsawo, kwatancin haikali na dā, ko kuma annabci masu wuyan fahimta da ake gani ba su da nasaba a rayuwa ta yau da kullum. Ka yi ƙoƙari ka ɗauki matakai da za su taimake ka ka cim ma makasudinka. Alal misali, kafin ka bincika wani sashe a cikin Littafi Mai Tsarki da ke da wuya, za ka iya karanta tarihinsa ko kuma yadda za ka yi amfani da shi. Za a iya samun irin wannan bayanin a cikin littafin nan “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial,” da ake da shi a kusan harsuna 50.

Yana da kyau sa’ad da kake karanta Littafi Mai Tsarki ka riƙa tunanin yanayin. Wannan zai taimake ka ka riƙa ganin mutanen a zuciyarka da kuma abubuwan da ke faruwa. Yin amfani da waɗannan shawarwarin za su sa ka ji daɗin nazarinka kuma ya kasance da amfani. Hakika, za ka so ka ba da lokaci don yin nazari. Zai fi kasance da sauƙi ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana.

Ko da yake shawarwari da aka ba da a sama za su iya taimakonmu ɗaɗɗaya, menene iyalai za su yi? Me ya sa ba za ku zauna tare ku tattauna amfanin nazari na iyali ba? Wataƙila daga abubuwan da aka tattauna za ku samu hanyoyi masu kyau na karanta Littafi Mai Tsarki, kamar tashiwa da sauri kowace rana, ko wasu kwanaki don ku karanta sashen Littafi Mai Tsarki. Ko kuwa wataƙila abubuwan da kuka tattauna zai nuna cewa kuna bukatar ku gyara tsarin iyalinku. Alal misali, wasu iyalai sun ga ya fi musu kyau su tattauna nassin yini ko su karanta Littafi Mai Tsarki lokacin da iyalin suka gama cin abinci. Kafin su soma kwashe kwanonin ko su soma wasu aikace-aikacen iyali suna tattauna Nassosi ko kuma su karanta Littafi Mai Tsarki na minti 10 ko 15. Da farko zai yi wa iyalin wuya, amma bayan ɗan lokaci iyalin za su saba kuma su ji daɗinsa.

Wojciech da Małgorzata sun faɗi abin da ya taimaki iyalinsu: “A dā muna ba da lokacinmu ga ayyuka da ba su da muhimmanci. Mun tsai da shawara mu yanke lokacin da muke aika saƙo ta intane. Mun kuma rage lokacin da muke yin nishaɗi kuma mun tsara ainihin rana da kuma lokacin yin nazari sosai.” Babu shakka wannan iyali ba ta yi nadamar yin wannan gyara ba, kuma zai kasance hakan ga iyalinka.

Ƙara Samun Cikakken Sani Yana da Amfani!

Yin nazarin Kalmar Allah sosai zai ba da “’ya’ya cikin kowane kyakkaywan aiki.” (Kol. 1:10) Idan hakan ya kasance gaskiya a rayuwarka, dukan mutane za su ga ci gabanka. Za ka zama mai ruhaniya da ke da cikakken fahimi na koyarwar Littafi Mai Tsarki. Shawarwarinka za su fi daidaitawa kuma za ka fi kasancewa a shirye ka taimaki wasu, ba za ka zama mai nace wa abu kamar waɗanda ba su da fahimi ba. Fiye da kome, za ka kusaci Jehobah. Za ka fi yin godiya don halayensa, kuma za a ga hakan sa’ad da kake gaya wa mutane game da shi.—1 Tim. 4:15; Yaƙ. 4:8.

Ko da menene shekaranka, ko kuma abin da kake fuskanta, ka yi iya ƙoƙarinka ka ci gaba da jin daɗin karanta Kalmar Allah kuma ka yi nazarinta sosai da nufin aikata abin da ka koya. Ka kasance da tabbacin cewa Jehobah ba zai manta da ayyukanka ba. (Ibran. 6:10) Zai ba ka albarka mai girma.

[Akwati a shafi na 13]

SA’AD DA MUKA ‘ƘARU DA CIKAKKEN SANI’. . .

Za mu ƙarfafa bangaskiyarmu ga Allah kuma mu yi tafiya wadda ta cancanta ga Jehobah.—Kol. 1:9, 10

Za mu samu fahimi, mu kasance da sanin ya kamata kuma mu tsai da shawarwari da suka dace.—Zab. 119:99

Za mu ƙara jin daɗin taimaka wa mutane su kusaci Jehobah.—Mat. 28:19, 20

[Hotuna a shafi na 14]

Samun wurin da ya dace don nazari yakan yi wuya, amma ya fi kyau

[Hoto a shafi na 15]

Wasu iyalai suna karanta Littafi Mai Tsarki bayan sun ci abinci

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba