Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/15 pp. 16-20
  • Ka Koya Daga “Surar Gaskiya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koya Daga “Surar Gaskiya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • INUWAR HADAYAR YESU
  • RA’AYIN DA YA DACE GAME DA HADAYAR
  • GARGAƊI GAME DA HADAYU
  • BA DA GASKIYA GA HADAYAR YESU!
  • Hadayu Na Yabo Da Ke Faranta Wa Jehovah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Za Ka Yi Sadaukarwa Saboda Mulkin Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Hadayu Da Suke Faranta Wa Allah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ba da Hadayu da Dukan Zuciyarmu ga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/15 pp. 16-20

Ka Koya Daga “Surar Gaskiya”

“A cikin shari’a kana da surar sani da surar gaskiya.”—ROM. 2:20.

1. Me ya sa za mu kasance da marmari wajen sanin abin da Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa take wakilta?

ABIN da manzo Bulus ya rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu fahimci muhimmancin ɓangarori da yawa na Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa. Alal misali, a cikin wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa, ya bayyana yadda Yesu a matsayin ‘babban firist mai aminci’ ya yi “kafara” sau ɗaya kuma ya sa ya yiwu waɗanda suka ba da gaskiya su samu “fansa ta har abada.” (Ibran. 2:17; 9:11, 12) Bulus ya bayyana cewa mazaunin “abubuwa na sama da inuwarsu” ne kawai kuma Yesu ya zama Matsakaici na “alkawari mafi kyau” fiye da wanda Musa ya yi matsakaicinsa. (Ibran. 7:22; 8:1-5) A zamanin Bulus, ya kasance da taimako sosai ga Kiristoci yadda Bulus ya bayyana musu abin da wasu fannonin Dokar yake wakilta. Abin da ya gaya musu sun ƙarfafa mu mu nuna godiya ga abubuwan da Allah yake tanadar mana.

2. Wane gata ne Kiristoci Yahudawa suke da shi da ’Yan Al’ummai ba su da shi?

2 A lokacin da Bulus ya rubuta wasiƙa ga Kiristoci a Roma, ya yi wasu cikin kalaminsa ga Yahudawa waɗanda aka riga aka koya musu Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa. Ya gaya musu cewa tun da yake sun san Dokar, sun riga sun san ‘surar sani da surar gaskiya’ game da Jehobah da kuma mizanansa na adalci. Sun fahimci kuma sun yi ƙaunar gaskiyar da suka koya daga Dokar. Kamar wasu Yahudawa masu aminci da suka kasance kafin su, za su iya koya wa mutane gaskiya game da Jehobah.—Karanta Romawa 2:17-20.

INUWAR HADAYAR YESU

3. Yaya muke amfana ta yin nazari game da hadayun da Yahudawa suke yi a dā?

3 Gaskiyar da ke cikin Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa da Bulus ya kwatanta a matsayin surar gaskiyar tana taimaka mana mu fahimci nufin Jehobah. Darussan da Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ta ƙunsa tana da amfani har yanzu. Da yake mun san wannan, bari mu tattauna fanni ɗaya kaɗai na Dokar, wato, yadda hadayu suka sa Yahudawa masu tawali’u su san Kristi da taimaka musu su fahimci abin da Allah yake bukata a gare su. Kuma tun da yake mizanan Jehobah ba sa canjawa, za mu sake ganin cewa dokokin Allah ga Isra’ilawa game da hadayu za su iya taimaka mana mu bincika yadda muke yin tsarkakkiyar hidima.—Mal. 3:6.

4, 5. (a) Mene ne Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa ta tuna wa mutanen Allah? (b) Dokar Allah game da hadayu tana nuni ga mene ne?

4 Ɓangarori da yawa na Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa sun tuna wa Yahudawa cewa su masu zunubi ne. Alal misali, duk wanda ya taɓa gawa yana bukatar ya tsarkake kansa. Don ya yi hakan, za a kashe da kuma ƙona jar karsana lafiyayya. Za a ajiye tokar don a yi “ruwan tsarkakewa” da ita kuma za a yayyafa masa wannan ruwan a rana ta uku da kuma ta bakwai bayan da mutumin ya zama marar tsarki don a tsarkake shi. (Lit. Lis. 19:1-13) Domin a tuna wa Yahudawa cewa an haife su da ajizanci da kuma zunubi, mace za ta kasance marar tsabta na wasu lokatai bayan ta haihu, kuma bayan hakan za ta miƙa hadaya na gafara.—Lev. 12:1-8.

