‘Yaya Zan Iya Yin Wa’azi Duk da Yanayina?’
Muna da fitattun misalai na ’yan’uwa a dukan duniya da suke saka hannu a aikin wa’azi da aminci ko da yake suna jimrewa da rashin lafiya mai tsanani. Ku yi la’akari da misalin Dalia, wadda take da zama a Vilnius, babban birni na jihar Lithuania.
Dalia ’yar’uwa ce ’yar kusan shekara talatin da biyar. Tun aka haife ta, ta sha wahala daga sakamakon ciwon ƙwaƙwalwa. Wannan ciwon ya shanye jikinta kuma don hakan ba ta iya magana sosai. Saboda haka, sai waɗanda suke cikin iyalinta ne kaɗai suke iya fahimtar abin da take faɗa. Dalia tana zama da mahaifiyarta, Galina, wadda take kula da bukatunta. Ko da yake rayuwar Dalia na cike da wahala da alhini, ta kasance da ra’ayi mai kyau. Ta yaya hakan ya yiwu?
Galina ta bayyana: “A shekara ta 1999, ’yar kawuna Apolonija ta zo don ta ziyarce mu. Mun lura cewa Apolonija, wadda Mashaidiyar Jehobah ce ta san Littafi Mai Tsarki sosai, kuma Dalia ta soma yi mata tambayoyi da yawa. Ba da daɗewa ba, aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Dalia. Jifa jifa, na bi su yin nazarin don na fassara abin da Dalia take faɗa. Amma na lura cewa dukan abin da take koya ya amfane ta sosai. Ba da daɗewa ba ni ma na ce a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.”
Yayin da Dalia ta soma fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki, wani abu ya soma damunta sosai. Daga baya sai ta tambayi Apolonija cewa: “Yaya zan iya yin wa’azi duk da cewa jikina ya shanye?” (Mat. 28:19, 20) Apolonija ta ƙarfafa Dalia: “Kada ki ji tsoro. Jehobah zai taimake ki.” Kuma hakika, Jehobah ya yi hakan.
Ta yaya Dalia ta yi wa’azi? A hanyoyi da yawa. ’Yan’uwa mata Kirista sun taimaka mata ta wajen rubuta wasiƙu na saƙon Littafi Mai Tsarki. Da farko, Dalia za ta gaya wa ’yan’uwa matan saƙonta. Sai su rubuta wasiƙa da ke ɗauke da saƙonta. Dalia tana kuma wa’azi ta wajen aika saƙonni ta wayarta na selula. Kuma sa’ad da yanayin yake da kyau, waɗanda suke cikin ikilisiya suna kai ta waje don su yi wa mutane da suke gareji da kuma kan titi wa’azi.
Dalia da mahaifiyarta sun ci gaba da samun ci gaba a ruhaniya. Sun keɓe kansu ga Jehobah kuma sun yi baftisma a watan Nuwamba ta shekara ta 2004. A watan Satumba ta 2008 an kafa rukuni na yaren Poland a birnin Vilnius. Dalia da mahaifiyarta sun shiga cikin rukunin da yake suna bukatar ƙarin masu shelar Mulki. Dalia ta ce: “Wasu watanni da suka shige na damu ƙwarai da yake ban yi wa kowa wa’azi ba. Amma bayan na yi addu’a ga Jehobah game da batun, ba da daɗewa ba wani ya ce zai zo mu fita wa’azi tare.” Yaya ’yar’uwarmu ƙaunatacciya take ji game da yanayinta? Ta ce: “Ciwon ya shanye jiki na, amma bai shanye zuciya ta ba. Ina farin ciki sosai da yake na iya gaya wa mutane game da Jehobah!”