Sabon Fasali na Talifi na Nazari
Mun sake yin gyara ga fasalin talifin nazari don ya ƙara yin kyau da kuma taimaka maka a nazarin Kalmar gaskiya mai tamani ta Jehobah.—Zab. 1:2; 119:97.
Shekara huɗu da suka shige ne muka soma wallafa Hasumiyar Tsaro ta wa’azi da kuma ta nazari don Shaidun Jehobah da kuma ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki masu ci gaba.
Wani mai bauta wa Jehobah da daɗewa ya rubuta game da talifi na nazari cewa: “Ina ganin cewa Hasumiyar Tsaro ta nazari ta farko tana da ban al’ajabi kuma ta kasance da amfani a gare ni sosai. Yadda take bayyana koyarwar da ta fi muhimmanci na Littafi Mai Tsarki dalla-dalla ya taɓa zuciyata. Mun gode sosai don wannan sabon tanadi mai ban al’ajabi.” Wani ɗan’uwa ya rubuta: “Ina marmarin ba da lokaci sosai wajen yin nazarin talifi na nazari tare da Littafi Mai Tsarki na.” Mun tabbata cewa kai ma kana jin hakan.
An soma wallafa Hasumiyar Tsaro tun shekara ta 1879, kuma hakan ya yiwu da taimakon ruhun Jehobah da kuma albarkarsa. (Zak. 4:6) A cikin waɗannan shekaru 133, an yi canje-canje masu yawa a bangon mujallar. A bangon kowane fitowa na nazari na shekara ta 2012, za a zana hotuna masu kyau na masu wa’azi kuma hakan zai riƙa tuna mana aikin da Allah ya ba mu na ba da shaida sosai game da Mulkin Jehobah. (A. M. 28:23) A shafi na 2, za ka ga inda aka ɗauko hoton da ke bangon mujallar, tare da ɗan kwatancin abin da ke faruwa da kuma inda ake hakan. A cikin shekarar gabaki ɗaya, hakan zai riƙa tuna wa dukanmu cewa mutanen Jehobah suna wa’azin bishara “cikin iyakar duniya.”—Mat. 24:14.
Waɗanne canje-canje ne kuma aka yi a wannan mujallar? An mai da akwatin bita daga ƙarshen talifi na nazari zuwa farkon kowane talifi. Hakan zai nanata maka muhimman darussa da ya kamata ka nema yayin da kake karanta da kuma yin nazarin talifin. Hakika, masu gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro za su ci gaba da yin amfani da waɗannan tambayoyi don su yi bitar talifin a ƙarshen kowane nazari. Za ka lura cewa an ɗan faɗaɗa gefen talifin kuma an daɗa girman lambobi na shafin da kuma na sakin layin.
Kamar yadda aka bayyana a fitowa ta wannan watan, an ƙara wani sabon talifi mai jigo, “Daga Tarihinmu” don a nuna ci gaba na musamman da Shaidun Jehobah suka samu. Kuma, tarihin mutane za su bayyana a wasu lokatai a ƙarƙashin kan maganan nan “Sun Ba da Kansu da Yardan Rai.” Waɗannan za su bayyana dalla-dalla murna da gamsuwa da kuma farin ciki da ’yan’uwa suka shaida ta wajen yin hidima inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai.
Muna fatan cewa za ka more nazarin Kalmar Allah da taimakon wannan mujallar.
Mawallafa
[Hoton da ke shafi na 3]
1879
[Hoton da ke shafi na 3]
1895
[Hoton da ke shafi na 3]
1931
[Hoton da ke shafi na 3]
1950
[Hoton da ke shafi na 3]
1974
[Hoton da ke shafi na 3]
2008