5 Ana bukatar a miƙa hadayu na dabbobi a yanayi masu yawa don gafarar zunubai. Ko sun sani ko a’a, waɗannan hadayun da kuma waɗanda aka miƙa daga baya a haikalin Jehobah ‘inuwa’ ce na kamiltacciyar hadaya da Yesu zai miƙa.—Ibran. 10:1-10.

RA’AYIN DA YA DACE GAME DA HADAYAR

6, 7. (a) Mene ne Isra’ilawa suke bukatar su nuna sa’ad da suke zaɓan hadaya, kuma mene ne wannan yake wakilta? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

6 Jehobah yana bukatar Isra’ilawa su miƙa dabbobi “kamili” ko kuma lafiyayyu, ba makafi ba da guragu da naƙasassu ko kuma masu ciwo. (Lev. 22:20-22) Sa’ad da Isra’ilawa suka miƙa ’ya’yan itatuwa ko kuma hatsi ga Jehobah, ya kamata su zama “’ya’yan fari,” “mafi-kyau” na amfanin gonarsu. (Lit. Lis. 18:12, 29) Jehobah ba ya karɓan hadayu da ba mafi kyau ba ne. Bukata mai muhimmanci game da hadayun dabba sun nuna cewa hadayar Yesu za ta zama marar aibi da tabo kuma cewa Jehobah zai miƙa abu mafi kyau da kuma mafi tamani a gare shi domin ya ceci ’yan Adam.—1 Bit. 1:18, 19.

7 Idan mutumin da ke miƙa hadaya yana godiya sosai ga Jehobah don dukan alherinsa, zai yi farin cikin zaɓan abu mafi kyau daga abin da yake da shi. Mutumin yana iya zaɓan ya miƙa hadaya mafi kyau ko a’a. Amma ya san cewa Allah ba zai yi farin ciki da hadaya mai aibi ba da zai nuna cewa mutumin bai ɗauki miƙa hadayu da muhimmanci ba ko kuma yana jin cewa Jehobah yana sa shi ya yi abin da ya fi ƙarfinsa. (Karanta Malakai 1:6-8, 13.) Ya kamata wannan ya sa mu riƙa tunani game da yadda muke bauta wa Allah. Muna iya tambayar kanmu: Me ya sa nake bauta wa Jehobah? Ina bukatar na canja yadda nake bauta masa kuwa? Shin ina ba shi abu mafi kyau ne?

8, 9. Mene ne muka koya daga yadda Isra’ilawa suke ji sa’ad da suka miƙa hadaya?

8 Ba’isra’ile yana iya miƙa wa Jehobah hadaya da son rai don ya nuna godiya. Ko kuma yana iya ya nemi amincewar Jehobah ta wajen miƙa hadayar ta ƙonewa da son rai. A irin wannan yanayin, zai yi masa sauƙi ya zaɓi dabba mafi kyau. Zai yi farin cikin miƙa wannan dabbar ga Jehobah. Kiristoci a yau ba sa bukatar su miƙa hadayu na zahiri da Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa take bukata, duk da haka suna miƙa hadayu ta wajen yin amfani da lokacinsu da kuzarinsu da kuma dukiyarsu don su bauta wa Jehobah. Manzo Bulus ya yi nuni ga “shaida” na begen Kirista da kuma “yin alheri da zumuntar tarayya” a matsayin hadayu da ke faranta wa Allah rai. (Ibran. 13:15, 16) Yadda muke yin irin waɗannan ayyukan zai nuna yadda muke nuna godiya ga dukan abubuwan da Allah ya ba mu. Kamar Isra’ilawa, ya kamata mu bincika yadda muke ji game da bauta wa Allah da kuma dalilin da ya sa muke bauta masa.

9 A wasu yanayi, Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ta bukaci wanda ya yi zunubi ya ba da hadaya ta zunubi ko kuma ta laifi. Tun da yake ana bukatar hadaya, kana ganin zai kasance da wuya ne ga Ba’isra’ile ya yi hakan da yardan rai? (Lev. 4:27, 28) Zai yi hakan idan yana son ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.

10. Wane “sadaukarwa” ne Kiristoci za su bukaci su yi don su daidaita dangantakarsu da wanda suka wa laifi?

10 A yau, muna iya faɗin abin da ya ɓata wa ’yan’uwanmu rai, wataƙila ba tare da saninmu ba ko kuma domin ba mu yi la’akari sosai ba kafin mu yi magana. Lamirinmu zai iya sa mu gane cewa abin da muka yi bai dace ba. Duk wani da ya ɗauki bautar Jehobah da muhimmanci zai yi iya ƙoƙarinsa don ya gyara halinsa, ko ba haka ba? Hakan yana iya bukatar neman gafara daga wanda muka wa laifi, ko kuma idan zunubi mai tsanani ne, mu nemi taimako daga dattawa. (Mat. 5:23, 24; Yaƙ. 5:14, 15) Muna bukatar mu ɗauki mataki don mu daidaita zunubin da muka yi wa wani ɗan’uwa ko kuma Allah. Idan muka yi irin wannan “sadaukarwa,” kuma muka kasance a shirye mu yi hakan, za mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma ɗan’uwanmu, kuma za mu kasance da lamiri mai kyau. Wannan sakamako mai kyau yana tabbatar mana cewa Jehobah ya san abin da ya fi kyau a gare mu.

11, 12. (a) Mene ne hadayu ta salama? (b) Mene ne za mu iya koya daga hadayu ta salama?

11 Wasu hadayu da Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa ta ambata, su ne hadayu ta salama. Suna nuna cewa mutumin yana da salama da Jehobah. Mutumin da yake miƙa irin wannan hadaya da iyalinsa za su ci naman dabbar da aka miƙa hadaya, wataƙila za a yi hakan a ɗaya cikin ɗakin cin abinci na haikalin. Kowane firist da ya yi hadayar da kuma wasu firistoci da suke hidima a cikin haikalin za su samu rabon naman. (Lev. 3:1; 7:31-33) Mutumin ya miƙa hadayarsa domin yana son ya more dangantaka mai kyau da Allah. Kamar dai shi da iyalinsa da firistoci da Jehobah suna cin abinci tare cikin farin ciki da kuma salama.

12 Saboda haka, miƙa hadaya ta salama tana kama da gayyatar Jehobah cin abinci. Gata ne mai girma ga Ba’isra’ila sa’ad da Jehobah ya amince da gayyatarsa na cin irin wannan abinci. Babu shakka zai so ya miƙa wa Allah abu mafi kyau. Hadayu ta salama suna cikin sashen inuwar gaskiya da ke cikin Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa, kuma sun nuna cewa dukan waɗanda suke son su ƙulla dangantaka ta salama da Mahaliccinsu suna iya yin hakan ta wajen hadaya mai girma ta Yesu. A yau, muna iya zama abokan Jehobah idan mun yi hadaya da yardan rai, ko kuma yi amfani da dukiyarmu da kuzarinmu a hidimarsa.

GARGAƊI GAME DA HADAYU

13, 14. Me ya sa Jehobah bai amince da hadayar da Sarki Saul yake son ya miƙa ba?

13 Jehobah yana amincewa da hadayu idan wanda ya miƙa su yana da halin da ya dace. Amma Littafi Mai Tsarki ya faɗi wasu misalan hadayun da Allah bai amince da su ba. Mene ne ya sa ya ƙi su? Bari mu yi la’akari da yanayi biyu.

14 Annabi Sama’ila ya gaya wa Sarki Saul cewa lokaci ya yi da Jehobah zai zartar da hukunci a kan Amalakawa. Ya kamata Saul ya halaka wannan al’umma magabta tare da dabbobinta. Amma, bayan ya ci yaƙin, Saul ya ce kada sojojinsa su kashe Agag, sarkin Amalakawa. Sai Saul ya bar dabbobinsu mafi kyau a matsayin abin da za a yi hadayarsu ga Jehobah. (1 Sam. 15:2, 3, 21) Mene ne Jehobah ya yi? Ya ƙi da Saul don rashin biyayyarsa. (Karanta 1 Sama’ila 15:22, 23.) Mene ne muka koya daga wannan? Allah yana amincewa da hadayunmu idan mun yi biyayya ga umurninsa.

