Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 12/15 pp. 29-31
  • Me Ya Sa Aka Wallafa Hasumiyar Tsaro a Turanci Mai Sauƙi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Aka Wallafa Hasumiyar Tsaro a Turanci Mai Sauƙi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA YA SA TA BURGE MUTANE
  • TA TAIMAKA WA IYAYE SOSAI
  • ABIN DA YARA SUKA CE
  • Sabuwar Fitowar Hasumiyar Tsaro ta Nazari a Turanci Mai Sauƙi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Sabuwar Hasumiyar Tsaro na Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Sabon Fasali na Talifi na Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • “Haka Nan Ya Gamshe Ka Sarai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 12/15 pp. 29-31

Me Ya Sa Aka Wallafa Hasumiyar Tsaro a Turanci Mai Sauƙi?

SHEKARU da yawa, mutane sun amfana sosai daga koyarwar da ke cikin Hasumiyar Tsaro. A watan Yuli na shekara ta 2011 ne aka soma wallafa Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi. Wannan talifin ya bayyana cewa: “Za a gwada wannan fitowar shekara guda, kuma idan tana da ban taimako, za a ci gaba da wallafa ta.”

Za ku yi farin ciki sanin cewa mun shawarta a ci gaba da wallafa ta. Nan ba da daɗewa ba, za a soma wallafa Hasumiyar Tsaro a Faransanci da Yaren Portugal da kuma Sifanisanci mai sauƙi.

ABIN DA YA SA TA BURGE MUTANE

Ga abin da mutane da yawa a Kudancin Tekun Fasifik suka ce bayan sun karɓi wannan Hasumiyar Tsaro: “Yanzu ne ’yan’uwa suke fahimtar ainihin abin da ke cikin Hasumiyar Tsaro sosai.” Wata wasiƙa kuma ta ce: “A dā muna amfani da lokaci sosai wajen neman ma’anar kalmomi a cikin ƙamus da kuma yin ƙoƙari mu fahimci Turancin, amma yanzu muna amfani da shi wajen fahimtar nassosi da aka nuna a cikin talifin da kuma muhimmancinsu.”

Wata ’yar’uwa da ke ƙasar Amirka da ta sauke karatu a jami’a ta ce: “Na yi shekaru 18 ina faɗi da kuma rubuta Turancin da masu ilimi sosai ne kaɗai suke fahimta. Kuma ina magana da kuma tunani a hanyar da yake wa mutane wuya su fahimce ni. Sai na gane cewa ya kamata na yi gyara.” Amma, yanzu da ta ƙware wajen koyar da Littafi Mai Tsarki, ga abin da ta ce: “Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi ta taimaka mini sosai. Turancin da aka yi amfani da shi ya koya mini yadda zan bayyana abubuwa a hanya mai sauƙi.”

Wata ’yar’uwa a ƙasar Ingila da ta yi baftisma a shekara ta 1972 ta ce game da wannan Hasumiyar Tsaro: “Da na karanta fitowa ta farko, sai na ji kamar Jehobah yana zaune kusa da ni da hannunsa a kafaɗata, kuma muna karatun tare. Yana kama ne da uba da ke wa ɗansa tatsuniya kafin ya yi barci.”

Wata ’yar’uwa da ta yi baftisma shekaru 40 da suka shige, kuma tana hidima a Bethel da ke Amirka ta ce wannan fitowar ta sa ta fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. Alal misali, akwatin nan “Some Expressions Explained” (Wasu kalmomin da aka bayyana) wanda ke cikin fitowa ta 15 ga Satumba, 2011 ya bayyana abin da ake nufi da “taron shaidu mai-girma” da ke cikin Ibraniyawa 12:1 cewa: “Sun yi yawa ainun da ba za a iya ƙirga su ba.”’Yar’uwar ta ce bayanin ya sa ta fahimci wannan ayar sosai. Ta ce game da nazarin Hasumiyar Tsaro na mako-mako: “Ko da yaro ya karanta furucinsa ne daga Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi, zai yi dabam da abin da ke cikin wanda aka saba yin amfani da shi. Kuma hakan yana sa furucin ya amfani ’yan’uwa.”

Wata ’yar’uwa da ke hidima a Bethel ta ce: “Ina ɗokin sauraron furucin yaran da ke cikin ikilisiya. Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi tana taimaka musu su yi furuci da dukan zuciyarsu, kuma hakan yana ƙarfafa ni.”

Wata ’yar’uwa da ta yi baftisma a shekara ta 1984 ta rubuto don ta yi godiya game da wannan Hasumiyar Tsaro. Ta ce: “Don ni aka wallafa wannan Hasumiyar Tsaro. Ta sa ina fahimtar abin da nake karantawa da sauƙi. Yanzu ina da gaba gaɗin yin furuci sa’ad da ake nazarinta.”

TA TAIMAKA WA IYAYE SOSAI

Wata ’yar’uwa da ɗanta shekara bakwai ne ta ce a dā shirya Hasumiyar Tsaro da ɗanta babban aiki ne, domin sai ta yi ta bayyana kowane layi. Amma yaya ta ji yanzu da ta sami wannan Hasumiyar Tsaro? Ta ce: “Ina mamaki ƙwarai cewa yanzu yana karanta da kuma fahimtar kowane sakin layin sosai. Yana jin daɗin talifin sosai domin jimlolin gajeru ne, kuma kalmomin ba su da wuyar fahimta. Yanzu yana shirya furucin da zai yi a taro da kansa, kuma yana mai da hankali sosai sa’ad da ake nazarin Hasumiyar Tsaro.”

Wata ’yar’uwa mai ’yar shekara tara kuma ta rubuto cewa: “A dā sai mun taimaka mata wajen shirya furucin da za ta yi. Amma yanzu tana yin hakan da kanta. Ba ma bukatar mu bayyana mata ma’anar kalmomin, domin ba su da wuya sosai. Yanzu tana more nazarin Hasumiyar Tsaro sosai.”

ABIN DA YARA SUKA CE

Yara da yawa suna ganin an wallafa wannan Hasumiyar Tsaro musamman domin su. Rebecca ’yar shekara 12 ta ce: “Don Allah kada ku daina wallafa wannan sabuwar fitowar! Ina son wannan sashen ‘Some Expressions Explained.’ Yana da sauƙin fahimta ga yara.”

Nicolette ’yar shekara bakwai ma hakan take ji. Ta ce: “A dā Hasumiyar Tsaro tana mini wuyar fahimta, amma yanzu ina iya yin furuci da kaina.” Emma ’yar shekara tara kuma ta ce: “Ni da ƙanena mai shekara shida mun amfana sosai. Yanzu muna fahimtar abubuwa sosai. Mun gode!”

Babu shakka cewa mutane da yawa suna more wannan fitowar Hasumiyar Tsaro da ke amfani da kalamai da kuma jimloli masu sauƙin fahimta. Tana taimaka wa mutane da yawa su fahimci koyarwar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma za a ci gaba da buga ta tare da wanda aka saba wallafawa tun shekara ta 1879.

[Bayanin da ke shafi na 30]

“A dā muna amfani da lokaci sosai wajen neman ma’anar kalmomi a cikin ƙamus da kuma yin ƙoƙari mu fahimci Turancin, amma yanzu muna amfani da shi wajen fahimtar nassosi da aka nuna a cikin talifin da kuma muhimmancinsu”

[Bayanin da ke shafi na 31]

“Ina mamaki ƙwarai cewa yanzu yana karanta da kuma fahimtar kowane sakin layin sosai”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba