Sabuwar Hasumiyar Tsaro na Nazari
Jaridar da ka ke karantawa ita ce fitowar farko ta sabuwar Hasumiyar Tsaro na nazari. Za mu so mu bayyana fasalolin wannan sabuwar jaridar.
An wallafa wannan fitowa na nazari ne domin Shaidun Jehobah da kuma ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke samun ci gaba. Za ta fito ne kawai sau ɗaya a wata kuma za ta ƙunshi talifofin nazari guda huɗu ko biyar. An buga tsarin yadda za a tattauna waɗannan talifofin nazarin a bangon wannan jaridar. Akasin Hasumiyar Tsaro na wa’azi, fitowa na nazari ba zai dinga kasancewa da hotuna dabam dabam ba a bangon, tun da ba za a ba da shi ba a hidimar fage.
A shafi na biyu na jaridar, za ka ga taƙaitaccen bayanin da zai taimaka maka ka san manufar kowane talifi na nazari da kuma sauran talifofin. Masu gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro za su ga cewa waɗannan bayanan za su taimaka masu sosai a lokacin da suke shiri don tattauna talifofin a taron ikilisiya.
Za ka ga cewa talifofin nazarin ba su da yawa kamar na dā. Saboda haka, wannan zai ba da ƙarin lokaci don tattauna muhimman nassosi a lokacin Nazarin Hasumiyar Tsaro. Muna ƙarfafa ka ka duba dukan nassosi na kowane mako. An rubuta “ka karanta” a wasu nassosin kuma ana bukatar a karanta su kuma a tattauna su a lokacin Nazarin Hasumiyar Tsaro. Ana kuma iya karanta sauran nassosin idan da lokaci. A wasu talifofin, za ka ga nassosin da aka rubuta “ka gwada da.” Tun da irin waɗannan nassosin ba su bayyana ainihin bayanan da ke cikin sakin layin kai tsaye ba, ba a bukatar a karanta su a taron ikilisiya. Duk da haka, nassosin da aka rubuta “ka gwada da” suna ɗauke da bayanai masu kyau, ko kuwa suna iya ba da wasu ’yan taimako na bayanan da ake tattaunawa. Muna ƙarfafa ka ka karanta su a lokacin da ka ke shirya Nazarin Hasumiyar Tsaro. Ƙila za ka iya yin bayani a kansu a lokacin da ka ke kalaminka.
Rahoto na shekara-shekara ba zai ƙara fitowa a cikin Hasumiyar Tsaro ba. Somawa daga shekara ta 2008, zai fito ne a cikin ’yar ciki na Our Kingdom Ministry da kuma Yearbook. Amma kamar yadda aka ambata a baya, fitowa na nazari zai ƙunshi wasu talifofin. Ko da yake ba za a tattauna yawancinsu a taron ikilisiya ba, muna ƙarfafa ka ka karanta su sosai. Su ma suna ɗauke da abinci na ruhaniya daga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.”—Mat. 24:45-47.
A ƙarshe, fitowar Hasumiyar Tsaro na nazari da kuma na wa’azi ba jaridu kala biyu ba ne. Su duka Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah ne. A shafi na 2, suna da sakin layi iri ɗaya da ke bayyana manufar Hasumiyar Tsaro. Su duka za su kasance a cikin dunƙulan Hasumiyar Tsaro na shekara-shekara. Kuma za a sami bayanin da suka yi a cikin fitowar “Ka Tuna?” wanda za a wallafa a cikin fitowa na nazari.
Tun shekara ta 1879, duk da yaƙi, rashin tattalin arziki, da kuma tsanantawa, Hasumiyar Tsaro ba ta taɓa fasa ci gaba da sanar da gaskiya game da Mulkin Allah ba. Fatan mu shi ne, da albarkar Jehobah, za ta ci gaba da yin hakan a wannan sabuwar fitowar. Kuma addu’armu ita ce Jehobah zai ci gaba da yi wa kai mai karatu albarka, yayin da ka ke amfani da sabuwar fitowar Hasumiyar Tsaro na nazari.