15. Mene ne hali marar kyau na wasu Isra’ilawa a zamanin Ishaya da suka miƙa hadayu ya nuna?

15 Da akwai wani misali a cikin littafin Ishaya. A zamanin Ishaya, Isra’ilawa a lokacin suna miƙa hadaya ga Jehobah don gafara. Amma halinsu ya sa hadayunsu sun kasance marar amfani. “Ina baicin yawan hadayun da ku ke yi mani?” in ji Jehobah. “Na gundura da raguna hadayun ƙonawa, da kitsen kiyayayyu; ban ji daɗin jinin shanu ba, ko na ’yan raguna, ko na bunsurai. . . . Kada ku ƙara kawo hadayu na banza; turare abin ƙyama ne a gareni.” Mece ce matsalar? Allah ya gaya musu: “Sa’anda ku ke yi mani yawan addu’o’i, ba ni ji ba: hannuwanku cike su ke da jini. Ku yi wanka, ku tsabtata; ku kawarda muguntar ayyukanku daga gaba idanuna: ku bar yin mugunta.”—Isha. 1:11-16.

16. Waɗanne hadayu ne Allah yake amincewa da su?

16 Jehobah ba ya amincewa da hadayun masu zunubi da ba su tuba ba. Amma, Allah yana amincewa da addu’o’i da hadayun waɗanda suke ƙoƙari su yi rayuwa da ta jitu da umurninsa. Inuwar gaskiya ta Dokar ta koya wa irin waɗannan mutanen cewa su masu zunubi ne kuma suna bukatar gafara. (Gal. 3:19) Sa’ad da Ba’isra’ile ya fahimci abin da Dokar take son ta koya masa, yana tuba daga zunubansa kuma yana son Jehobah ya gafarta masa. Haka nan ma a yau, muna bukatar mu tuna cewa ta wajen hadayar Kristi ne kawai Jehobah zai iya gafarta mana zunubanmu. Idan muka fahimci da kuma nuna godiya ga wannan, Jehobah zai “ji daɗin” dukan abin da muke yi a hidimarsa.—Karanta Zabura 51:17, 19.

BA DA GASKIYA GA HADAYAR YESU!

17-19. (a) Ta yaya za mu iya nuna godiyarmu ga Jehobah don hadayar fansa ta Yesu? (b) Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

17 Isra’ilawa sun ga “inuwar” nufe-nufen Allah kawai, amma muna ganin wannan da gaske. (Ibran. 10:1) Dokoki game da hadayu sun ƙarfafa Yahudawa su koyi halaye da suka dace don kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah, wato, suna bukatar su nuna godiya a gare shi da son su ba shi abu mafi kyau da kuma fahimtar cewa suna bukatar ya gafarta musu. Nassosin Helenanci na Kirista sun taimaka mana mu fahimci cewa ta wajen fansa, Jehobah zai kawar da zunubi da mutuwa har abada, kuma a yanzu ya sa mu kasance da lamiri mai kyau a gabansa. Hadayar fansa ta Yesu tanadi ce mai ban al’ajabi!—Gal. 3:13; Ibran. 9:9, 14.

18 Don mu amfana daga hadayar fansa, muna bukatar mu ƙara fahimtar abin da take nufi. Manzo Bulus ya rubuta: ‘Shari’a ta zama mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi, domin a baratar da mu ta wurin bangaskiya.’ (Gal. 3:24) Dole ne mu nuna bangaskiyarmu ta ayyukanmu. (Yaƙ. 2:26) Bulus ya ƙarfafa Kiristoci na ƙarni na farko da suke da surar sani ta Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa su aikata bisa abin da suka koya daga Dokar. Ta yin hakan, halinsu zai jitu da ƙa’idodin Allah da suke koya wa mutane.—Karanta Romawa 2:21-23.

19 Ko da yake ba a bukatar Kiristoci a yau su kiyaye Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa, har ila dole ne su miƙa hadayu da Jehobah zai amince da su. Za mu tattauna yadda za mu iya yin hakan a talifi na gaba.

KA NEMI AMSOSHIN WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

․․․․․

Mene ne hadayu da ke cikin Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa suke wakilta?

․․․․․

A wace hanya ce hadayun da muke miƙawa a yau suke kama da waɗanda Isra’ilawa suka miƙa a dā?

․․․․․

Waɗanne hadayu ne Jehobah yake amincewa da su kuma waɗanne ne ba ya amincewa da su?

[Bayanin da ke shafi na 17]

Abin da Jehobah yake bukata daga bayinsa ba ya canjawa

[Hoton da ke shafi na 18]

Wane ne cikin waɗannan dabbobi biyu za ka miƙa wa Jehobah?

[Hoton da ke shafi na 19]

Jehobah zai amince da mu idan muka miƙa hadayu da ke faranta masa rai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba