Sabuwar Fitowar Hasumiyar Tsaro ta Nazari a Turanci Mai Sauƙi
MUNA farin cikin gabatar da fitowa ta farko ta Hasumiyar Tsaro ta Nazari a Turanci mai sauƙi. Za a gwada wannan fitowar shekara guda, kuma idan yana da ban taimako, za a ci gaba da wallafa ta. Za a aika wa ikilisiyoyi a lokaci ɗaya da ake aika Hasumiyar Tsaro da aka saba amfani da ita a Turanci.
Yana da muhimmanci sosai kowa ya fahimci bayani da muke nazarinsa a cikin Hasumiyar Tsaro a kowanne mako, domin Nazarin Hasumiyar Tsaro ne hanya ta musamman da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake koyar da mutanen Allah a yau. (Mat. 24:45) Amma me ya sa ake bukatar Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi.
’Yan’uwanmu da yawa a dukan duniya suna yin taronsu a Turanci amma ba a koyaushe ba ne suke fahimtar Turancin da ake amfani da shi a cikin Hasumiyar Tsaro ba. Da akwai dalilai da yawa don wallafa Hasumiyar Tsaro ta Nazari a Turanci mai sauƙi. Alal misali, ana amfani da Turanci a ƙasashe da yawa a Afirka da Asiya da kuma Kudancin Tekun Pasifik. ’Yan’uwanmu da ke waɗannan wurare suna yin amfani da Turanci a tarurrukansu da kuma aikin wa’azi amma suna iya yin wasu harsuna a gida. Kuma Turancin da ake yi a waɗannan ƙasashen yana iya bambanta da wanda ake amfani da shi a cikin Hasumiyar Tsaro ta Turanci. Wasu cikin ’yan’uwanmu sun yi gudun hijira zuwa ƙasashen da ake yin tarurruka a Turanci. Amma yana musu wuya su fahimci nazarin Hasumiyar Tsaro domin Turanci ba yarensu ba ne. Yana wa wasu yara da ainihi Turanci ne yarensu wuya su fahimci nazarin Hasumiyar Tsaro ɗin. Mujallar a Turanci mai sauƙi za ta sa ya yi wa ’yan’uwanmu a dukan duniya sauƙi su amfana daga Nazarin Hasumiyar Tsaro.
Ko da yake wannan mujallar ta yi amfani da Turanci mai sauƙi fiye da wanda aka saba amfani da ita, dukan mujallun za su koyar da abu iri ɗaya daga cikin Littafi Mai Tsarki. Duka za su kasance da adadin sakin layi ɗaya, duka za su samu adadin tambayoyi da hotuna da tambayoyin bita iri ɗaya. Hakan yana nufin cewa kowane mutum zai tsai da shawara a kan mujalla ta Turanci da yake son ya yi nazarinsa da kuma yi amfani da ita a Nazarin Hasumiyar Tsaro. Don ganin bambanci a Turancin da aka yi a waɗannan fitowa biyu, ka duba misalin da ke ƙasa wanda aka kofa daga shafi na biyu na talifin nazari na farko na wannan fitowar.
Muna da tabbaci cewa mujalla a Turanci mai sauƙi za ta sa ya yi wa ’yan’uwanmu da yawa har da yara sauƙi su shirya don Nazarin Hasumiyar Tsaro a kowanne mako. Jehobah yana ƙaunar dukan “’yan’uwanci” kuma muna godiya da yake yana amfani da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” don ya ba mu kome da muke bukata a kan kari.—1 Bit. 2:17.
Hukumar Mulki ta Shaidun Jehobah